DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Wani irin sanyi yaji aransa, koba komai yana jin dadin yanda take kiran sunansa, gaba daya jiyake Kamar tafi kowa iya fada
Idanunsa har wani lumshe wa suke yadago yazuba mata wani irin kallo Mai karya garkuwar jikin yanmata ????
Cikin kulawa yace “lafiya”
Daga haka bata sake cemasa komai ba, Momy ma taji dadin yanda Nihla koda wasa bata raina yayun nataba, gashi de Abba bawani shiri sukeba, ba qaunar sa takeba, amma tana bashi girman sa yanda yadace
Momy tace “Nihla jeki kitchen kidaukomin wannan garon, saiki kaiwa maqota”
Ahankali tatashi, yana jin tashin ta yadaga kansa yabita da kallo, ba komai ne yafi daukar hankalinsa ba irin hips dinta, Momy ta kalli Abba taga inda hankalinsa yake ta girgiza kai ????
Saida yaga tashige sannan yasaki wata ajiyar zuciya Mai nauyi, yamaida hankalinsa ga abinda yake
Murmushi Momy tayi cikin ranta tace oh Abba, babu ta ido, inaga mantawa yake da kowa idan Nihla tana waje, agefe daya kuma tausayin dannata yana damunta
Goron takawo da alawa Momy tafara yimata bayani “kikai duka gidajen Dan Allah, idan an tambayeki na menene kifada musu, idan kuma bazaki iyaba kice su kirani awaya”
Tace “to Momy”
Kasancewar unguwar Babu mutane sosai yasa tasaka hannu ta kunce Babban dankwalin kanta, gashin kanta yazubo gafen fuskarta, tasa hannu ta maida shi baya sannan tayafa dankwalin a jikinta kasancewar da girman sa, tadauki goron tanufi hanyar fita
Cikin sauri yatashi yasha gabanta yaje bakin kofar falon ya tsaya, daga Momy har Nihla mamakin yanda yayi tsalle yaje bakin kofar dakin ya tsaya suke ????
Shikuwa ko ajikinsa yace “haba Momy Dan Allah, ya za’ayi kibarta tafita ahaka, haka kawai taje tadauko mana magana”
Momy ta girgiza kanta “Abba kabata hanya tawuce mana, menene haka”
Cikin shagwaba yace “gaskiya Momy a a”
Momy ta dubi Nihla tace “dawo ki zauna Nihla, bani goron”
Babu musu tadawo tazauna tareda bata goron
Momy ta kalleshi tace “to tunda ka hanata kaiwa, gashi saikazo kakai”
Yace “wai goron menene ma Momy, saikace masu shirin taro”????????♀️
Momy kanta tsaye tace “goron saka ranar qanwar ka ne, na saka ranar auren Nihla ne”
Wani dummm! Yafara ji akansa, gabansa yafara faduwa, numfashinsa yafara yin sama, daqyar ya’iya cewa “Momy saka rana kuma?”
Momy data fara tsorata da yanayin sa yace “emana, menene?”
Hannu yasa yadafe kansa dake masa mugun ciwo, qirjinsa ya riqe numfashi yana neman gagararsa, ahankali yadora dayan hannunsa akan qirjinsa, Idanunsa suka fara rufewa, yafara ganin duhu-duhu har suka rufe gaba daya yadena gani dajin komai, nan take ya sulale awajan yafadi
Cikin sauri Momy tayi kansa tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihir raju’un…. Abba!”
Girgiza shi tafara yi amma Babu alamar numfashi awajan Abba, gaba daya Momy ta rikice sai jijjigashi take, hasbunallah wani’imal wakil… Abinda take guje musu kenan dama, nan take hawaye ya balle mata
Ta kalli Nihla cikin kuka tace” yi sauri ki kira Daddynku mutafi asbiti”
Da gudu tajuya zuwa dakin Daddy yana zaune yana duba jarida, ganin yanda tashigo dakin hankali tashe yasa yatashi tsaye da sauri yace “lafiya?”
“Daddy kazo inji Momy”
Cikin sauri yafuto itama Nihla ta biyo bayansa, yana qarasa wa wajanda Abba ke kwance ya tsugunna yana taba fuskarsa yace “meyasa meshi ne Rahma?”
Cikin kuka tace “Alhaji kaga abinda nake fadama ko? Kaga irinta ko? Babu abinda aka masa, kawai dagajin ansa ranar Nihla shine yayanke jiki yafadi”
Daddy yace “subhanallah… Kamamin shi Muje asbiti”
Daqyar suka dagashi, suka tafi asbiti baki dayansu, sai adala kawai aka bari agidan
Zuwan su asbiti keda wuya likitoci suka karbe shi cikin gaggawa, suka shiga bashi temakon gaggawa, Daddy da Momy kam kasa zama sukai, sai Nihla ce take bawa Momy hakuri akan tadena kukan datake amma ina! Hawaye Yaqi tsayawa a idanun Momy
Sun kusa awa daya da zuwa asibitin sannan likitocin suka futo, cikin sauri suka nufesu suna tambaya
Babban cikin su yace “kuyi hakuri Alhaji, ku kwantar da hankalin ku, amma Dan Allah ku kiyaye fadar abinda zai dinga tsorata mutum lokaci daya, yanzu haka danku yaji abinda ya tsorata shi ne sosai, shiyasa yasuma, kuma dama bugun numfashin sa ba normal yake fitaba sakamakon ciwon da zuciyar sa take son kamuwa dashi “
Daga Momy har Daddy hada baki sukai wajan fadin
” ciwon zuciya Doc.?
