DANGI DAYA HAUSA NOVEL

” Babu komai ai matar mutum kabarinsa “
Alhaji Baqir yace” toni ina ganin, tunda abin yazo da haka, memakon Muje musake dawowa, kawai asiyo goro yanzu adaura, shikkenan anhuta “
Alhaji Isma’iel yace” A a akwai goro, Muje masallaci anemi liman yadaura musu auren, ni Zan zama waliyin Nihla “
Baba yakasa magana ganin irin karamcin da Alhaji Isma’iel yayi masa, haqiqa samun irinsu a yanzu sai antona
Gaba dayansu kuwa suka futo, kai tsaye masallacin unguwar sukaje aka kira liman, da maqocin Alhaji Isma’iel Wato baban Nadiya, Alhaji Baqir yaje banki da kansa yaciro kudi, yace shine zaiyi wa Abba waliyi, nan take kuwa aka daura musu aure akan sadaki nera dubu dari, aka danqawa baban ta sadakin, kowa aka bashi goro, suka yiwa limamin ihsani, sannan suka futo kowa zuciyarsa fes
Daga nan su Daddy sukayi wa su Alhaji Isma’iel godia, suka nufi Airport
Mamy da taji labarin abinda yafaru ta tausayawa Abba, saide wani bangaren na zuciyarta yana jimamin rabuwarta da Nihla, taso ace danta Yusuf yasameta, amma yaya za’ayi, matar mutum kabarinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zuwan su kenan asbitin itada Dida da Ilham, Diyana bata zoba tana fama da cikin ta, Ilham sai fada take mata “kintashi kinsaka wa kanki damuwa ina dalili? Tunda shine yace zaiyi hakuri yaya zakiyi dashi, amma Tun jiya kidinga kuka,Yaya zakiyi da qaddarar da Allah yadora miki, kokuma zuwa zakiyi wajan Yusuf din kijashi ta qarfi, kuma Momy tayi miki Tambayar duniya kinqi bata amsa, yanzu idan taji saboda Yusuf yace yafasa aurenne saboda danta ya warke kike kuka ai ba zataji dadi ba, menene amfanin rashin mantuwa da ruqo Nihla “
Itama Dida tace”wallahi de kam, idan ma kina tunawa da lokacin da yace baya son ki ne agaban family ai yakamata ace zuwa yanzu kisan cewa saboda ke dinne ya kwanta jinya, idan mutane kowa da kowa yaji ya Abba yace baya sonki to yanzu kowa ya shaida ya Abba yadawo yana sonki, kuma gashi Akwance baisan wake kansa ba saboda ke, duk cikin mu waye yasamu irin wannan soyaiyar? Yakamata ki godewa Allah Nihla “
Nihla tayi shiru tana jin maganganun yan’uwanta, ahaka suka qaraso cikin asbitin da hannunsu dauke da abinci, kasancewar ba’a barin kowa yashiga dakin dayake shiyasa suka nemi waje suka zauna, sai Momy ce kawai acikin dakin nasa
Daddy ne yashigo asbitin fuskarsa dauke da farin-ciki Kamar ba dansa ne baida lafiya ba
Su Ilham suka gaida shi, sannan Nihla takira wayar Momy tafuto daga cikin dakin
Gaisawa sukai dasu Ilham suka qara yimata, yamai jiki sannan suka bata Abincin, Momy taji dadi sosai tayi musu godia sannan sukai mata sallama suka tafi, sukabar Nihla awajan
Tazauna tana duba wayar hannunta, Momy dake gefe itada Daddy tace “Alhaji yanaga kanata Fara’ah ne? Allah yasa lafiya”
Murmushi yayi yace “daga Abuja muke”
“Abuja kuma Alhaji, meyake faruwa”
Hannu yasa a aljihunsa yadauko goro yace “riqe wannan goron”
Momy ta karba tace “na menene Alhaji?”
Yace “goron daurin auren Takwarana ne shida yarki”
Momy ta zaro ido tare saka hannu abaki cikin mamaki, takai Kallanta wajan Nihla taga hankalinta yanakan waya
Tace “Alhaji da gaske kake?”
“da gaske nake, ga shaida nan kingani, shikkenan Abba sai hankali ya kwanta”
Momy tasaki ajiyar zuciya tace “Alhamdulillah… Allah nagode ma, to Alhaji binka zanyi mutafi gida nayi wanka nahuta nima, tunda ga matar sa nan ita saita zauna ta dora daga ina na tsaya”
Daddy yayi Murmushi yace “to zo mutafi”
Abincin hannunta takai wa Nihla tace “Nihla riqe wannan Abincin, idan Allah yasa yau yafarka shikkenan sai kuci, akwai kayan Tea aciki, idan kuma bai farkaba sai kici, ni natafi gida sai munyi waya”
Mamaki yakama Nihla, tace “Momy gida kuma? Ba anan zaki kwana ba?”
