DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Kallansa tayi cikin harara, tatashi zata fice daga dakin

Cikin sauri yatashi yariqota, tafara fizge-fizge “nika cikani natafi gidanmu tunda dama baka kaunar ganina”

Yace “maryam nifa wasa nake miki”

“Babu wani wasa, bayan gashinan kashigo daki kana waya da’ita, kacika…… Bata qarasa maganar tataba yahade bakinsu waje daya, diff kakeji Diyana tayi shiru

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Itada Momy ne a kitchen sunata aiki kayaiyakin yin kek ne agabansu Nihla tana hadawa

Adede lokacin yafuto daga dakinsa yana daura agogo a hannunsa, yana sanye cikin suit,sunyi mutuqar yimasa kyau, amma baisaka jacket dinba, a hannunsa ya riqeta, ko wajan Momy bai nufa ba yafita Dasauri, zai qarasa campany wajan Aslam

A kitchen din kuwa Momy ta kalleta “Nihla idan kinsan bazaki iya yin kek dinnan ba Tun wuri nasa ayi muku oder”

Murmushi tayi “Momy kenan, kede zuba ido kisha kallo, da kaina zanyi kek din”

Momy tace “shikam Abba da alama ma ya Manta cewa yau yake birthday, ke kuwa gashi baki Manta nakiba Tun safe kin hana kanki sukuni, nima kin hanani zama saboda wannan bikin birthday ganaki Gana Abba”

Murmushi tayi tace “Momy ai abune na rana daya, idan tawuce shikken”

“hakane, to Allah yabada sa’ah, guda daya zakiyi muku ne ke dashi kokuma daban daban zakiyi?”

Kai tsaye tace “Momy da nawa Zan farayi, idan yanaso shima sai ayi masa”

“wacce irin magana ce wannan Nihla? Nafada miki Abba ya Manta yau yake birthday, ya za’ai kuna gida daya keda yayanki kuma ranar birthday dinku daya aje ana rabe raben wani kek, kiyi muku babba guda daya keda shi, sannan idan masu kayan Decoration din sun kawo kishirya muku komai tare “

Jikinta ne yayi sanyi tace” to Momy “

Momy tafita daga kitchen din, ita kuma tayi shiru tana tunani, Allah yasa ta dinga control din kanta agaban Momy karta ga tana tsanar danta qiri-qiri

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin motarsa qirar Rang rover yafuto daga gidan, adede lokacin wani matashi yafaka motarsa, yafuto hannunsa dauke da Wata leda anyi rapping dinta, cikin sauri ya Dakatar dashi yace “yallabai Dan Allah nanne family house na Mazawaje ko?”

Yace “lafiya?”

Matashin saurayin yace “a a babu komai dama maigida nane ya aikoni daga Abuja wajan hajiya Nihla, gift din birthday dinta ne yace ayyuka sunyi masa yawa bazai samu damar zuwaba, amma very soon yana hanya”

Cikin mamaki yafara magana aransa Birthday? dama yau take yin birthday?to ai shima yaune nasa, Waye wannan daya aiko mata da gift daga Abuja? Haushi ne ya kamashi, yaji wani irin kishi aransa

Kallan matashin yayi yace “i don’t no, ka tambayi wasu”

Daga nan yaja motarsa yayi gaba, matashin yayi sa qare yana kallan motar Abba, ikon Allah, shikuma wannan daga tambaya? ????
Cikin gidan yanufa yaga maigadi anan yafara tambayarsa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“kaga Abba idan muka saka hannun jarinmu Awannan campany zamu samu riba sosai, saboda shima Babban campany ne ansan shi sosai”

Yana jiran yaji Abba yabashi amsa sai yaji shiru, cikin mamaki ya kalleshi “Abokina mekake tunani ne?”

Nanma yaji shiru, ta’bashi yayi yace “Abba!!”

Cikin sauri yadawo daga duniyar tunanin daya lula, ya kalleshi “Aslam ya akayi?”

Dan qaramin murmushi Aslam yayi “kana nufin kacemin duk wannan maganganun danayi baka jina?”

Kallansa yayi yadaga masa kai alamar hakane

Wani murmushin Aslam yasake yi “meyake damunka haka Abba? Tunanin me kake? Yanzu fadamin menene matsalar?”

Ajiyar zuciya yayi “yanzu Aslam misali idan mace tana Birthday me kake ganin za’a bata amatsayin gift?”

Aslam yayi Murmushi, sai yanzu yagano Inda tunanin Abba yadosa
Yakalleshi yace “um nide aganina za’a iya bata kyautar sarqa idan ranar birthday din tazo saika saka mata, kokuma zobe kakama hannunta kasaka mata, kokuma ka tambayeta abinda takeso, shine ma yafi”

Cikin damuwa Abba yace “zobe, sarqa, kokuma kayan ciye-ciye ai duk sun zama gama gari Aslam”

Aslam ya kalleshi cikin mamaki, lalle Abba yashiga dayawa ????

