DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Hasken camera kuwa sai aiki yake awajan, saboda Babu Wanda basu birgeba, kowa zaiyi tunanin wasu shahararrun masoya ne

Ahankali ta motsa hannunta suka yanka kek din tare, sannan ta dago, shima yamiqe tsaye Ahankali

Bakinta zatakai kek din, Diyana tataka kafarta alamun tabashi amma sai tayi mursisi da’ita, takai kek din cikin bakinta

Aslam daya harde hannu aqirji yana Kallansu cikeda birgewa sai lokacin yayi magana yace “no!, Nihla Kibashi mana”

Cak ta tsaya da hannunta, ita bataci ba, ita bata bashi ba, ahankali ta juya tana fuskantar sa, tadaga kanta ta kalleshi saboda yamata tsawo, gani tayi idonsa akanta ko kunyar jama’ar wajan bayaji

Ahankali tadaga hannun Kamar bataso ta nufi bakinsa dashi, shikuma ganin Kamar zata bashi kunya agaban qannansa su Diyana yasa cikin aji yadora duka hannunsa biyu akan nata, wani irin zirrrr yaji ajikinsa sakamakon laushin dayaji hannunta yana dashi

Ahankali yakai hannunta bakinsa yakaryi kek din Dan kadan yaci, sannan yasake kai hannunta bakinsa yayi kissing bayan hannun nata,sannan yasaki hannun

Farouq dayaga pictures bazai yi ba saiya koma yimusu vedio kawai ????

Diyana datake ziga Nihla akan tabawa ya Abba kek abaki sai tayi shiru tana ganin ikon Allah, tana ganin yanda ake bawa masoyi kek, ita tana ganin idan an bashi abakin ma yayi, ashe shi nasa salon ya dame nasu

Shikuwa bejira komai ba ya yanko wani kek din Dan qarami yanufi bakinta dashi, qin bude bakin tayi, yazuba mata ido yana kallan Dan qaramin bakinta yace “Open your mouth”

Ahankali tabude bakinta yasaka mata kek din, gaba daya jikinta yayi sanyi,maganar su Ilham de tazama gaskiya

Yana saka mata duk falon aka hau tafi, sannan kowa yazo yayanki yanda yakeso, jiki a sanyaye Nihla ta zauna akujera, ta kalli ya farooq tace “ya farouq katuramin pic din ta WhatsApp gaba dayansu, harda Wanda nayi rannan a wayarka”

Cikin mamaki yace “wayata? No awayar Abba kikayi, yaturo miki”

Shiru tayi bata sake cewa komai ba

Momy tafuto daga daki tace “a a, har angama kenan naga kowa ya yanka yanaci”

Dariya sukai dukansu, cikin shagwaba Nihla tace “Momy shine kikaqi zuwa”

“in banda abinki Nihla abinku na yara mezai kawoni, fatana nide Allah yarayamin ku”

Gaba dayansu sukace amin

Abba ya kalleta,”Momy thank you, kek din yayi dadi sosai”

Murmushi Momy tayi tace “ai Nihla ce tayi da kanta, ita zakayi wa godia”

Wani irin dadi yaji acikin ransa, ya juya Yakalleta Bece da’ita komai ba, Sannan yatashi yace “nagaji” yakalli Aslam yayi cikin dakinsa, shima Aslam din yagane nufin sa danhaka yabi bayansa cikin dakin hannunsa dauke da Lil Abba

Saida su Dida sukaci sukasha sannan sukai shirin tafiya, amma ko waccensu da magana a bakinta, sai dariya sukewa Nihla ita kuwa ta sharesu

Saida sukai sallah sannan suka tafi, suma su ya Aliyu kowa yatafi, Momy tasa Adala tafara gyara wajan, ita kuwa Nihla dakinta tashige tazauna agefen gadon ta tana tuna abinda ya Abba yayi mata, idan tatuno yanda yayi kissing hannunta saitaji gaba daya tsikar jikinta tatashi

Haka tashiga wanka tafuto tayi sallah, tasaka kayan bacci masu kauri, sannan tazauna atsakiyar gadon tatafi duniyar tunani, yakamata ace ya Yusif yazo ko yaya ne taganshi, zamanta agidan nan tana hango yar qaramar qura, kowa cewa yake ya Abba yana sonta, Shin idan Momy da Daddy sukaji wannan batun yaya zasu dauki maganar? Su Ilham ma dasuke DANGI DAYA dashi suna bashi goyon baya to inaga iyauensa? Tasan cewa suma sai sunfi kowa murna, kuma da kunya tana zaune acikin gidansu taqi dansu na cikin su,abinda kunya, saide kuma yanda takeji aranta ko duniya da abinda yake cikinta ya Abba zai bata bazata iya auren saba kwata kwata, baba kansa yasan cewa ya Abba baya sonta, amma ya Yusif yayi mata komai, yaso ta a lokacin da Abba yagujeta

