DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Ajiyar zuciya tayi “Usman Nikaina nasan Abba yanason Nihla, amma bazan yi masa magana ba, zan zuba masa ido naga gudun ruwansa, ban qara tabbatar wa yana sonta sosai ba, sai yau daya aiko mata da Mota wai shine gift dinsa”

Gaba dayansu suka kwashe da dariya, Aliyu yace “lalle Abba, ko’itace wannan Sabuwar motar damuka gani a compound?”

Momy tace “itace Aliyu, kuma shi kansa yasan cewa abinda yake shirin yi bazai taba iyuba”

Usman yace “Momy saboda me? Meyasa zakice haka? Abba yanason ta”

“Usman ka Manta abinda Abba yayiwa Nihla ne?”

Yace “nasani Momy, abinda yafaru abaya yariga yafaru Momy, Abba da Nihla duka yaranki ne, Kibashi dama yanemi yafiyarta suyi aurensu”

“aure fa kace Usman, Hmm to ai ko Nihla ta amince saina zigata tarabu dashi, waye yayi wasa da damar sa?”

Farouq yace “Amma Momy munason kasancewar ta acikin mu ne shiyasa”

Shima Aliyu yace “Momy ni ina ganin abarshi da yarinyar yanemi yafiyarta yafi, ubangijin daya haliccemu ma muna masa laifi yayafe mana, ke kanki zakiji dadi ace Nihla ce matar Abba, akan yadauko wata yakawo miki, haba Momy kiduba mana”

Cikin fishi Momy tace “toku hademin kai saboda qaninku, yayi mata laifi kuma saiya gane kuskuren abinda ya aikata mata”

Usman baice da’ita komai ba yatashi yafuto daga falon yana kiran wayar Abba, ya sanar dashi cewa sutaho gida yana nemansa, bai fada masa cewa shi suke jira yazo a yanka kek ba

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Diyana ta kalleta “Nihla gaskiya kinyi kyau sosai masha Allah, Kamar amarya”

Cikin sauri tace “agidan ya Yusif ba, bari na kawo muku lemo, babu komai a fridge dina”

fita tayi tabarsu

Ilham ta kalli Dida da Diyana tace “wallahi akwai abinda nake zargi, kunsan Allah ya Abba naga alama yanason Nihla, bakuga abinda yamata ba rannan”
Nan take ta basu labarin komai

Adede lokacin Nihla takawo musu lemuka ta ajiye sannan tazauna

Diyana tace “aini Ilham haka nakeso, ya Abba ya haukace akan Nihla, yanda zataji dadin juya shi son ranta”

Ta kalli Nihla tace “wallahi idan nice ke ko, riga da wando zanyi ta sakawa a gidannan tunda momy ba magana zata mikiba, kidinga daukan hankalinsa”

Girgiza kanta tayi “bazan iyaba Diyana, dane da kaina yake rawa nake iya yimasa komai, amma yanzu ni, bazan iyaba, ina fata de yasoni,shima ya dandana abinda naji a raina, yaji irin quncin danaji a lokacin daya qini, nikuma daga baya sainayi aure na”

Dida tace ” gaskiya Nihla Kamar be kamata ba, tunda kowa yafara fahimtar yana sonka kibarshi da wannan ma ya’isa, meyasa zakike masa fatan yaqara sonki duk dan yaji abinda kikaji kuma daga qarshe ki auri wani bashi ba?

Nihla tace “Dida kenan, bakisan abinda naji bane, bakisan wahalar da zuciyata ta fuskanta ba, to wallahi rannan har kuka nayi, saboda taqaici na daya zaije wajan wata zance, hakan yana nufin bayasona kenan, nikuma nafiso yasoni ta yanda Zan nuna masa kuskurensa, sannan daga qarshe na auri ya Yusif, Kamar yanda shima yaqini yace zai Auro wata,da kam naso ya Abba Kamar hauka,kuma naji dadin yanda kukace yafara sona saboda lokaci yayi da zanqi shi na auri bare, Kamar yanda yaqini abaya yaso bare, amma a yanzu soyaiya ta kacokam takoma kan ya Yusif, shi nakeso, kuma shi Zan aura insha Allah”

Ajiyar zuciya Ilham tayi “to munji, komai de Yusif Yusif, to munji, saura kuma anjima kikasa bashi kek din” ????

Diyana tace “shikkenan Nihla, ni dama bazan miki dole akan ya Abba ba, saboda naji ciwon abinda yamiki nima, amma yanzu de tunda taro ne yahadamu anan, Dan Allah kiyi hakuri Karki bamu kunya, kiyi hakuri farin ciki ne yahadamu, kuma shi muke fata yarabamu, Kibashi kek dinnan a baki please “

“abakifa kikace Diyana, saikace wani ya Yusif”

Dida tace “ai roqonki mukayi, please”

Shiru tayi musu kawai, domin kuwa bata tunanin zata iya abinda suka nema

Ilham tace “zamu ga kyautar da ya Abba zai miki”

Nihla tace “Hmm gatacan kun ganta awaje”

Gaba dayansu sukace “Kamar ya”

Tace “Sabuwar motar datake compound shine ya aikomin dazu”

Gaba dayansu suka hada baki wajan fadin “Mota!”

