DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Abba najin haka cikin ransa yace Innalillah.., yayi shiru Kamar ruwa ya cinye shi

Daddy yaci gaba da fadin “nadade inama kallan marar lafiya ashe ba haka bane kalau kake tunda gashi har kana rashin lafiya akan haka, ina ita yarinyar dakace kanaso din take, inane gidansu sai Muje ayi magana guda daya, ka dade da sanar damu cewa kana sonta, amma maganar aure kayi shiru”

Shiru Abba yayi, idonsa yayi jajir, ga kunyar iyayen nasa dayakeji Ahankali yace “Daddy tayi aure”

Cikin sauri iyayen suka kalleshi, Daddy “to shikkenan Allah yakiyaye gaba, sai kayi kokari kasamo wata ka aura, bazai iyu kaci gaba da zama da rashin lafiya ba”

Jinjina kansa yayi yace “insha Allah Daddy”

“zaka iya tafiya”

Ahankali yatashi yafuto daga dakin, ta gabanta yazo yawuce yashige dakinsa, itade Nihla taga shigar sa daki Kamar yana cikin damuwa, tabe baki tayi taci gaba da kallonta

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Bayan sati daya tana kwance tana bacci da weekend kasancewar bazata ko’inaba
Wayarta ce tahau ruri cikin magagin bacci takai hannu tadauki wayar cikin sexy voice tace “Hello”

“Baby na kina bacci kenan”

Tace “Um”

Murmushi yayi “to albishirinki”

“goro ya Yusif”

“yau ina kan hanyar zuwa naganki, aide adress din dakika taba turomin kina nan ko?”

Bude idonta tayi “ya Yusif da gaske kake zakazo?”

“Yes, yau zanzo insha Allah, yanzu hakama wanka zanyi nabiyo jirgin dazai tashi 12”

“wayyo ya yusif, mekakeso na shirya ma?”

“Karki wahalar min da kanki, kiyi zaman ki kawai”

Murmushi tayi, amma Babu yanda za’ai zaizo takasa shirya masa wani abu

Daga nasa bangaren yace “me kikeso nataho miki dashi?”

“mamy ya Yusif, ita nakeso, nayi missing dinta”

Murmushi yayi yace “tunda zaki ganni ai Kamar zaki ganta ne”

“to shikkenan ya Yusif sai kazo”

Tashi tayi taje ta sanar da Momy, nan da nan kuwa Momy ta aiki Adala kasuwa tasiyo musu abubuwan buqata, Adala tana dawowa suka hau aiki itada Nihla,ko sau daya bataga Abba yafuto ba, may be baya gidan ne, aikin sukaci gaba dayi lokaci daya gida yadauki qamshin hadadden girki

Saida Nihla taga komai yayi normal sannan taje tashiga wanka

Karfe biyu saura yakirata yace yana bakin get
Kwalliyar datayi ta doguwar riga ta atamfa ya karbi jikinta, tayi mutuqar kyau sosai
Da kanta tafuto taje ta taryoshi daga bakin get,ta karbi key din motarsa tabawa Direban gidan tace yashigo masa da ita

Yusif sai Kallanta yake, kwalliyar tata tayi bala’in tafiya da imaninsa, ahankali suke ta kowa gwanin sha’awa har suka qaraso part din Momy, Nihla sai Fara’ah take, a falon suka zauna Momy tafuto suka gaisa, tayaba da Yusif din Babu laifi, cikin sakin fuska tace “yaka baro mutanan Abuja” yace “Alhamdulillah, suna lafiya wallahi”

“aaa masha Allah, ai kullum muna jin labarinka awajan Nihla”

Yusif yayi Murmushi cikin ransa yana yabon matar

Tashi tayi tace “bari akawo maka Dan ruwa, Alhaji yafita aida kun gaisa dashi “

tatafi tasa Adala takawo masa kayan motsa baki dakuma Abincin da aka shirya masa

Kallanta yayi yace “wannan ce Momy ko?”

“itace ya Yusif”

“tanada kirki gaskiya, idan naje gida saina fadawa baba cewa kina nan kalau wani kyau ma kike qarawa”

Murmushi tayi masa, tatashi tazuba masa Abincin, yafaraci, Dan kadan yaci yace ya’isa

Yakalleta yace “Nihla gaskiya bazan boye miki ba ina qaunar ki, kuma naji dadin yanda naganki hankalin ki kwance, fatana mu kasance inuwa daya amatsayin Ma’aurata nanda Dan wani lokaci qanqani”

Kallansa tayi “ina fatan hakan ya Yusif”

Fira sukaci gaba dayi har yamma tayi, yatashi yayi sallah suka dawo falon suka zauna, wayarta ce tayi ringing, cikin zolaya tace “bakada kirki yaron nan”

Daga daya bangaren akace “ninema yaron, gaskiya kin cuceni, koke aka kawomin yanzu tsaf Zan riqeki”

