DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“Abdallah yakirani awaya yafadamin komai, meyasa kika boyemin gaskiyar ke Wacece Nihla?”

“Anty Nadiya… Dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan ta yanda za’ai nayi miki bayani ba, Anty Nadiya ya Abba ke yakeso, kuma a lokacin dana hadu dake kuna tare da juna, yana sonki kina sonsa, meyasa Zan rusa muku soyaiyar ku, bazan iyaba, shiyasa nayi shiru ban fada miki alaqa ta dashi ba, duk family dinmu kowa Abba yake cemasa, nahadu dake naji kince sadiq Mazawaje, banyi tunanin shi bane saida kika nunamin pic dinsa, kuma daga lokacin nake sporting dinsa awajan ki, harga Allah banso kikaqi auren saba, saboda banji dadi ba kokadan Anty Nadiya, koma meyayi min shidin dan’uwana ne,nida shi munkance cikin DANGI DAYA, duk da yayi min laifi wallahi banso kika Barshi ba, amma kiyi hakuri Anty Nadiya akan rashin sanar dake dabanyi ba “

Ajiyar zuciya Nadiya tayi” nafahimceki Nihla, sai da abdallah yafadamin komai nasan cewa bakida laifi, Sadiq yahadu Nihla Nikaina nasan da haka,ashe ba banza ba kika rikice, Nikaina rashin kulawar sa ce tasa narabu dashi, amma Abdallah yacemin yaga soyaiyar ki sosai acikin idonsa, hakane? “

” hakane Anty Nadiya, yafadamin ma, kawai de bazan iya sauraron sa bane, kuma nafada masa “

” eto yakamata de yasan darajar ki gaskiya, sai kiyi addu’ah Allah yazaba miki mafi alkhaairi, idan ansa ranar bikin saiki sanar Dani “

” munyi maganar ya Yusif da baba ma Anty Nadiya, insha Allah idan ansa Zan sanar dake “

” to shikkenan qanwata Mai yan samari, sai munyi waya, kicewa sadiq Nadiya tana gaishe shi “????

Murmushi Nihla tayi tace” Babu ruwana Anty Nadiya, kunfi kusa kedashi “

Da haka sukai sallama

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Sanye take da atamfa Mai launin pink da brown, dinkin riga da siket ne amma Yazauna a jikinta sosai, mayafi tayafa dan qarami iya gefen kafadarta daya, yayinda data riqe hand bag dinta tafuto daga cikin dakinta, da alama unguwa zataje, adede lokacin shima yafuto idonsa yasauka akanta, tayi mutuqar yimasa kyau sosai, kasa dauke idonsa yayi akanta harta qaraso ta gabansa zata wuce shi batare data kalli Inda yakeba, hannu yasa ya fuzgota, lokaci daya tafada jikinsa, bai jira komai ba yasaka ta cikin qirjinsa ya rungumeta sosai

Tudun nashanunta dayakejinsu akan qirjinsa ne yasa ya lumshe idonsa, sannan yaqara matseta tsam ajikinsa, jijiyoyin jikinsa suka fara karbar wani irin saqo, wani irin zirrr yakeji tundaga tafin qafarsa har zuwa kansa, kansa yasake turawa cikin wuyanta yana shaqar wani sihirtaccen qamshi dake tashi a jikinta, bayaso yadena jin abinda yakeji ajikinsa, baiqi ace su dauwama ahaka ba, ahankali yadago bakinsa, yadora Dan qaramin lips dinsa akan kunnanta yana gatsawa Ahankali

Wani irin numfashi Nihla tasaki, gabobin jikinta suka saki lokaci daya

Motsi tafara tanaso taraba jikinta danasa, cikin shagwaba tace “ya Abba please kasake ni mana, Momy fa zata iya zuwa”

Wata irin murya yayi magana da’ita, wadda tunda take dashi bata taba Jin muryar sa hakaba, cikin shagwaba yace “to kice kin yafemin mana please “

Ahankali ta zare jikinta daga nasa ta kalleshi tace “ya Abba kenan, kada kadamu, nayafe maka, komai yawuce kaji ya Abba na, duba kaga yanda ka rame, Pls kasaki ranka kaji?”

Yace “da gaske kike kin yafemin?”

Tace “ya Abba, nace nayafe ma, komai yawuce fa, Muje ka rakani unguwa….”

Cikin sauri yafarka daga mafarkin dayake ????????
Sakamakon qaran wayarsa data tashe shi, a dalilin wani abokin aikinsa dayake kira

Kansa yadafe da hannunsa duka biyu ya furta kalmar “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un…” ????????‍♂️

Jikinsa yataba yaji zafi sosai, ga kansa dake sara masa, zuciyarsa ce yaji tana tashi, cikin sauri yasauko daga gadon yanufi toilet yafara kwara amai, babu komai acikinsa sai riqe cikin sa yake ga ciwon kai, ga zazzabi, haka yadawo ya kwanta agadon, yanzu duk abinda yafaru dama mafarki yake? Ya Allah!

