DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Kallansa tayi, “na’am Abba”
Yace “Momy nasha wahala bazan sake dawowa garin nanba”
Murmushi Momy tayi “a a Abba karka ce haka mana, kaida nakeso duk wata kana zuwa kana duba Nihla” ????
Nihla ta kalleshi tasaka daria, shima Kallanta yayi yadauke kansa, amma baiyi mata ko murmushi ba
Suna zuwa kofar gidansu Nihla tasake saka daria, Abba yajuyo ya kalleta, su kuwa su Momy da Diddi rabuwa sukai dasu suka shige gida
Yace “me kikewa daria?”
Saida tasake yimasa daria sannan ta kwaikwayi maganarsa tace “Momy nasha wahala bazan sake dawowa garin nanba”
Haushi tabashi sosai,beyi wata wataba yasa hannu ya tureta tafadi aqasa
Da gudu ya qaraso wajan, tun daga nesa yake kallansu, shima yana qaraso wa yasa hannu yabige Abba yace “me tayima zaka bigeta?”
Cikin bacin rai Abba yace “menene ya shafeka? Qanwarkace ko qanwata?”
“bansaniba, amma idan kasake tureta, saina rama mata” yana fadar haka ya tsugunnawa yadaga Nihla tatashi tsaye
Cikin fishi Abba yasa hannu ya fizge hannunta yace “cika mata hannu!”
Shima dayan cikin tsawa yace “bazan cika ba!”
Lokaci daya ransa yaqara baci, ya kalli Nihla batare dayace mata komaiba ya shige gida
Itama dayan ta kalla tace “yusif…”
Kafin taqarasa maganar da zatayi yace “karkiyi kuka, idan yadakeki ki fadamin Zan rama miki kinji?”
Daga masa kai tayi, sannan tashige gida
Tana shiga taga Diddi tana ha’bo, Abba yana zuba mata ruwa abuta, bata wani damuba saboda tasaba ganinta ta nayi, rana d’ai’dai ne Diddi bazatai ha’bo ba, Dan haka hauka irinna yarinta dakuma gani yauda kullum yasa bata damu sosai ba, wajan Momy ta nufa tafada jikinta tace “Antyyy” ????Girgiza kai Momy tayi, har cikin ranta bataso antyn nan da Nihla take fada, sotake tadinga kiranta Momy Kamar yanda sauran yaranta suke fada, har zatayi mata magana saita fasa
Diddi nagama wanke fuskarta suka dawo tabarma suka zauna, Abba yace “Sannu Diddi, idan na girma Zan kaiki asbiti”
Daria Momy tayi, “wannan girma wannan girma, zamu gani dai, ga umara ga hajji, yau kuma anqara da asbiti ????”
Diddi na goge fuskarta da gefen zaninta tace “kuma insha Allahu duk saiya cikasu”
Momy tayi daria tace “muma haka mukeso aisha, wai dama har yanzu kina wannan ha’bon naki? Aisha yakamata kije asibiti fa kiga Babban likita akan haka, kina zubar da jini dayawa”
Murmushi Diddi tayi “Anty Rahma kenan, to Tun muna yara mukeyi nida yaya, saide ni nafishi yi, kuma Tun umman mu tanada rai muke zuwa asibiti, maganin dai dayane ake bamu, kuma anan ma inashan irinsa, amma bandainaba, shiyasa nake yanka albasa ina shaqar qamshin nata, shima yana maganin ha’bo sosai”
Farouq najin haka yace “to Diddi bari na yanka miki yanzu ma, yatashi yadauki wuqa yanufi wajan da take ajiye albasa”
Nihla ta kwaikwayi Abba tace “Sannu Diddi” ????
Kallanta yayi yasakar mata harara, yadauke kansa, Momy tana kallansa, cikin ranta tace to da alama sunyi fada ????
Saita kalli Diddi tace “to Allah yasawaqe aisha, amma Zan sake yiwa yayanki maganar gaskiya,abin yayi yawa”
Babu musu Diddi tace to, Dan itama abin yana damunta, wani lokacin tana bacci zataji jini yana futowa daga hancin ta
Har dare, Abba Yaqi kula Nihla, da niyya take tsokanar sa amma saiya shareta, idan ya tuna abinda yafaru dazu a kofar gida shida wannan gayan sai yaji haushi ya kamashi ????
Shiyasa itama yarabu da ita, da daddare ma ko kallan Inda take baiyiba, ita kuwa bata fasa tsokanar saba, har sukayi bacci
Washe gari da yamma sunata shirin tafiya, Nihla duk tayi shiru bataso sutafi, har direba yazo yagama zuba musu komai nasu amota, kowa yayi wanka ya shirya, dukansu qananun kaya suka saka
Momy ta kalli Diddi, “to Aisha zamu tafi”
“to Anty Rahma Allah yakaiku lafiya, idan kinje ki gaida kowa,”
Momy tace “to yayanki fa?”