Momy tace “a a, aina dena wannan zaman Nihla, yanzu kam saike” ????
Jikinta yayi wani iri, tayaya Momy zatace tazauna da ya Abba bayan tasan hakan bai kamata ba? Tace “to Momy kuma….”
Cikin sauri Momy ta katseta, “Nihla bafa Zan zauna ba, yau kema ki d’ana”
Tadubi Daddy tace “Alhaji Muje”
Har sun fara tafiya Tajuyo tace “yawwa Nihla Karki Manta likita yace kullum dasafe ana goge masa jikinsa da ruwa Mai Dan dumi, duk abinda kike buqata yana cikin dakin, idan baki ganiba saiki kirani”
Nihla ta kalli Momy takasa cewa komai, wai me Momy take nufi ne, ya za’ayi takama taba jikinsa bare har dasu goge jiki? ????
Momy kuwa bata jira amsar taba, suka tafi itada Daddy
Kuyi hakuri da wannan ba yawa
Sharhi please ????
Amnah El Yaqoub ✍????
[7/14, 2:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
53&54
Jiki a sanyaye tajuya cikin dakin, ahankali ta tura kofar dakin tashiga, idonta yasauka akansa, babu oxygen din ancire masa, amma fuskarsa tayi wani irin fari, Dan qaramin lips dinsa ta kalla duk yafara bushewa, gashin idonsa sun kwanta gwanin sha’awa
Kujerar dake gefen kansa tazauna ta ajiye Abincin, sannan tayi shiru tana tunanin irin wannan zaman jinya, ko yaushe zai farka? ????
Ya Yusuf ne yafado mata, Allah sarki, tunda sukai maganar rabuwa dashi basu sake waya ba, tana mamakin yanda lokaci daya yace zai sadaukar da soyaiyar ta ga ya Abba, bayan tasan ya Abba da kishi idan shine ba lalle ya’iya hakura da itaba
Haka tazauna shiru ita kadai a dakin, lalle idan hakane Momy tayi kokari, amma tarasa Inda Momy tasa gaba, tayaya zasu barta daki daya da ya Abba?
Ajiyar zuciya tayi tajuya ta kalleshi, saikuma ta dauke kanta cikin sauri Kamar tana tsoro karya kamata
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Mutanan gida kam, kowa labari ya sameshi, saboda su Alhaji Baqir kowa daya koma gida yafadawa iyalansa, Aslam Kamar yayi me saboda murna, Ilham kuwa bakinta Yaqi rufuwa, haka tadinga d’aga lil Abba sama tanayi masa wasa Yaron kuwa sai dariya yake shima Kamar yasan abinda ake
Aslam Yazauna yanemi number Yusuf domin su tattauna kuma yaqara yimasa godia amma kiran duniya ya Yusuf bai dagaba, haka ya hakura, ya shirya da daddare domin suje asbitin shida Ilham, Ilham tazuba musu abinci, sannan tahada wa Nihla wani maganin mata, tatafi mata dashi, cikin ranta tana cewa gara tafara bawa qawar tata Dan abubuwan nan tanasha, tunda auren yazo a qurarran lokaci, kuma tasan halin Nihla yanda batason ya Abba yanzu tsaf zataqi sha, Dan haka gara tana zuwa dashi tana bata tanasha a gabanta
Zuwan su asibitin kenan suka kira wayarta tafuto, fuskarta Babu yabo Babu fallasa, ya Aslam sai Fara’ah yake yace “Amarya kinsha qamshi”
Nihla bata kawo komai ba, tunda kowa yasan ansa mata rana Dan haka tace “na’am ya Aslam”
Yace “yaya marar lafiyar naki kuma”
“ya Aslam namu de”
Yayi Murmushi yace “A a, mun barmiki, keda dan’uwanki, kinga ai yanzu yazama naki”
“duk da haka de ya Aslam, kaima ai dan’uwanka ne”
Ilham ce tajata gefe tace “ke rabu dashi, zomu zauna”
Tabashi Abincin tace “ga Abincin nasu, ka shiga musu dashi ciki tunda zakaga jikin nasa”
Abincin ya karba yawuce cikin dakin
Yau Tun safe ransa fari tas, Baqin cikin sa daya yanda Abba yake kwance bai farkaba, yaso ace shine mutum na farko dazai fara bawa Abba labarin aurensa da Nihla , amma yaya zaiyi? Wayarsa yafara dubawa yaga batanan, da alamun agida akabar masa wayoyin, yar drower din gefen gadon yafara dubawa cikin sa’ah yaga biro da wani littafi, cikin sauri yayagi qaramar paper yayi rubutu aciki, sannan ya linke takardar yaqaraso gaban gadon na Abba yana dube duben Inda zai saka takardar ko Allah zaisa Abba yagani batare da Nihla ta lura ba, hannunsa ya kalla, yadaga hannun yasaka masa takardar aqasa hannunsa, yasan ma Nihla zata gani, amma duk da hakade yana fatan karta gani din