DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Zuciyarta fal da tunanin maganganun Ilham, tabbas maganar ta Babu ta yarwa aciki, Momy uwace abar alfahri ako’ina, to amma baban ta fa? Tayaya zata iya nusar dashi? Tayaya zata fuskanci ya Yusuf da wannan maganar? adede lokacin yaqaraso wajansu, suka gaisa cikin kulawa, ahankali suka qarasa cikin asbitin
Ya kalleta yace” yanaga jikinki yayi sanyi ne? Waye baida lafiya? “
Murmushi tayi tace” lafiya ta kalau ya Yusuf , ya Abba ne baida lafiya, dukanmu ma muna ciki, ko zaka qarasa ku gaisa da Momy duk suma suna ciki “
Yace” why not “
Ahankali suka qaraso cikin asbitin, cikeda kulawa Yusuf ya gaisa da kowa, sosai Momy ta ware suka gaisa dashi Kamar Babu abinda yake damunta
Suma su Daddy sun yaba da halin sa sosai, kowa dayake wajan yayaba da tarbiyarsa, babu laifi yanada nutsuwa
Likita ne yazo yace zasu iya shiga su ganshi yanzu, gaba dayansu kuwa suka nufi dakin
Yana kwance hancinsa sanye da oxygen, ga kuma na’ura agefen kansa tana aiki, dakuma wadda take nuna yanayin hawa da Saukar numfashin sa
Cikin sauri Momy ta qarasa wajansa, ta dora kanta agefen gadon tasaki wani irin kuka, tama kasa magana sai kuka datake sosai
Hajiya Farida ce tazo ta janye ta tana bata baki, gaba daya dakin Babu Wanda bai tausayawa Abba ba, ajikin hajiya Faridanma bata dena kukan ba, tari yafara Ahankali, duk hankalinsu saiya dawo kansa, Tun yana tari Ahankali harya dawo yanayi sosai, Aliyu yayi sauri yakira likita, likitan na zuwa yace Dan Allah su fita daga dakin, gaba dayansu suka futo
Aslam yaja Yusuf gefe suna magana, wadda Babu Wanda yasan akan me suke tattaunawa saboda sunyi nesa da mutane
Saida suka gama magana sannan Yusuf yakira Nihla, suka tafi zata rakashi wajan motarsa, har tana mamakin wacce iri magana ya Aslam yayi masa? Kuma menene dalilin karbar number sa awajan ta?
Har gaban motarsa sukaje yashiga Yazauna amma bai rufe motar ba, ta kalleshi tace ” banji kace komai ba, akan maganar da mukai waya”
Memakon yabata amsa sai yace “Wancen gayen yacemin sunansa Aslam, yayi min magana akan ki, yace ma ya karbi number ta awajan ki zai kirani kuma sai akai sa’ah nazo, yafadamin saboda ke Abba yake rashin lafiya, kece maganin damuwar sa, yayi min bayani sosai akan hakan, kuma na gamsu da bayanin sa, Nihla why not muhaqura ki auri Abba?”
Mutara zuwa gobe insha Allah ????????
Sharhi please
Amnah El Yaqoub ✍????[7/12, 9:57 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
51&52
Lokaci daya idanunta suka cicciko da qwallah, ta dubeshi muryarta na rawa tace “ya Yusuf… Mekake fada hakane? Meyasa zaka qini saboda shi?”
“ba saboda shi nafadi wannan maganar ba Nihla, kinsani ina son ki, tunda kina qarama, Tun bansan menene so ba nake tare dake acikin zuciyata, halin da suke ciki shida iyayen sa zaki duba, mutanan nan sun karbeni hannu bibbiyu Babu Wanda ya nunamin komai ko akan fuska, sunada karamci Nihla “
” yanzu me kake nufi kenan?”
” ki auri Abba Nihla”
Batare daya shiryaba hawaye yazubo masa yasaka hannu ya goge cikin sauri sannan Yarufe motar tareda dora kansa akan sitiyarin motar yana kuka
Kallansa tayi tasaki wani irin kuka tareda juyawa ciki aguje tana kuka
Usman dake zaune gefensu Daddy yace “yanzu Daddy ai sai a fadawa su baba Ibrahim adaga wannan aure na Nihla, mu dangin mahaifiyarta bamu shirya ba, saboda Abba bashida lafiya”
Alhaji Baqir yayi Murmushi yace “naga alama de Usman bakason wannan auren ko”
Kansa ya sosa yace “A a kawu, danaga wai hankali ba’a kwance yakeba”
Murmushi yasake yi, amma Daddy de yayi shiru baice komai ba, zuwa yanzu kam kodan ceto Rayuwar dansa yakamata yaje su Gana shida Ibrahim Mai hakuri, yakamata su shirya suje su sameshi
Cikin kuka tashigo wajansu, gaba daya hankalinsu yadawo kanta, Nihla kuwa bata zarce ko’inaba sai wajan Momy, fadawa tayi jikinta tana kuka sosai, Momy tace “me yake faruwa Nihla?keda waye?”