Dida tace “um Ilham nayarda da maganar ki”

Diyana ma tayi daria tace “gaskiya nima nayarda yanzu, tab Mota! saikace Wanda kika kai masa budurci lafiya” ????

Nihla tace “Diyana banason Wulaqanci, ni wallahi da niyata nabashi key dinsa, amma wai sai Momy tace idan yazo namasa godia, ni kuwa ya Abba mezai fadamin”

Ahankali Momy taturo kofar dakin tashigo tace “toku kowa yazo ku ake jira”

Fita sukai gaba dayansu zuwa falon, sai fira suke cikin farin ciki

Da niyya Diyana ta kalli su ya Usman tace “ya Usman ba yanzu zata yanka bane?”

Kafin Usman din yabata amsa farouq yace “sai Abba yazo, suna hanya, yana zuwa zasu yanka tare”

Dariya ta kamata, Wato ta lura yaran Momy ma gaba dayansu jona Nihla da Abba sukeyi, tatashi tsaye tace “to mufara yin picture kafin yazo”

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Daga cikin motar suka futo shida Aslam, suna tafiya ahankali cikin aji, hannunsa daya yana cikin aljihun wandon suit dinsa,dayan hannun kuma yana riqeda wayarsa da kuma jacket dinsa

Ya kalli Aslam yace “kana ganin wannan kyautar kuwa zata birgeta?”

Aslam yace “sosai ma kuwa, kasan mata da Mota, sannan motar tayi kyau sosai, dole zatayi mata kyau Idan tahau”

Jinjina kansa yay”to amma wannan kalaman fa?”

Murmushi Aslam yayi” haba Abba, ai wannan ma nasan zasufi birgeta fiyeda motar, zasu tsaya aranta nake fadama, haba paper nawa muka ‘bata akan tsara kalaman? “????

Murmushi yayi shima Bece komai ba, cikin ransa yana fatan hakan, qarasowarsu part din keda wuya sukaci karo da rubutun da Nihla ta liqa awajan

Aslam yace” wow wow, Abba waye yayi mata wannan abun? “

Murmushi yayi”bansan waye yayi ba, batare nake dakai ba”

Aslam yace “a a, Abba kenan, Abba na Nihla”

Dariya sukayi suka qaraso cikin falon, ba sukai ga shigowa ba kuwa ya farouq ya kashe wutar falon baki daya

Ahankali Abba yace “subhanallah”

Kunnawa yayi haske ya gauraye falon, da’ita yafara yin tozali, cikin ransa yace ” Beautiful”

Itama ana kunna wutar falon idonta yasauka akansa, kalamansa suka fara dawo mata, nan take tayi gaggawar janye nata idon, tayi watsi da kalamansa daga qwaqwalwarta

gaba dayansu suka hada baki suna fadin ” Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday happy birthday to you… Suna qarasawa suka fara tafi kowa yana daria

Qamewa Abba yayi awajan yakasa motsi, ashe shirin da ake musu kenan shiyasa ya Usman yace yataho gida?

Ya Aliyu yace “to bamuda lokaci, azo ayanka kek, wannan yaron duk ya bata mana lokaci”

Dariya sukai gaba dayansu, Nihla de kanta yana qasa bata cewa komai

Ya Usman ya kalleshi yace “to Abba a qarasa mana, Aslam farouq Muje da Allah”

Cikin aji ya qaraso gaban kek din, mamaki duk yagama kamashi, Diyana ta janyo Nihla ta kawota kusa dashi, ita kuma ta tsaya daga hannun hagun ta

Sunkuyawa tayi zata yanka kek dinta, ya Usman yace “Nihla ya haka,? tsaya ayi pictures tukun”

Ya kalli farouq yace “farouq ayi musu pictures”

Ya farouq yafara daukan su pictures, gaba dayansu sunyi bala’in birge kowa, danma Babu wani Fara’ah da Nihlan take

Nihla kuwa jinta akusa dashi yasa duk ta takura, gashi sai binta yake dawani mayan kallo

Aliyu yace “Nihla ku yanka kek din mana, me ake jira”

Ahankali ta sunkuya zata dauki wuqar yanka kek din, adede lokacin shima ya sunkuya, yakai hannu takai hannu saijin Saukar hannunsa tayi akan nata hannun, gashi duk sun sunkuya hakan yasa dogon gashinta zubowa ta dede fuskarta, kallan hannunsu yayi, sannan ya juya ya kalleta, itama kallansa tayi tana masa nuni da idonta akan yadauke hannunsa amma saiya shareta Kamar bai ganeba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button