Dariya tayi “lalle ma Abdallah, aikuwa baza’a kawo makaba, yakake yagida, ya service”

“gida lafiya Nihla, dama nashigo kano ne shine zanzo mugaisa saina wuce”

“Ok to shikkenan abdallah saikazo, zan turoma adress din gidan yanzu”

Wayar ta katse ta kalli Yusif “ya Yusif abdallah ne yakirani, wai zaizo mugaisa”

Yace “Ok Abdallah qanin Nadiya qawarki”

“eh shi”

Yace “to saiyazo, ina pictures din birthday din naki baki turomin ba, nunamin nagani” ????????‍♀️

Hankalinta kwance tabashi wayarta tace “gashinan suna cika duba kagani”

Bude wayar yayi yashiga gallery anan yaga pictures din, lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya yace “ashe bake kadai kikai ba”

Jikinta ne yayi sanyi “eh nida ya Abba ne”

Tabe baki yayi yabata wayarta, sannan yatashi yace “toni Zan tafi”

Shagwaba tafara masa “haba ya Yusif, ya za’ai katafi Tun yanzu, karfe hudu nefa”

Jiyayi ta birgeshi, yace “karfe hudu nakeso nabi jirgi nakoma, bakina tareda wani masoyin nakiba, menene zaki damu?”

“saboda ina sonka, kuma kai zuciyata ta’aminda dashi shiyasa nabaka dama ka gabatar da soyaiyar mu awajan mahaifina”

Yaji dadin maganar ta, kuma ya gamsu sosai, danhaka shima ya lallabata yace bayason yayi missing flight ne, daqyar ta yarda, takira masa Momy sukai sallama sannan suka futo harabar gidan tare domin tayi masa rakiya

Awajan motarsa suka tsaya suka jingina da motar, sai kallan soyaiya suke sakarwa junansu, yabude bayan motar yabata wata leda cikeda coculate, ta karba tayi masa godia, yace “to Zan tafi, mezaki fadamin Wanda Zan dinga tunawa ina jin dadi”

Murmushi tasakar masa har dimple dinta suka futowa sosai, adede lokacin maigadi yabude wa Abba get yashigo ciki

Dasu yafara tozali, lokaci daya gabansa yayi mugun faduwa, jikinsa har rawa yake yana neman yakasa driving din, hakan yasa yafaka motar tasa a’inda bai kamata ba, waye wannan yake tareda Nihla? Wanne dan’iskanne yazo yasakata agaba ita kuma sai wani murmushi take masa?

Cikin sauri yabude motar yafuto, fuskarsa adaure, Dafarko yayi niyyar zuwa wajansu, amma saiyayi hakuri yarabu dasu yazo yawuce su ko kallan Yusif din baiyi ba

Yusif ya kalleta da mamaki “waye wannan?”

Tabe baki tayi sannan tace “ya Abba”

Nan take shima bacin rai ya wanzu a fuskarsa ????????‍♀️

Falon yashigo anan yaga kayaiyakin da’aka ajiye da alama wannan gayen aka sauka dasu, zama yayi akan kujera yadafe kansa????????‍♂️, lokaci daya idonsa yayi jajir, to zaman mema zaiyi anan? Meyasa zai zauna yanacin Baqin ciki ita kuma tanacan tareda wani? Lokaci daya wani irin kishi ya rufe masa ido, glass cup din da’aka kawowa Yusif domin shan lemo yasa qafa yayi ball dashi, lokaci daya cup din yahadu da bangon falon ya tarwatse awajan, cikin bacin rai yafuto daga falon yanufi wajan Nihla da Yusif

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Cikin kuka tace “mum wallahi Tun safe nakejin qaiqayin, Tun yanayi Dan kadan yadawo yanayi dayawa, idan nasosa ma sakeji nake”

Hajiya Farida tace “Dida, to kiyi shiru kidena kuka mana, ba komai gane sanyi ne yake damunki, kuma muddin kina dashi to shima Fawaz din zai iya samu, kina amfani da Ruwan zanyi ne?”

Tace “eh mum inayi”

Hajiya Farida tace”to ai kinji, Dida Tun kuna gida nake muku magana akan Ruwan sanyin nan, kidena tsarki da Ruwan sanyi, sannan idan kina period kwata kwata kidena shan Ruwan sanyin ma bare kiyi tsarki dashi ko wanka, kiyi shiru zansa akawo miki magani yanzu, shima Fawaz din saiki bashi yadinga sha “

Tashare hawayen ta tace” to mum, mungode “

Yana zaune agefenta yayi tagumi, yace” to yanzu kinsa itama hankalinta zai tashi, bayan nace Karki fada mata kinqi ji, tunda safe fa nakira ummah nima nafada mata, kuma tacemin zata kawo miki magani da kanta “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button