Daria Diddi tayi, “harda shi Anty Rahma, ki qara yimasa godia, ki gaishe shi sosai”
Tace “to zaiji, yanzu Aisha Allah bazaki bani Nihla ba?”
“Anty Rahma rigima, sokike na zauna nikadai agidan de” ????
Momy da taga alamar Aisha bazata iya rabuwa da Nihla ba, sai tayi shiru kawai, suka futo, har kofar gida suka rakosu itada Nihla, suka tsaya daga bakin kofa suna kallansu
Yaran kowa yashiga Mota, Nihla tanata kallan Abba, shima ita yake kallo, lokaci daya idonta yayi rau-rau, tasaka kuka tace “Diddi zasu tafi”
Hannu Diddi tasa tashare mata hawaye, jikin Abba ne yayi sanyi, Dasauri yabude motar yafuto, duk ‘yan uwansa suna kallansa, har gaban Diddi yaje, ya tsugunna agaban Nihla yace” kiyi shiru, kefa qawata ce, You’re my friend “
Kallansa tayi ta daga masa kai alamun to
Saida ya kalli Diddi, sanan yamatso da fuskarsa daidai tata, yasakar mata kiss akumatu
Zaro ido ????Nihla tayi tana kallonshi, kafin tayi magana yajuya ya shige motarsu da gudu
Qamewa Diddi tayi a tsaye, Abba datake ganinsa shiru shiru shine yayiwa Nihla haka? ????
Momy kuwa murmushi tayi, tace “Allah ya kyauta” ????
Sannan tayiwa direba umarni yaja motar sutafi
Cikin gida Diddi tajuya tashige, tana tunanin wani abu aranta
Nihla kuwa qin shiga gidan tayi, tazauna akofar gidansu tana wasa, Kamar daga sama taji maganarsa “Nihla, mekike yi anan kinyi shiru?”
Kallansa tayi, lokaci daya tasaki murmushi, “yayunane suka tafi, nikuma banaso sutafi “
“haba? Yaushe suka tafi? Kinsan garin da suka tafi?”
Girgiza kai tayi, “nima bansan garin su ba”
Hannunta yariqe yace “zomuje gidanmu muyi wasa”
Gidan dayake kallan nasu gidan ta kalla, hadaddan gida ne daya gama haduwa, harda beni, tace “to Muje”
Janta yayi suka shige cikin gidan, har falonsu suka shiga Nihla sai kalle kalle take, mamansa tana zaune tana kallo, falon ya tsaru iya tsaruwa
Kamannin Ibrahim Mai hakuri da tagani a fuskar yarinyar hakan ya tabbatar mata da cewa yarinyar Diddi ce
Wajan ta suka qarasa yace”Ummah kinga qawata, sunanta Nihla, Acan gidan take naje na kirata zamuyi wasa “
Murmushi tayi, tashafa kan Nihla tace” a a masha Allah yanmata, to kuje kuyi wasan, banda fada kunji ko “
Dakinsa yakai ta, nan taga kayaiyakin wasa iri iri, nan take suka fara wasansu, yana koya mata abinda bata iyaba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Har bayan sallar isha’i Nihla bata dawo gidaba, Diddi tayi neman ta harta gaji, haka ta tsaya akofar gida tana Tambayar duk Wanda taga yazo wucewa ko yaga Nihla, amma Babu Wanda yace yaganta
Umman yusif tazo rufe window tana daga saman beni, hango Diddi a tsaye akofar gida
Saukowa tayi tafuto wajan ta sameta, Diddi tace “a a Hajiya, ina gajiya,”
Tace “lafiya kalau, da alama de Nihla kike nema”
Dasauri Diddi tace”wallahi ita nake nema hajiya, Tun yamma ban ganta ba, “
Murmushi tayi tace” ai tana gidana, sunata wasa da yusif Yarona, yanzu kam nayi musu shimfida ma sunyi bacci “
” to bari naje nadauko ta hajiya, kar babanta yadawo begantaba “
” haba Diddin, ki barta mana, dasafe sai akawo ta “
Murmushi Diddi tayi, cikin ranta tace nagode Allah, kowa yana qaunar ‘yata, afili tace” Hajiya ai wataran zata kwana, ina Ruwan yara “????
Badan tasoba, suka shiga gidan, Diddi tanata yaba haduwar gidan, Dan bashiga takeba, amma gashi yau wannan yarinya takawo ta
Baccinsu suke hankali kwance, ga esi nan yana sanyaya musu jiki, haka Diddi tasa hannu tadauketa, suka tafi gida, tanata yiwa Maman yusif din godia
(idan naga ana Comments Zan qara yawan page d’in)