Saboda haka Tun ana yad’a jita jita a family gara tayi maganin abun Tun kafin ya furta mata kalmar soyaiya

Hannunta tadaga sama tayiwa Allah godia daya saka soyaiyar ta acikin zuciyar Abba, ko banza zaiji abinda taji abaya

Gift din ya Yusif tafara budewa

Bude ledar keda wuya kwalin Sabuwar waya qirar iphone ya baiyana
Murmushi tayi tace “Allah sarki ya Yusif”
Lokacin dazai siya mata waya tatuna, ya tambyeta wacce takeso tace iphone amma a lokacin kishi ya hanashi siya mata, shine sai yanzu kenan yasiyo mata

Kwalin wayar ta dauke anan taga wani kati Dan qarami Mai kyau sai sheqi yake, saikuma rafar kudi yan dari biyar guda daya, Wanda ta tattabar da cewa rafar dubu hamsin ne

Katin tabude taga rubutu aciki Mai kyau, nan take tafara karantawa :

Alkawari ne na dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu a cikin zuciyar ki ba matukar muna a tare da juna, ina fatan nan da dan wani lokaci kadan zaki tabbatar da hakan bayan kin zamo mallakina kuma mata a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Nihla,naso nazo naciyar da mata ta kek da kaina amma aiki yamin yawa, dafatan zakimin uzuri, Happy birthday

Tana gama karantawa tayi kissing katin, tace “i luv u ya Yusif”

Wayarta tadauka ta kirashi, ringing din farko yadaga, cikin farin-ciki tace “ya Yusif, irin wannan gift haka, gaskiya naji dadi nagode sosai, i luv u so much dear”

Murmushi yayi tareda lumshe idonsa “saqona ya’iso gareki kenan”

“yes, yazo, kuma wayar tamin kyau sosai, naji dadi”

“da gaske kinji dadi?”

“emana ya Yusif, naji dadi sosai”

Yace “to tayaya Zan gane hakan?”

“mekakeso nayima Wanda zaka gane?”

Yace “um think about it”

Fari tayi da idonta Kamar yana ganinta tace “to idan kasamu time kasamu baba kayi masa magana akan soyaiyar mu, kaga shikkenan dana gama service sai bikinmu “

Sosai Yusif yayi mamakin kalaman ta, Murmushi yayi yace “Really?”

Tace “yeah”

Murmushi yasaki har tana jiyoshi sannan yace “gaskiya naji dadi, nagode sweethrt,kuma zan sameshi a gobe muyi maganar, zan fadawa Abbana ma, but yanzu yaya taron?”

“Alhamdulillah ya Yusif, komai yayi daidai, rashin daidai dinsa shine baka nan”

“to kiyi hakuri, tuba nake, idan nasamu time zaki ganni verry soon”

“to shikkenan ya Yusif thnks”

Yace “yr wlcm”

Daga nan sukai sallama.

Momy ce taturo dakin tashigo, cikin murna Nihla tanuna mata abinda Yusif din ya aiko mata dashi

Murmushi Momy tayi, tazauna abakin gadon, saide wannan ne karon farko da taji tausayin Abba aranta, saboda yanda taga Nihla tana farin-ciki akan kyautar da saurayinta yayi mata, saide Babu yanda zatayi, dole sai Abba yagane laifin dayayi abaya, bazata biyewa son zuciya dason datake wa danta ba

cikin nutsuwa tace “nagani Nihla, Yusif yayi kokari sosai, amma dafatan de dashi za’ayi ko ‘yar Momy?”

Ahankali tadagawa Momy kai cikin kunya

Momy tayi Murmushi “to shikkenan, idan kunyi waya dashi kifada masa momynki tana gaishe shi, sannan kifuto muci abinci, goma saura yanzu”

Ahankali tace “to Momy”

Falon suka futo itada Momy, yana zaune shi kadai a dining yana daddanna waya, tunani yake aransa meyasa har yanzu Nihla bata sakewa dashi tayi masa magana Kamar da? Bayan kuma tasan cewa shi bawata magana yakeba dama can

Yayi tunanin dazu da farouq yace pictures dinta suna wayarsa zatace yatura mata, amma sai yaji tayi shiru, yarasa me zaiyi mata tadinga sakewa dashi suna magana Kamar da

Zuwansu wajan ne yakatse masa tunanin dayake, Nihla ta kalleshi yana sanye da jallabiya fara qal wadda ta karbi jikinsa, sumar kansa ta kwanta luf tana sheqi gwanin sha’awa, hankalin sa yanakan waya

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button