DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Tadawo wajan Nihla tace “waye ya aiko miki?”
“nima bansaniba Momy, amma gashi harda takarda bari nagani”
Momy tace “duba kam” ????
Nihla tabude ‘yar qaramar takardar da aka hado da’ita tafara karantawa :
{ Ina tunanin Babu Wanda ya taba sanar da ke cewa_ murmushin ki abin so ne ga kowa,duk lokacin da kike yin murmushi yana mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai hasken gaske, You’re Beautiful, shiyasa akoda yaushe qwaqwalwata take zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata, wadda ta zamo abar kallo a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni daya cikin kadaici , murnar qarin shekara.
ABBA }
Gabanta ne yahau luguden faduwa bayan tagama karantawa, cikin ranta tace ya Abba!
Momy dake zaune ta kalleta cikin matsuwa tace “waye ya aiko miki”?
Gaskiya banda bakin godewa masu yimin sharhi akan wannan littafin, saide nace Allah yabarmu tare yabar zumunci, inajin dadin yanda kuke sharhi akan DANGI DAYA nagode ????????
Amnah El Yaqoub ✍️[7/7, 2:00 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
41&42
Gabanta sai faduwa yake, yayinda jikinta yayi mugun sanyi tadubi Momy tace “Ya Abba ne”
Ita kanta Momy saida tayi mugun mamaki, Abba kuma? Wannan yaron kuwa yasan meyake shirin janyo musu? Aqasan ranta tabbas tayi murna sosai yar’uwa da siyan motar, koba komai Kamar kansu yafara haduwa ne, amma ganin yanda Nihla tayi tsaye jikinta asanyaye yasa tayi Murmushi tace “Ah masha Allah, gaskiya Abba na ya kyauta, to menene kuma kikai shiru banga kina murna ba?”
Murmushin yaqe tayi “Momy ya Abba fa nace miki “
” aina jiki Nihla, naji abinda kika fada, to menene kuma Dan yayanki yasai miki Mota? Dama ai acikinsu shine baiyi miki Babbar kyauta ba tunda kika zo gidannan, kisaki ranki kije kici Gaba da aikin ki, idan yazo sai kiyi masa godiya”
Sai yanzu tayi wata irin ajiyar zuciya tace “to Momy”
“kin fadawa su Ilham kuwa?”
“eh Momy nafada musu, harsu ya Usman ma”
“to shikkenan, kije kici Gaba da aikin ki kiyi sauri Dan Allah”
Nihla na wucewa Momy ta kalli key din motar dake hannunta, Innalillahi wa inna ilaihir raju’un… ta dade tana zargin Abba nason Nihla, gashi yau ta qara gani da idonta, kome ya rubuta mata ajikin takardar? ???? Su suka sani, abinda tasani de shine itace mace ta farko dazata ziga Nihla akan karta kuskura ta amince wa Abba dukda shine danta mafi soyuwa acikin zuciyarta, Alhamdulillah da Daddy zai dawo gobe.
Tana aiki a kitchen amma zuciyarta tana wajan wannan kyauta
(ina tunanin Babu Wanda ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne ga kowa…)
Kalamansa suka fado mata arai, ta tsaya da aikin tayi shiru, yanzu shi ya Abbanne yaturo mata da wannan kalaman?To idan kyautar Mota Momy tace bawani abu bane, shikuma wannan kalaman fa? Amatsayin me zata daukesu?