Kai tsaye yace “qwarai kuwa, amma tunda kunzo asbiti insha Allah zamuyi kokarin ganin yasamu lafiya, yanzu za’a futo dashi a sauya masa daki”
daga haka ya juya yabasu waje
Momy kasa magana tayi daga nan, kawai de tana goge hawayen idonta, kuma har zuwa yanzu kokadan batajin haushin Nihla, fatanta daya, Allah yabawa danta lafiya
Daddy yakira Alhaji Basiru da Alhaji Baqir ya sanar dasu abinda yake faruwa, nan take suma suka Garzayo asbitin
Cikin lokaci qanqani jinyar Abba tacika family din Mazawaje
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Aslam yafi kowa shiga cikin tashin hankali, musanman daya tambayi Momy menene yake faruwa tafada masa komai bata boye masa ba, haka Yazauna yana tunanin mafita
Nihla ya hango tareda Ilham azaune agefe, tana riqeda lil Abba a hannunta
Ahankali yataka yaje wajansu Yazauna, yadubi Nihla tareda miqa mata wayarsa yace “qanwata temakamin da number Angon namu mana”
Murmushi tayi kadan, ta karbi wayar tasa tasaka masa number ya Yusuf aciki, sannan tabashi, ya karba yayi godia
Wayarta ce tahau qara, tana dubawa taga ya Yusuf ne, tadauka
Ilham da Aslam suka kalleta, cikin zazzakar muryarta yace “hello ya Yusuf , yakake yagida”
“lafiya amarya ta, nashigo kano fa, zanzo naganki inaso naji shirye shiryen dakika tsara, saina wuce daga nan”
“Ayya ya Yusuf ai bana gida, munzo asbiti ne, saide nayima kwatancen wajan saimu hadu anan, kaga sai Muje gidama nahadama wani abin kaci”
Be tambayeta waye baida lafiya ba yace “toki turomin adress din Inda kike yanzu”
Sunan asbitin kawai tafada masa yace yana kusa, tace to zata futo waje bakin titi Inda zai ganta
Wayar ta kashe tadubi Ilham tace “zanje waje nadubo ya Yusuf “
Ilham tace “to shikkenan”
Ahankali ta miqe tafuto, Aslam ya kalli Ilham yace “kibita mana, kidan bata shawara ko zata saurareki”
Kallan mijin nata tayi, duk yashiga damuwa, tarasa wacce irin soyaiya sukewa tsakanin su shida ya Abba, tace “to” sannan ta biyo bayan Nihla
Daga murya tayi ta kirata, Nihla ta tsaya ta, sannan ta qaraso sukaci gaba da tafiya
Ilham tace “ya Aslam ne yace nazo naraka ki”
Nihla tace “Allah sarki, kinga salihin miji, wallahi idan ya Abba ne bazai bar matar saba”
Murmushi tayi tace “nikam Nihla nabaki shawara mana”
“inajinki” cewar Nihla
Shiru Ilham tayi, saida suka qaraso bakin titi suna jiran ya Yusuf ya qaraso sannan tace “Nihla Dan Allah meyasa bazaki tausaya wa ya Abba ki aure shiba?”
Cikin sauri ta dago kanta ta kalli Ilham tace “aure fa kikace Ilham”
Hannunta Ilham takama hannunta ta riqe tace “eh, aure nace Nihla, to menene aciki idan kin aure shi? Nihla wacce irin zuciya gareki?yaushe kika koma haka? Mutumin nan yayi miki laifi kuma yabaki hakuri, babu wanda baya aikata kuskure acikin Rayuwar sa Nihla, saide na wani yafi na wani,kidinga tunawa ya Abba dan’uwana ne da’aka bar wasiyya cewa kuyi aure, Nihla ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi muroqeshi gafara yayafe mana, haba Nihla, yanzu ashe bazaki iya tausayawa yaron Momy ba? Bazaki iya ceto yaron Daddy daga halin da yake ciki ba? Nihla wannan shine sakayyar dazaki nunawa Momy kenan? matar da tasoki Tun kina qarama kina gaban mahaifiyarki? Duk cikin yaran Momy Babu Wanda ya qyamaceki Nihla, kowa kokari yake yaga yafaranta ranki, Momy tana qaunar ki Nihla, Inda wata uwarce da tuni ta sauya miki, suna qaunar dansu fa, soyaiyar dasuke miki ce tasa bazasu iya nuna miki komai ba, idan kina tuna laifin dayayi miki bazaki taba yafe masaba, kuma bashi zaki dubaba, a a, iyayen sa zaki duba, kinji de abinda likita yace, zuciyarsa tana gab da kamuwa da ciwo, kuma komai yana hannun ki, idan kinso zaki iya ceto Rayuwar Dan mutanan dasuke kaunarki Kamar yarsu ta cikin su, idan kuma kinso zaki iya barin sa, amma kiyi tunani akai “
Tana gama fada mata tayi shiru tareda sakin hannunta