Shiru tayi takasa bata amsa, mezatace mata? Saboda ance na auri danki nake kuka kome? Dan haka tayi shiru, Momy tasa hannu tafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, haka tayi shiru amma cikin ranta wani kukan takeji tanaso tayi, Ilham tataso tace” kitashi mukoma can “
Babu musu tabi Ilham suka koma gefe sai Jan zuciya take, Ilham bata tambayeta dalilin kukan ba, tabarta tagama hucewa tukunna
Nihla tayi shiru tana tunani, ita kuma tata qaddarar kenan, sai anzo auren ta afasa, yanzu gashi shima yace ta auri Abba, hakan yana nufin za’a sake fasawa kenan akaro na biyu
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari Alhaji Basiru da Alhaji Baqir dakuma Daddy da Alhaji habib mijin hajiya Farida suka shirya sassafe suka nufi Abuja
Saukarsu keda wuya Alhaji Isma’iel da baba sukayi musu masauqi acikin falon nasu, baba sai mamaki yake irin wannan zuwan nasu
Saida suka gama gaishe gaishe sannan Daddy yadubi ma hakuri yace “Ibrahim wajan ka mukazo gaba dayanmu nan da qoqon bararmu, haqiqa munyi maka laifi abaya, kuma muna qara neman kuskure, ba kuma komai ne yasa nina aikata hakaba saidon kaunar yar’uwata Aisha dakuma abinda kuka haifa, Awannan lokacin kokadan banaso nayima magana akan Zan dauki Nihla natafi da ita, saboda nasan yanda kake jin mutuwar Aisha kaima bazaka so karabu da yarka ba, nikuma ina qaunar yarinyar, hakanne yasa nadauke ta muka tafi, maganar aure kuma da bamu sanar makaba wannan ma mun dauki laifin mu, amma maganar gaskiya itace banine nayanke wannan hukuncin ba, iyayen mune, bawai ikona bane hakan, amma kayi hakuri “
Baba yayi Murmushi yace”haba Alhaji, ai Babu komai, komai yariga yawuce, rannan ma kuwa Shima Abubakar yazo shida Aslam”
Mamaki yakama su Daddy, ashe su Abba sunyi hankali, Alhaji Baqir mahaifin Aslam yayi Murmushi cikin ransa yace shikkenan ma sun rage mana hanya, yadubi baba yace “ai Abubakar dinma bashida lafiya, yana kwance a asbiti yanzu haka, zuciya ce takeson yimasa ciwo, amma batakai ga farawar ba”
Alhaji Isma’iel yace “subhanallah… Subhnllh, kode shine yaron da Yusuf yake fadamin bashida lafiya?”
Baba yadubi Alhaji Isma’iel yace “A a yaushe Yusuf din yaje kano?”
Alhaji Isma’iel yace “toni jiya yazo yake min kuka waishi afada maka sun hakura da aure shida Nihla, saboda akwai wani dan’uwanta dayake rashin lafiya akanta, wai kada ya mutu a dalilin su, toni kuma ban dauki zancen nasa serious ba, tayaya kuna tareda yarinya zakace kunfasa, ban yarda da maganar tasaba, shiyasa ma ban yiwa mai hakuri maganar ba “
Alhaji Baqir yayi Murmushinsu na manya yace” wallahi shine, ai mungaisa dashi jiya, Yusuf kenan, Yusufa yaron kirki “????
Alhaji Basiru yayi gyaran murya yace” ai jikin nasama da sauqi, har yanzu de bai farfadoba,”
Baba ya Jinjina kansa yace ” inafa lafiya kana cewa yaro har yanzu bai farfado ba “????
Alhaji Isma’iel Yace”Allah sarki, Allah yabashi lafiya, to amma ina ganin tunda yara sun fahimci juna harshi Yusuf din yayi jihadi, to ina ganin kawai ayi hakuri gaba daya tunda kowa ya fahimci kowa yanzu, sai adaura musu aurensu kawai, idan Allah yabashi lafiya duk wata bidi’ah da za’ayi suyi daga baya “
Farin ciki yakama Daddy, da kansa yasauko daga kan kujerar dasuke kai yafara yiwa Alhaji Isma’iel godia, Alhaji Isma’iel yace