Kanta datafe tace “kaiii ya Allah!” sannan taci gaba da aikin, tsaf ta shirya kek din yayi mutuqar kyau, Babban kek ne sosai data hada wiped cream fari da ja, tayi adon dasu, ta yankashi daga tsakiya tasaka cream din Wanda tadan disa jar color aciki, Sannan tasake rabashi tasaka farin kawai batare datasa komai ba, yanda idan ka yankashi zakaga cikin kek din yayi kaloli hawa biyu, sama fari, qasa ja
Momy tashigo kitchen din tana yin tozali da kek din tace “kai kai kai, masha Allah, amma gaskiya wannan kek din yayi kyau sosai yata, babu wanda zaigani yace kece kika yi”
Nihla tayi Murmushi kawai
Momy tace “yabaki rubuta sunaba? Ki rubuta sunanku ajiki, amma kifara saka naki sunan, sannan na Abba”
“to Momy”
Sauran cream din ta dauka ta rubuta Happy birthday Nihla & Abba
Momy tace “yawwa kinga saiya qarayin kyau sosai, kije kiyi wanka wadda zata miki kwalliya tana hanya”
Hannunta ta wanke tace “to Momy,”
sannan tafice daga kitchen din, Momy kuma ta kira Adala akan shirya abincin dazasuci anjima
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wanka tashiga tayi, tafuto daure da towel tana goge jiqaqqen gashin kanta Momy tashigo ta leda a hanunta tace “to gashi inji farouq yace ga tasa kyautar nan”
Cikin murna ta karba tabude ledar wani kwali ne Mai kyau babba, tabude taga riga me bala’in kyau ta bayyana, me launin pink,rigar daga qasan ta abaje take sosai gawani uban stone da taji , cikin murna ta rungume Momy, tace “Momy kiga rigar wallahi tayi kyau”
Momy tayi daria “yau kam aini ina ganin ikon Allah awajan wannan yan’uwan naki, kingani ko, wannan ne abinda nake fada miki dangane da kyautar da Abba yayi miki, shiyasa nace ki saki ranki”
Nihla cikin ranta tace Momy kenan Dan baki karanta abinda yake cikin takardar bane
Cikin sauri tashafa Mai da turere sannan tazura rigar, tajuya bayanta tace “Momy zugemin zip din”
Momy tarufe mata,rigar ta karbi jikinta sosai, breast dinnan sun futo sosai masha Allah
Momy tace “rigar kuwa tayi miki daidai Kamar danke akayi”
Zama tayi tafara gyara gashin kanta tace “wallahi Momy tayi kyau sosai”
Momy tafuto daga dakin, itama tana gama gyara kanta tafuto tasamu wata Babbar Cardboard paper ta yanki dede yanda takeso sannan ta rubuta Happy Birthday Nihla da biro sannan tadinga bin wajan biro din tana liqa stone’s ajiki fari da baqi, dakuma ja, sai rubutun biro din yabuya sai stone din kawai kake gani
Tafuto farkon kofar dazata kawoka cikin falon ta manna anan, Momy de tazama yar kallo sai bin Nihla take da kallo
Mai kwalliya ce tashigo tareda temakon iliya, nan suka baje afalo tafara yimata kwalliyar tagani tafada, tunma kafin agama Momy tayaba, da aka gama kuwa ita kanta maiyin makeup din saida tayi mata picture, gawani irin Style datayi mata na gyaran gashi, Momy kawai masha Allah take fada aranta, tabbas Abba ya cucesu, Inda ya aure ta ko banza wata rana zata haifa musu yara kamarta
Momy ta biya Mai kwalliyar kudi masu yawa sannan tasa driver yamaidata, ita kanta tasan yau tayiwa yar gata kwalliya
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da yamma su yaya Usman sukazo,gaba dayansu zaune suke afalo, ankawo musu abinci kowa yanaci
Futowa tayi suka gaisa gaba dayansu kuwa Babu Wanda bai yababa, Usman yana murmushi cikin ransa yana yiwa qaninsa fatan samun Nihla
Momy tasa Adala ta shirya falon da kek din dakomai, sannan ta shirya lemuka agefe, falon yaqara tsaruwa yayi kyau sosai
Direban Ilham ne yakai ta gidan Dida da Diyana suka daukosu suka Taho gidan gaba dayansu, zuwansu ne yasa Nihla tatashi sukai cikin dakinta dasu
Aliyu yace “Momy karfe biyar saurafa, me take jirane?ta yanka kek din mana muwuce ko”
Momy tace “lalle Aliyu yazama dole acika tara, kamanta da birthday din Abba kenan”
Aliyu yace “yasalam!, wallahi Momy namanta, yanzu kam nasan Wanda muke jira”
Usman yace “ni dama ban Manta ba, nasan yau Abba yake birthday, saikuma da Nihla takirani ta sanar Dani cewa itama tana birthday”
Farouq yace “um yau zamu ga yanda d’an miskilin Momy zai yanka kek, ko zai bawa Nihla,? Momy kina ganin bata kiwa?”
Tace “kaifa farouq haka kake dajan magana, saikace abokinka?”
Dariya yayi yace “Momy kinsan me, wallahi rannan nakama Abba yanata kallan pictures din Nihla, Kamar fa yana ciki”
Usman yace “nifa na dade da ganewa, kune de baku fahimta ba amma yanda yake kallanta ma ai ya’isa mutum yagane akwai wani abu”