DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Momy tace “Abba, nasan halin ka sarai, idan bakaine ka fasa mata wayaba waye zai fasa? Adala bata nan, dagani saikai sai ita dakuma Daddynku, mune zamu fasa wayar kenan?”
Cikin kishi dakuma wata irin murya Kamar zaiyi kuka yace “to Momy meyasa zata dinga waya dawani can, bana fada mata banaso ba”
Hawaye suka zubowa Nihla ta kalli Momy tace “Momy ai kinji shi ko? Allah saiya biyamin wayata”
Tashi yayi tsaye ya kalleta, ya girgiza kansa, sannan ya sunkuya yadauki wayarsa da jacket dinsa daya cire yayi hanyar dakinsa
To,ko Alhaji Abubakar zaibawa Ibrahim hakuri akan abinda yafaru abaya?
Yaya labarin abdallah qanin Nadiya ne? Anya kuwa zai iyayin shiru akan abinda yagani dangane da Abba da Nihla?
More Comments more typing….????????
Mrs Usman ce ✍️
[7/11, 12:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
47&48
Momy tayi zuru da ido tana Kallonsa, gaskiya ne karabu da miskilin mutum, ka kalleshi kawai, kagama yiwa yarinya kuka ka matseta kayi kissing dinta amma kaduba kaga Kamar bashi ba, kome yataka oho?
Usman yace “Nihla kiyi hakuri kidena kuka kinji, zanyi masa magana saiya nemo miki waya wayar, kiyi shiru”
Ahankali yatashi yabi bayan Abba, zaune ya sameshi yayi tagumi hannu bibbiyu, zama yayi a gefensa
“Abba!, meyasa zaka fasa mata waya, tayaya zata soka ahaka Abba?”
Kallan yayan nasa yayi, qwallah tacika idonsa, bai iya boye waba danhaka yabasu damar zubowa, jikin ya Usman yafada, cikin hawaye yace “yaya ashe kowa yagane halinda nake ciki? Yaya zanyi da soyaiyar ta yaya?”
Usman ya shafa kansa “kadena kuka mana”
“dama wannan shine abinda muke gujema tunda farko” Aliyu daya shigo dakin yafada
Gaba dayansu suka daga kansu suka kalleshi, farouq ma yashigo dakin sannan Yarufe
Zama sukai duk su hudun, Aliyu ya cigaba da cewa “yanzu wa gari ya waya? Kai taurin kai gareka Abba, yarinyar nan kowa yasan tasoka, amma ka Qita, tayaya zata soka yanzu?”
Hawaye suka zubo daga idanun Abba, Usman yace “Abba na hanaka kukan nan, kuka bazai kawo mafita ba”
Cikin hawaye yace “ya Usman kabarni nayi kukana, cewafa tayi batasona, kuma bata barni hakaba saita dinga kula wasu”
Dariya takama farouq, bai boye ba yasaki dariyarsa ????
Wani irin haushi yakama Abba, yazuba masa ido yana kallansa batare dayayi magana ba
Saida farouq yagama dariyarsa yace “wallahi banga laifin Nihla ba, gara ta gwaraka ka gwaru”
Cikin haushi yace “Aidama nadade da sanin sonta kakeyi, ai shikkenan”
Farouq yayi Murmushi yace “ahhh ina son Nihla,wayace ka Qita? Lokacin dakace baka sonta nace Zan aure ta kaji haushi nane? Sai yanzu dakake sonta ne zakace ai dama kasan ina sonta, a a ina auren ta”
“dan Allah kuyi mana shiru munemo kanmu mafita” cewar Aliyu
Gaba dayansu kuwa sukai shiru, ya Usman ya kalli Abba yace “Abba kishi banaka bane, ka lallabata kagane? Kabata kulawa, kuma ka sameta kasake bata hakuri, kai Abba inta kama ma saika tsugunna a gabanta ne, to kayi inde hakan zaisa tahuce”
“ya Usman har hakan fa nayi mata taqi yarda”
Aliyu da farouq suka saki murmushi, lalle Abba da gaske yake
Shima ya Usman din murmushin yayi yace “naji, kaci gaba da bata hakuri, insha Allah wani lokacin zata hakura”
Aliyu ma yace “yawwa kuma naga Kamar Momy ma tanabin bayanta, yakamata kasamesu itada Daddy kuyi magana, amma wannan fishin naka akan ankirata awaya Babu Inda zai kaika”
Haka yan’uwan nasa suka sakashi agaba sunayi masa huduba, dakuma shawara akan abinda zai kawo musu mafita
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune yake agaban iyayen sa,acikin dakin Daddy, kansa aqasa, Momy tana zaune agefen Daddy, yayinda hankalin Daddy yake kan news din da akeyi
Saida aka gama sannan ya kashe, yajuyo ya kalli Abba yace “Abubakar muna jinka, kazo kace akwai maganar dakake so muyi, amma kayi shiru”
Gabansa ne yafara faduwa, yarasa ta Inda zaiyi wa iyayen nasa bayani
Momy tace “kayi shiru Abba”
Ahankali yadago kansa ya kallesu sannan yasauke idonsa cikin sauri,”Am.. Daddy dama…. dama inaso ne infada muku inason yin aure”
Murmushi ya baiyana a fuskar Daddy, amma Momy kuwa Kallonsa tace, tanaso taji yafadi abinda ta dade dasani
Daddy yace “wacce Abba? Alhmdllh ashe de kaji fadan damukai ma”
Ahankali yadaga kansa alamar yaji
Momy tace “to Wacece? Ko wata yar Abujan kasamu?”
