DANGI DAYA HAUSA NOVEL
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari bayan sallar asuba yaran duk bacci suka koma, sai Diddi da Momy ne kawai suke fira sama-sama, gari nayin haske suka fara had’a abin karya wa, zuwa tayi d’aki tataso Nihla tashiryata tsaf sannan tabata nera ashirin tace ta tatafi makaranta
Yauma tana fita kofar gida taga gate din gidansu abude,direban gidan yana goge Mota, shikuma yana tsaye da lunch box ahannun sa, lokaci d’aya farin ciki ya kamata, yau itace da kanta tafara d’aga masa hannu, cikin sauri ya ajiye Abincin nasa aqasa yafuto da gudu, direban yana kiransa amma ko waiwayowa baiyi ba, qyaleshi yayi amma de yabishi da kallo yanaso yaga Inda zaije
Kusa da ita yaje ya kalleta “meyasa jiya ban ganki ahanya ba da aka tashi daga school?”
Zaro ido tayi “laaaa ashe kaima kana nemana, nima inata kallan hanya banganka ba”
Zuba mata ido yayi yace “yaya sunanki?”
Tace “Nihla Ibrahim Mai hakuri, kaifa?”
Cikin farin ciki yace “Yusif Isma’eeil,”
Hannun ta yaja yafara tafiya “zomuje direba yakaimu school tare”
Qwace hannunta tayi tace “um um Babu ruwana Diddi zata dakeni, tace karna tsaya ako’ina”
Tana fadar haka taqwace hannunta tatafi da gudu, shima Kallanta yake yana daria, sannan ya juya ya koma cikin gidansu
Da azahar ana tashinsu daga makaranta bata tsaya wasaba tataho gida, tana hanya bataga motarsu ba, saida ta kusa qarasawa gida sannan ta hangi motarsu suna shiga gida
Bayan sallar la’asar dukansu suna zaune suna fira, Nihla tana kwance akan tabarma Momy tajata ta d’ora mata kanta akan cinyarta ????
Sukuma mazan suna buga ball Ahankali kasancewar gidan akwai d’an fad’i kad’an yau harda Abba akeyi, yana sanye da qananun kaya riga me Jan duhu da wandon jeans amma ya tattare wandon daga qasa ya maidashi Kamar three quater
Saida sukayi suka gaji sannan kowa Yazauna, wayar Usman Abba ya karba yafara game, Nihla tanajin qaran game tatashi takoma wajansa tana gani, qasa-qasa tayi muryarta tace masa “zomuje yawo”
Shiru yayi ya qyaleta, tasake cewa “kaji”
Kallanta yayi becemata komaiba ya kashe game din yasaka wayar a aljihunsa yatashi yace mata “Muje”
Daria tayi itama tatashi, takama hannunsa suka fara tafiya ya kalle Momy yace “Momy munfita”
Cikin farin-ciki tace “to Abba na, amma Karku d’ad’e naga garin akwai hadari”
Basuce mata komaiba suka fice daga gidan ita kuwa Nihla takama hannunsa ta riqe sosai
Suna fita suka dinga zaga garin, sai surutu take masa amma amsar datake samu kad’ance daga wajansa
Kallanta yayi “ina zamuje?”
Tace “zakaje rafi innuna ma ruwa dayawa muyi wasa saimu dawo?”
“akwai ruwa sosai?”
Tace “eh akwai sosai baka ganiba harda kwale-kwale”
Yace “to Muje mu”
Tafiya sukayi me nisa sosai, Yakalleta yana haki yace “kewai bamuzo bane?”
“to idan munzo ai zakaga Ruwan ko? Kaide kataho kawai”
Bece da’ita komaiba suka cigaba da tafiya har sukazo wajan, hannunsa tasaki tatafi wajan Ruwan da gudu tana daria, abaki bakin Ruwan ta tsaya, sannan tasaka hannunta tad’ebo Ruwan ta watsa masa
Firgigit yayi, yadawo hankalinsa daga kallan yawan Ruwan wajan, yace “kika jiqani?”
Kafin tabashi amsa ya qaraso wajan shima yad’iba ya watsa mata, bata damuba, dariya ma tayi tasake diban wani tajiqashi, shima yasake ramawa, haka duk suka jiqa jikinsu shima ya biyemata sai daria suke cikin farin-ciki
Hijabin jikinta ta cire tana wullashi sama, tana cafewa, sai tsalle take tanata farin ciki, wayar Usman yadauko acikin aljihun wandon sa ya tsaya yanayi mata photo, gani tayi yana binta da waya ta tsaya tace “photo kakemin?”
