DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Awaje kuwa Ilham ta dubi Nihla tace “amarya, amarya, ah ah, kaga amarya kinsha qamshi”????
Tsaki taja tace “keni ba wannan ne yake damuna ba, Ilham yanzu Dan Allah tayaya Momy zata tafi gida ta barni tareda ya Abba, bayan tasan surutun wannan family din yanzu sai kiji ankasamu a faranti ana qananun maganganu akan mu”
Ilham tace “Babu wani maganar da za’ayi, to waye ma ya’isa yace muku wani abu?” ????
“Ilham bazaki ganeba, bafa muharrami na bane sannan wai Momy harda cewa wai….” shiru tayi takasa qarasa wa
Ilham tayi Murmushi tace “kinga, ki kwantar da hankalin ki Nihla, babu abinda zai faru, tome zai miki shida bashida lafiya? Kisaki jikinki kiware ki kula da dan’uwanki, karkiji komai tunda su Momy sunsan kina tare dashi, kifa saki jikinki dashi” ????
Cikin sanyin jiki tace “to Ilham, amma de..”
Ilham tace “kinga, karbi wannan hadin kisha, kinga yanzu bawani zaman gida zakiyi ba bare Momy tadinga baki kina sha, kuma mazan yanzu saida gyara, ke masu gyaran ma yaya aka qare dasu, Dan haka gara kije gidan mijinki tsaf”
Babu musu takarba tace “to Ilham nagode”
Dariya sai cin Ilham take, Nihla kuwa bata kulaba
Fira sukaci gaba dayi har ya Aslam yafuto sannan sukai mata sallama suka tafi, ita kuma tajuya cikin dakin
Wajan shadaya na dare likita yazo ya dubashi yace “idan akwai matsala zaki iya kiranmu”
Tace “to”
Likitan nafita tadauki wayarta tafara kiran ya Yusuf amma baya dauka, Tun tana yin na marmari harta gaji da tadena, sai message ta tura masa
Tashi tayi tadauro alwala tazo ta shimfida sallaya tatada sallah, data idarma addu’ah kawai tayi tayi sannan tatashi ta linke sallayar takoma kan kujera tazauna, zuba masa ido tayi, gaskiya ya Abba qarshe ne, yahadu iya haduwa, halin sa ne bai haduba, ajiyar zuciya tasaki ta kalli girarsa datake kama da tata girar, Allah de yabashi lafiya tadena wannan zaman shirun
Tun tana kallansa tana tunani harta gaji tadan dora kanta agefen gadon nan take bacci ya kwasheta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
“Rahma sai murna kike Tun safe”
Momy ta kalli Daddy tace “Alhaji ai dole nayi farin ciki, yau Abba na yasamu abinda yakeso, koda na mutu nasan yarana dukansu sun samu mata nagari”
Jinjina kansa yayi yace “hakane, Allah yabasu zaman lafiya”
“Amin Alhaji, ni dama nasan Dan bakasa baki bane, amma inde an fahimci juna ai komai Mai sauqi ne”
“hakane, yabata min raine yaron, haba yaro sai taurin kai”
“Hmm Alhaji kenan, kowa yasan de halin Abba gaba daya naka yadauko, kuma kaga laifin yaro?, amma Alhaji yanzu ai sai afara gyara musu gidansu, idan komai ya kammala saisu koma can”
Daddy yace “Haba Rahma, korar yaran nawa kuma kike? me zaisa sukoma wani waje Rahma? Da badamu suke zaune ba? Yanzu ma ai sai suyi zaman su”
Cikin sauri Momy tace “um um Alhaji, kayi hakuri da wannan maganar, ba zaman gidan kake bane shiyasa, amma nida nake zaune dasu nasan abinda yake faruwa, Abba bashida kunya gara su tafi kawai”
Murmushi Daddy yayi yace “to bansan de mekika ganiba, amma tunda kince haka, idan angama gyare gyaren komai saisu koma ai”
Tace “yawwa yanzu naji batu”
Asuba tagari Daddyn Momy ????????
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Karfe hudu da rabi na dare yaji kansa yasara, Ahankali Ahankali yafara bude idonsa
Hasken dayagani adakinne yasa yasake runtse idonsa sannan yasake budesu Ahankali, Nihla kuwa bacci yayi bacci kanta yanakan dantsan hannunsa tayi fillo dashi
Kallan kansa yayi anan ya tabbatar da asbiti aka kawoshi, ahankali yafara tariyo abinda yafaru dashi harya tuna komai, yana gama tunowa yaji wani irin Baqin ciki aransa
ga kansa dayake masa ciwo,qirjinsa nauyi idan yanajan numfashi, jin alamun mutum akan hannunsa dakuma gashinta daya bazu akan hannun nasa shiyasa yakai dubansa ga hannun damansa anan yayi tozali da dogon gashin kanta, babu dankwalin yazame yafadi qasa
Gabansa yafadi,meyakawota nan?
