DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Fuskarsa yadora akan hannayenta dayake cikin nasa hannun yayi shiru, lokaci daya Nihla taji ruwa yana sauka akan hannunta, hakan ya tabbatar mata da cewa kuka yake

Momy dake kallansu lokaci daya taji qwallah tacika idonta ganin yanda Nihla take kuka shima ya tsugunna a gabanta yana mata kuka

Dago kansa yayi ya kalleta idonsa yayi jajir, ganin taqiyin magana yasa Ahankali yatashi tsaye, har lokacin kuma hannunta yana cikin nasa

Dora hannun nata yayi akan qirjinsa yace “zaki iya Rayuwar aure dawani batare daniba?”

Hannunta ta qwace daga kan qirjinsa, ta kalli idonsa tace “ya Abba, wacce irin magana kake min haka? Kasan abinda kake fada kuwa? Saboda banda gata ne yasa zaka nemi kayi wasa da rayuwa ta? Alokacin dana soka nunamin kayi baka qaunata, baka duba maraicin mahaifiyata danake tare dashiba Alokacin haka kace baka qaunata cikin bainar jama’ah, mutanan dakake cewa narabu dasu sune suka soni, suka qaunaceni Alokacin da dan’uwana ya nuna baya qaunata”

Hawaye yacika idonta, bata damu data goge ba taci gaba da cewa “Inda ace mahaifiyata tana raye, bazata taba bari hakan tafaru daniba, Tun banda wayo nasan cewa Diddi tasoka ya Abba, amma kai kaqi abinda tahaifa kaso Nadiya, to idan baka saniba Anty Nadiya itace tanusar dani nasan menene rayuwa, ta nunamin maisona da maqiyina, amma yau dan’uwanta yazo wajena kaci masa mutunci, da kaqini, sai yanzu da hankalina ya karkata wajan wani sannan zakace kana sona? ta yaya? Impossible! “

Tasa hannu tashare hawayen idonta sannan tawuce tabarshi awajan

Zuwa wannan lokacin kam Momy ma sun sata kuka, hawaye yacika fuskarta

Shikuwa Abba kansa ne yayi mugun sarawa, yazube awajan yana fadin” Innalillahi wa inna ilaihir raju’un… “

????Um jama’ah rikicin Mazawaje family naga alama ba qarewa zaiyi ba saide mu taqaita, nagaji wallahi, yakamata mu huta haka, kuma zaku Dan huta da Comments, Mutara zuwa jibi ko gata insha Allah, nagode ????????

Amnah El Yaqoub ✍️
[7/10, 1:36 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-10548777110149

45&46

‘Da uwa sai Allah, tausayin Abba yakama Momy, ta kowa tafarayi Ahankali zataje wajansa, saikuma ta fasa tajuya cikin dakinta itama saboda bataso yaran su fahimci cewa tasan abinda yafaru atsakaninsu

Agefen gadon ta tazauna tafada duniyar tunani, ada kam abinda tasa aranta shine koda Nihla ta amincewa Abba itada kanta zatasa karta amince, to ashe awajan Nihla itama hakanne, ashe bata son Abban a yanzu, ashe tunanin ta qarya yake bata,da gaske yarinyar bata qaunar Abba, amma yaya zatayi? Tanajin Nihla acikin ranta Tun tana qarama, tanajin ta Kamar yarta ta cikinta, ba zatayi mata dole akan Abba ba, dole zasu bata haqqinta, tazabi Wanda ranta yakeso, hakan shine adalci, amma Abba Babu kunya yakama yarinya yana mata kiss? ????
Baya tsoron tazo wajan ko Daddy

Nihla nashiga daki tashare hawayen idonta, tafara cire kayan jikinta domin ta watsa ruwa,akan gado tazubar da kayan nata, daga ita sai towel tashige wankan, kokadan bataji tausayin ya Abba ba, koma menene shine yajawa kansa acewarta

Abangaren Abba kuwa awajan Yazauna yadafe kansa, idonsa sunyi jajir tsabar kuka, bai taba tunanin cewa watan watarana zaiyi kuka akan soyaiya ba, amma gashi na farko yayi kukan Baqin ciki akan Nadiya, yanzu gashi yana kuka na biyu shikuma kukan nadama akan Nihla, ahankali yatashi tsaye jiri yana dibansa, yashige cikin dakinsa, akan gado yafada yadauki wayarsa yakira Aslam, bugun farko Aslam yadaga yace “Abba yane”

Cikin muryar kuka yace “komai yaqare Aslam…, komai yazo qarshe, tace bata sona”

Aslam yayi shiru Kamar an doka masa sanda
Yasaki ajiyar zuciya yace “Abba wannan shine abinda nake gujema Tun farko, meyasa zakayi magana Awannan lokacin? Yanke hukunci cikin fishi banaka bane, a lokacin Abba Kowama yana jin abinda kake ji, duk cikin mu Babu Wanda yake son wannan hadin da akayi mana, amma haka mukai shiru, amma yanzu de kayi hakuri, nasan cewa Nihla zata soka”