“eh” shine kawai amsar daya bata
Tace “to tsaya na gyara”
Tsayuwa ta gyara, yanata yimata photon iri iri, ya shagala yanayi mata pictures din, ta tsugunna ta d’ebi yashin dayake wajan ta zuba masa ajikinsa
Wandonsa ya kalla yanda tazuba masa yashi,memakon ransa yabaci saiyayi murmushi yabiyota da gudu, tana gudu tana waiwayensa har tazo wajanda aka tara wani yashin da yawa, tana zuwa wajan tafad’i
Shima yana qarasowa wajan yariqe gashin kanta yace “wana kama?”
Daria tayi tace “nadena, Allah nadena”
Rabuwa yayi da ita ya kwanta anan gefenta akan yashin, sai haki suke maidawa kowa yana kallan Dan’uwansa, wayar hannunsa yadaga yayi musu pic suna daga kwancen
‘Dis taji an d’iso mata ruwa, Dasauri tatashi duk yashi yabata mata gashin kanta tace,”ABBA ruwa”
Hannunta ya fizgo tadawo ta kwanta yanda take da, yace “me kikace?”
“Abba” tabashi amsa kai tsaye
Girgiza kansa yayi yace “Yaya Abba zakice”
Daga masa kai tayi, kafin tace wani abu sukaji Saukar ruwa akansu, cikin sauri suka tashi, tadauki hijabinta, yariqe hannunta suka tafi qasan wata bishiya da gudu, suka tsaya anan, Tun ana yayyafi aka dawo ana shara ruwa da karfi, duk tsoro yakamata, ta rikice, shikuwa Babu wani tsoro atare dashi, iskar da akeyi ne yasa bishiyar dasuke qasanta kad’awa, nan take ruwa yajiqe musu jikinsu jagab,kallan gashin kanta yayi, gaba d’aya yajiqe ya kwanta sosai yana sheqi Kamar Wanda ake saka masa Mai, hijabin jikinta ya karba Yarufe mata Kannata dashi, sannan yajata yasakata ajikinsa yace “kidena tsoro”
Bata iya cemasa komaiba, ahaka suka tsaya har aka qare Ruwan tas, Inda Allah yarufa Asiri ba’a dauki lokaci ana Ruwan ba
Ana gama Ruwan yasaketa, cikin tsoro tace “mutafi gida”
Bece mata komai ba yariqe hannun ta suka fara tafiya, mutane kowa yafuto yanata harkar gabansa
Sunzo wucewa ta wata bishiya su kaga mutane suna gudu ana cewa Zuma! Zuma!! Zuma!!!
Kallansa tayi tace “la’ila, wallahi mugudu karya cijemu”
Nan take suka fara gudu duk yanda sukaso kaucewa saida zuman yacijeshi awuyansa, kafin ya farga wani yashiga cikin hancinsa, lokaci d’aya ya rikice ya tsaya yadena gudun, hannunta yasaki, yarasa yaya zaiyi yafitar, wani me machine ne yazo wucewa ya gansu, ita yagane yace “subhanallah Nihla, me yakawo ku nan wajan?”
Kafin tace wani abu yacacimi Abba yasakashi akan machine din, ita kuma yasakata agaba, be tsaya ko’inaba sai Dan qaramin asbitin garin (Nuhu Alfa Hospital)
Saida ya danqasu ahannun likita, yaga sun fara duba Abba sannan yace musu zaije gidansu yasanar
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Acan gida kuwa duk sun fito kofar gida, gaba dayansu har mahaifin Nihla, sunyi neman duniya sun rasa Abba da Nihla ????
Me machine yana zuwa kofar gidan yafaka, suka gaisa da mahaifin Nihla, nan take ya sanar dasu komai, cikin tashin hankali suka nufi asbitin baki d’ayansu
Waye yusif? Menene yake tsakanin Aisha da yayanta Abubakar? Wacce irin wasiyya iyayen su suka rubuta? Duk Ku biyoni
Sharhi please ????
Mrs Usman ce ✍️
[6/14, 10:40 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{ Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook
5&6
Suna zuwa asbitin sukaga Abba Akwance Idanunsa yayi jajir, Nihla tana zaune agadon kusada qafafunsa, sai likitan daya dubashi a tsaye
Momy tace “subhanallah, sannu Abba,”
Sannan ta kalli likitan tace “doctor Babu dai wata matsala ko?”
“Babu komai hajiya, ai anyi masa allura ma, zaku iya tafiya, saide a kiyaye gaba”
Diddi tace “insha Allah likita, yanzu ma nemansu mukai muka rasa, amma insha Allah za’a kiyaye”
Takai Kallanta ga Abba tace “Sannu Abba, kanajin zafi yanzu?”
Girgiza mata kai yayi, Bece komai ba
Momy tasa hannu ta kamashi yasauko daga gadon, su Usman suka riqoshi suka futo daga asibitin
Suna hanya yadaga kai yakalli momy yace “Momy”