Ahankali yafara motsawa zai tashi yaji hannunsa na hagu akan takarda, komawa yayi ya kwanta sannan yadauki takardar Ahankali baiyi tunanin komai ba yabude, mamaki ya kamashi, wannan ai rubutun Aslam ne
Ahankali yafara karantawa :
Ango mijin amarya, congratulation Abokina, Allah yasa kada wani yarigani sanar dakai cewa Nihla tazama mallakinka , but ka kiyaye batasan komai ba “
Cikin sauri yatashi zaune Kamar ba marar lafiya ba, sai yaji yana nema yanemi ciwon kan nasa yarasa, ita kuwa Nihla jin kanta ya koma kan katifa yasa ta danyi motsi, sannan tasake gyara kwanciyar ta tajuya taci gaba da bacci
Dube dube yafara yana neman wayarsa amma bai gantaba, wasiqar yasake karantawa, ya karanta ta yakai sau biyar
Yajuya yasake Kallanta tana bacci hankalinta kwance, Hawaye ne suka zubo masa, yasaka hannunsa duka biyun ya share, sannan yadaga hannunsa sama yana yiwa Allah godia, domin kuwa yasan cewa banda addu’ah Babu abinda zaisa yasamu Nihla cikin sauqi
Alerm din wayarta ne yafara qara, Ahankali ya koma ya kwanta Yarufe idonsa Kamar me bacci, nan take masallatai suka dauki kiran sallah
Saida Alerm din yaqare yasake bugawa sannan tabude idonta, bacci takeji sosai
Kallan kanta tayi Babu dankwali tace “subhanallah,” tadauko shi aqasa ta daura dankwalin ta sannan ta kalleshi, tasaka hannu ta gyara masa fillo din da kansa yake kai sannan tashige toilet, yana jin alamun shigar ta toilet yabude idonsa yatashi zaune yana daga hannu yana ta murna ????
Haka yaita murna saida yaji zata futo sannan ya koma ya kwanta, harta idar da sallah duk yana jinta, wayarta tafara qara, tadauka yaji tace “Hello Momy”
“Nihla kuna lafiya deko?”
“lafiya kalau Momy, yanzu na idar da sallah ma”
“toya jikin nasa”
“gashinan nan de Momy, har yanzu shiru”
“to Allah yasawaqe, Karki Manta da goge masa jikinsa de anjima, akwai Ruwan zafi a flask, anjima za’a kawo muku abinci”
“to Momy sai anjima”
Tayi shiru tana azkar, har gari yafara haske, ganin idonsa biyu kuma ga lokacin sallah yana wucewa shiyasa yafara bude idonsa Ahankali, ya kalleta da gefen ido yaga tayi tagumi tanajan carbi
Ahankali yafara cewa “Momy!, Momy!! Momy kaina”
Cikin sauri ta zabura tayi kansa “ya Abba! Katashi? Sannu, bari akira Doc.”
Tajuya tafice daga dakin cikin sauri
Wani irin murmushi yasaki, yana jin wani masifar dadi aransa yabi bayanta da kallo, wai yau shine Nihla take nuna masa wannan kulawar, aikuwa in hakane Babu shi Babu warkewa????
Tare suka dawo da likitan, ya dubashi, yasake kallansa yace “abin mamaki, ya akai ciwon naka yaragu haka sosai?”
Maida kansa yayi majinyacin sosai, ya langabe yace “qirjina yana min ciwo kadan, kuma ko’ina ma ciwo yake min na jikina”
Doc. Yayi Murmushi yace “insha Allah Ahankali zaka dena ji”
ya kalli Nihla yace “please ki goge masa jikinsa idan zai iya saiyayi sallah ma, idan ma zai iya wanka saiyayi ko zaiji qarfin jikinsa”
Jikinta a sanyaye tadaga masa kai, yafice daga dakin yarage saisu biyu
Kallansa tayi, cikin sauri takawar da kanta tafara linke sallayar datake kai
Shikuwa sai binta yake da wani irin kallon soyaiya , badan kada ya to nawa kansa Asiri ba da Babu abinda zai hana tajita ajikinsa
Toilet tashiga tahada masa ruwa, sannan tafuto tazo wajansa tana kallansa qasa qasa tace “Anhada Ruwan wankan ko zaka shiga kayi?”
“Ai bazan iyaba, saide nagoge jikina”
Cikin sauri tace “to” sannan tahada Ruwan zafin agabansa, tadauko qaramin towel takai masa gabansa ta ajiye tace “gashinan ankawo”