Yace “tome kake gani za’a bata?”

“why not asiya mata Mota? Kamar zatayi murna da’ita”

Aslam yayi dariya yace “gaskiya Abokina Nihla tayima Babban kamu, irin wannan soyaiya haka aiko Nadiya ba’a nunawa itaba”

Memakon yabawa Aslam amsa sai yace “please ka bincika min yanzu, inaso akawota yanzun nan”

Aslam yace “okey” sannan yadauki wayarsa yafara dube-dube, yadago yadubi Abba yace “wacce irin qira kake buqata?”

Kai tsaye yace “Camry”

Aslam yace “angama”

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Suna tsaka da aiki iliya maigadi yashigo yace tanada baqo, cikin mamaki tafuto anan taga Baqon fuska, suka gaisa dashi faram faram, gift din hannunsa yabata yace “gashi daga Abuja, inji ogana, yace kiyi hakuri shima yakusa zuwa”

Murmushi tayi jin daga Inda saqon yake, tasan ya Yusif ne, tace “a a babu komai wallahi, zamuyi waya dashi, qaraso mana ciki kasha ruwa”

Yace “a a Hajiya, inakan hanya ne wallahi, babu damuwa”

Nihla tace “to shikkenan nagode” daga nan takoma ciki

Tana zuwa tabawa Momy gift din nata tace “Momy, ya Yusif ne ya aikomin da birthday gift”

Jikin Momy yayi sanyi, amma dukda haka saida ta nuna murnar ta afili, tace “masha Allah, Allah yasaka da alkhaairi, da alama ko menene aciki zaiyi kyau Kamar kyakykyawar ‘yata”

Murmushi tayi tafara kokarin budewa tace “Momy bari mu bude mugani”

Cikin sauri Momy ta riqe hannunta “a a, kibari idan mungama aiki, kinyi wanka, me makeup tazo tazo tayi miki kungama bikin birthday dinku lafiya saiki bude abinki atsinake”

Tace “to Momy,”

Sannan tayi hanyar dakinta da kyautar tata

Dawowa tayi sukaci gaba da aiki, Momy tana ganin tsantsar baiwar da Allah yabawa Nihla, kek din ta cire daga cikin oven tafara yaiyenke gefensa,sannan tadauko wifed cream na ruwa, ta ajiye, tafara neman sauran kayaiyakin buqata

Kallan Momy tayi tace “Momy, wai yaushe Daddy zai dawo ne?”

“kinyi missing dinsa kenan, gobe zai dawo insha Allah,”

Cikin murna tace “to Allah yakaimu”

Momy taga yanda Nihla take murna saitaji dadi, amma itama kanta tana murna da dawowar da Daddy zaiyi saboda tanaso tayi masa maganar matsalar Abba, gara su zauna dashi suyi masa magana akan Budurwar sa Nadiya, yaushe zasuje anema masa auren nata, bazai iyu suci gaba da zama dashi hakaba

Iliyane yasake shigowa cikin part din, fuskarsa dauke da murna, yafara kiranta

Dasauri ta kashe oven din suka futo daga kitchen itada Momy, Momy ta zauna akujera tace “dama ni duk kin gajiyar dani, bari nadan huta”

Nihla ta kalli iliya tace “iliya danme qarfi lafiya kuwa?”

Yace “hajiya kinada wani Baqon ne, gashinan yashigo har ciki, yana compound”

Cikin mamaki tafuto harabar gidan, da wata hadaddiyar mota tayi tozali Ash color, qirar CAMRY, na cikin motar da yaga tafuto yabude shima yafuto, yagaidata tareda miqa mata wats takarda da key din motar yace “gashi inji yallabai”

Jikin Nihla yayi sanyi, yallabai kuma? Waye hakan? Cikin mamaki ta kalleshi tace “please waye ya aikoka?”

Yace “daga campany ne”

Daga nan ya juya yatafi, batare daya sake cemata komai ba

Motar ta qarewa kallo, tayi masifar yin kyau na qarshe, amma waye wannan dazai aiko mata da Mota?

Cikin sanyin jiki tajuya cikin falon su, Momy tace”yanaganki haka jiki a sanyaye, menene? “

Zama tayi kusa da Momy ta miqa mata car key din tace
“Momy Mota aka aikomin dashi”

Momy tace “Mota kuma?”

Daga kai Nihla tayi, Momy cikin sauri tatashi ta leqa taga motar Sabuwa ce dal sai daukan ido take, dole nema ta birge Wanda aka mallaka wa ita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button