Kallanta yayi ya girgiza kansa alamun a a
Daddy yakalli Momy yace “ikon Allah, kinga yau Abba kunyar mu yakeji”
Momy tayi Murmushi batace komai ba
Daddy yace “to a wanne garin take? Saina tura su Alhaji Baqir suje su nema ma auren ta, Wacece?”
Karon farko da Abba yaji tsoron mahaifin sa, gabansa sai faduwa yake, jikinsa yayi mugun sanyi, har wata irin karkarwa yakeyi
Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace “Nihla ce Daddy”
Lokaci daya, annurin fuskar Daddy ya dauke
Yamiqe tsaye yace “zancen banza, zancen wofi, Abubakar ashe bakada hankali bansani ba?”
Yasake maida kallansa wajan Momy yace “toke Rahma idan kin gama sauraren abinda yake fada, saiku tattara kufita, nima zanje daki nahuta” yana fadar haka yafara takawa zai tafi dakinsa
Caraf yasa hannu yariqe kafar mahaifin nasa, kansa aqasa, amma yakasa Dagowa, Daddy jin anriqe masa kafa yasa ya tsaya cak, hawaye ne yake disowa daga Idanunsa, numfashin sa yafara sama sama Kamar Mai Asma, yasaka hannunsa daya ya goge, yayinda dayan hannun yake riqe da qafar Daddy
Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace “Daddy please, Dan girman Allah Daddy kayi hakuri kuyafemin irin laifin danayi abaya, Daddy ka tausayamin wallahi ina sonta….” ya qarasa maganar yana sakin wani irin kuka Mai cin rai
Daddy yajuyo ya kalleshi yace “Abba!, kalleni nan, niba mutumin banza bane, kuma niba qaramin yaro bane dazaka raina wa hankali, saida kasa natara mutane agabansu ka nunamin ban isa dakai ba, yarinyar nan akan ka aure ta kazabi karbar Mazawaje family, sai yanzu zakazo min da wata irin magana, kaga da Allah, tashi kafice kabarmin dakin nan indena ganinka “
Ahankali yamiqe yadafe kansa dayake masa muguwar sarawa, yakalli Momy da jikinta yayi sanyi yace” Momy, Dan Allah Kibashi hakuri, kuyi hakuri Momy wallahi zuciyata zafi takemin, Momy inason Nihla “
Momy tace” Abba ai lokaci yaqure ma, Nihla akwai wanda takeso, sannan mahaifin ta yayi magana da ita akan hakan, kaine ka janyo koma menene, katashi kafice kawai, banason maganar banza “
Hawaye yasake zubowa Abba, shikkenan Babu wani Mai goyon bayansa kuma, tunda Momy ma tace haka to Babu Wanda bazai iya juya masa baya ba
Duhu duhu yafara gani, ahankali yafara takawa sai jiri ne yake dibansa, hannunsa yana dafe da kansa, haka yatafi yabar falon na Daddy yana tafiya yana hada hanya
Hawaye ya zubowa Momy, tana tausayin Abba sosai amma dole zataso yagane dai dai da abinda ba dai dai ba
Cikin sauri tatashi zatabi bayansa Daddy yace “Karki kuskura kije Inda yake, kinji nafada miki”
Yana fadar haka ya juya yashige dakinsa ransa duk abace
Momy ta zube akan kujera tana sakin wani irin kuka Mai ciwo
Jikin bango yakebi yana tafiya Kamar Mai koyon tafiya, sakamakon duhun dayake gani acikin idonsa, da haka ya qarasa dakinsa yazube akan gado yana sakin kuka sosai abaiyane, nan take wani irin zazzabi Mai zafi ya rufeshi