Saida yaji dama dama sannan ya koma toilet din yayi wanka, yadauro alwala yafuto, jallabiyar sa yasaka fara qal da ita, sannan yatada kabbarar sallah, yadade yana sallah sannan yadaga kansa ya kalli agogo yaga sha biyu da kwata

Ahankali yamiqe, yafuto daga dakin nasa, kai tsaye dakin Nihla yanufa, wannan shine karon farko daya fara shiga dakinta

Ahankali yatura kansa cikin dakin, tana kwance agado wayarta da ya yusif ya aiko mata take gani, tana sanye da riga da wando na bacci, wandon ko gwiwar ta baizoba, rigar ma batada tsawo hakan yasa fararen cinyoyinta suka fara futowa

Ganin mutum kawai tayi akanta, cikin sauri tatashi zaune tace “subhanallah… Ya Abba lafiya?”

Ahankali yake ta kowa har yazo gabanta, ganin yana nufota yasa taja blanket din kan gadon tadora a jikinta

Bai tsaya a ko’inaba saida yazo saitin qafafunta, yazuba gwiwar sa aqasa har kafarta tana gogar gwiwar tasa

Shiru yayi yazuba mata ido yana Kallanta, Bece da ita komai ba

Nihla sai kallan mamaki take masa tace “lafiya ne?”

Ahankali, cikin sigar rada yace “kiyi hakuri”

banda dare ne kuma su kadai ne a dakin Babu abinda zai hana takasa jin Mai yace

Tace “for what”

“for Everything, please kiyafemin, nakasa bacci, hankali na yakasa kwanciya, meyasa bazaki yafe minba Nihlaaaa” ya qarasa maganar yanajan sunanta

Shiru tayi masa batace komai ba, Yakalleta yaci gaba da cewa “nasa ranki yabaci saboda nafasa miki wayarki, kiyi hakuri, insha Allah bazan sakeba, but kidena waya agabana, raina yana zafi, idan kikaci gaba dayi zan’iya fasa gaba dayan wayoyin hannunki, Allah ne yasakamin kishin ki acikin zuciyata, bazan dena ba kuma saboda ina qaunar ki, Nihlaaa! kidubi girman Allah kiyafemin, kisoni”

Kallansa tayi, mamaki ya kamata, lalle ya Abba

Ahankali tace “idan kagama inaso Zan kwanta, a tunani na mun dade da gama wannan maganar, babu abinda yayi saura bayan wannan”

Tana fadar haka takwanta, tajuya masa baya sannan taja blanket dinta tarufe jikinta dashi gaba daya

Bayanta ya kalla, yau shi Nihla take juyawa baya, shine yasa kafarsa aqasa yana neman yafiyarta amma taqi, yau shida Nihla takeso shine takasa bashi soyaiyar ta akaro na biyu

Dumin dayaji akan kumatunsa ne yasa yagane hawaye ne suka zubo masa, ahankali yasa hannu ya share, yamiqe yafuto daga dakin tareda ja mata kofar dakin

Yadade awajan ya tsaye idonsa arufe, tsayuwa ma neman gagararsa take, cikin damuwa ya juya yana tafiya ahankali Kamar zai fadi, yayi hanyar dakinsa

Momy ta duba gefenta taga Alhaji yayi bacci, ahankali ta sauko daga kan gadon tafuto daga dakin nasa, Allah nagani bazata iya runtsawa batare dataga halinda yaranta suke ciki ba, dakin Nihla tafara zuwa taganta tana bacci amma wutar dakin akunne, tasa hannu ta kashe mata wutar sannan tajuya, Nihla tana jinta, saboda ba bacci takeba

Dakin Abba tanufa, tana budewa taganshi azaune atsakiyar gadonsa yana kuka wiwi

Gaban Momy yafadi, cikin sauri ta qarasa wajansa tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un… Abba!!”

Tana qaraso wa wajansa yafada jikinta, kansa tashafa tace “me yafaru?”

Ahankali yazame yadora kansa akan cinyarta, cikin kuka yace “Momy bata sona, naje wajanta yanzu taqi kulani, Momy zuciyata zafi take min, rannan ma nabata hakuri taqi kulani Momy, yanzu ma haka,Momy ya zanyi? Wallahi ina sonta, kowa Yaqi bani goyon baya, shikkenan ni Kowama ya tsaneni…” hannu tasa tarufe masa baki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button