“bazata soniba Aslam, yarinyar nan har tsugunna mata nayi nabata hakuri, amma taqi yafemin, saima laifukan dana aikata mata abaya tasake maimaita min, Aslam tayaya zata yafemin idan tana tuna abinda nayi mata? Yanzu shikkenan mutum bazai iyayin kuskure ba a rayuwa kuma yadawo ya gyara? “

” Abba!!, kaima fa abinda kayiwa yarinyar nan bashida dadi, dole zata tuna, saide Ahankali ta Manta “

Cikin hawaye yace” kuma sai tace bazai iyu tasoni ba “

” kayi hakuri Abba, amma ka denayin kukan nan, insha Allah nima Zan tayaka addu’ah zata soka, mu miqa lamuranmu ga Allah, shine kawai mafita “

” Aslam bazata soni ba, tsanata nake gani qarara akan idonta, wallahi idan taqi aure na Allah saina saceta “????????‍♀️

????Zaro ido Aslam yayi” a a Abba ba za’ayi hakaba, babu maganar sata, mubi komai Ahankali “

” wani fa takawo gidan Aslam, agabana take masa murmushi, Allah idan yasake zuwa wajan ta saide ayi biyu Babu, zan kasheshi nima nakashe kaina tunda haka takeso “

Aslam yayi Murmushi, Abba da kishi sai Allah, afili yace” Abba, kayi hakuri, kaci gaba da bata haquri, amma kasan abinda zamuyi yanzu? Mufara gyara sama tukunna, Abuja zaka shirya Muje munemi mahaifin ta mufara bashi hakuri, sai aci gaba daga inda aka tsaya “????

Jan zuciya yayi yace” shikkenan ” qit ya kashe wayar

Ilham ta dafa Aslam tace” meyake faruwa ne? “

” nida Abokina ne, yanason qawarki sosai amma tana bashi wahala, yayi laifi yanaso ya gyara laifukan dayayi mata amma taqi bashi damar hakan, yanzu abnda yake fadamin har tsugunna wa yayi a gabanta yabata hakuri amma taqi yarda “

Ilham ta zaro idonta cikeda mamaki tace” ya Abban? “

” shikuwa, ai soyaiyar Nihla nema take tahaukatashi Kamar yanda taki ta haukatani, kika hanani kallan ko wacce mace “

Murmushi tayi tace ” ya Aslam kenan, amma ina tausayin ya Abba gaskiya, Dan Nihla koda yaushe muka hadu sai munyi mata maganar sa, amma sai takawo maganar saurayinta “

Cikin damuwa Aslam yace” akwai damuwa de gaskiya, Allah yashiga cikin lamarin kawai”

“amin” cewar Ilham

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

After one week

Kwance suke akan gado, ta dora kanta akan qirjinsa, yayinda hannunsa yake kanta yana shafa mata, yace “Baby Dida kinga maganin nan na ummah wallahi yayi kyau sosai, gashi yanxu shiru kake ji Babu kowacce damuwa”

Idanunta a lumshe tace “Um, Allah yakiyaye gaba, amma ai zamuci gaba da sha”

Yace “to, duk yanda kikace haka za’ayi”

Kanta ya daina shafawa yatura hannunsa cikin blanket din dasuke ciki yana shafa qirjinta, rabuwa tayi dashi yana abnda yakeso, amma da aka jima taga abinnasa bana qare bane, kawai saita fara masa kukan shagwaba “ya Fawaz yanzu fa kagama, nide Dan Allah muhuta…”

“Baby Dida kadanfa Zan qara, bazan dadeba kinji”

“naji, amma gaskiya daga wannan shikkenan ko”

Murmushi yayi yace “um inajin”

Itama Murmushin tayi masa daganan suka lula duniyar Ma’aurata

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke afalo itada Momy, wayarta tayi qara, tana dubawa taga baba ne, cikin girmama wa tadaga suka gaisa yace “Yusif yazomin da wata magana yace kece kika bashi dama yazo muyi magana ko?”

“eh baba nice nace yayima magana”

“to yamin magana, amma kuma yace kinfada masa wai saikin kammala service tukunna, menene abin jira Nihla, tunda Allah yakawo miji kawai ayi aure, auren ki na farko matsala ce tasa ba’aiba, amma yanzu tunda gashi kinsamu ilmi ai Babu abinda zamu jira, amma mahaifin Yusif din baya nan, idan yadawo daga tafiyar dayayi zamuyi magana akan hakan insha Allah, idan ma aurenne sai ayi, inyaso saiki qarasa service din agidan mijinki “

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button