DANGI DAYA HAUSA NOVEL
Kallanta yayi har yana lumshe idonsa alamun jin jiki yace “bazan… Iyaba fa”
Shiru tayi, tarasa meyake mata dadi, shikuma yana Kallanta yanaso yaga yaya zatayi
Ajiyar zuciya tasaki ta qarasa wajansa ta matsar da Ruwan gefe, ta kalli rigar jikinsa tace “to dan gyara”
Sarai yagane nufin ta sai yace “jikina ne Babu qarfi, bazan iyaba”
Wannan karon kam kawarda kanta tayi gefe, itade wannan zama baiyi mata ba kokadan, sai hura hanci take, takasa yin komai ????
Kamar wadda aka tsikara Tajuyo takama rigar jikinsa Ahankali tafara yin sama da ita, babu musu yadaga mata hannunsa ta cire masa rigar duka, gabanta yafadi ganin yanda hannunsa yake a murde, ga gashi daya kwanta akan qirjin nasa,lokaci d’aya yacika idonta yayi mata masifar kwarjini, fat… fat… fat… takejin bugun zuciyarta nayi, ta ajiye rigar sannan tadauko towel din dake cikin Ruwan ta matse, tadora shi akan qirjinsa
Zirrr yaji wani irin abu acikin jikinsa, cikin sauri ya lumshe idonsa yanajan wani irin numfashi
Satar kallansa tayi taga idonsa arufe, dan haka tafara goge masa cikin sauri, shikuma wani irin dadi yakeji Kamar karta daina abinda takeyi, bayaso yadena jin abinda yakeji din
Ita kuwa sai kawarda kanta takeyi, har wajan wuyansa saida ta goge masa, sannan ta ajiye tace “nagama”
Ahankali yabude idonsa yasauke su akanta, meyasa Nihla ta kasance damuwar sa dakuma maganin damuwar tasa? Meyasa yakejinsa Kamar ba marar lafiya ba? Tabbas dole ne yayi azumi domin nuna godiyar sa ga Allah
Gari kam har yayi haske sosai, ahankali yafara kokarin tashi yadubeta tareda miqa mata hannu cikin shagwaba yace “kikamani natashi”
Kallansa tayi, tadauke kanta, inaga yamanta itace atare dashi ba Momy ba shiyasa yake mata wannan shagwabar
Ahankali ta dora hannunta cikin nasa, yanajin haka yariqe ta sosai, saboda yanda yaji hannun nata da taushi, yatashi tsaye yadora kansa akan kafadarta, yasaka dayan hannun yariqe waist dinta
Yanayin yadda ya tura saqon nasa kuwa ya karbu, nan take tayi taga zatayi baya, amma saiya sake riqe waist dinnata sosai, cikin shagwaba yace “Uhm… Uhmm…. Nifa bazan iyayin wankan ba”
????Zaro idonta tayi, sannan tazare jikinta Ahankali, ta kalleshi tace “tome kake nufi? Ban fahimta ba?”
Saura kadan tasaka shi dariya, amma saiyayi Dan murmushi yakawar da fuskar sa, yadafa bangon dakin harya shige cikin toilet din Ahankali
Wata irin nannauyar ajiyar zuciya tasauke sannan takoma kan gadon ta zauna tareda dafe kanta????????♀️
Inda yariqe mata dinnan wani iri takeji
“Zoki gani”
Ta tsinci muryar ya Abba yana kiranta
Dak.. Dak.. Gabanta yafara faduwa, Innalillahi…. mekuma zataje tagani? ????
Abba dake toilet yaji shiru, yasaki yar qaramar dariya yasake cewa “Kizo kigani”
Nihla kuwa mayafin ta tayafa, tana jiran likita yashigo tagudu gida, sarai tana jinsa tayi shiru, da yasan zai iyayin wankan amma shine zaisata wahalar goge jiki
Masu cewa naqara yawan typing suma su qara yawan Comments, dama nafada more Comments more typing ????????
Amnah El Yaqoub ✍????
[7/15, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
55&56
Jin bata amsa masa ba yasa yayi Murmushi yafara wankan sa, yasan cewa sarai tana jinsa
Bai dauki lokaci Mai tsawo ba yafuto, yana sanye da kayan jikinsa, Nihla tana jinsa yafuto amma bata daga kai ta kalleshi ba, idonta aqasa, ya kalleta yayi Murmushi yasaka hannu yadauki sallaya sannan Yazauna abakin gadon yayi qasa da muryar sa Kamar Wanda yake rada yace “please yaushe mukazo asbiti?”
Yatsun hannun ta take wasa dasu batare data dago ta kalleshi ba tace “Shekaran jiya”
“kwana biyu kenan?” yasake yimata Tambayar
Kanta tadaga masa alamun hakane
Kansa ya Jinjina alamun gamsuwa sannan yatashi yatada kabbarar sallah
Yasha addu’ah sosai acikin sallar tasa, yana qara yiwa Allah godia, bayan ya idar ya ajiye abin sallar sannan yafara kokarin hawa gadon
Cikin sauri tatashi takoma kujera tazauna, Sam taqi yarda suhada ido dashi
Shikuma kwanciyar ta isheshi, haka Yazauna yasata agaba yana Kallanta, tanaji a jikinta ana Kallanta Dan haka koda wasa taqi yarda suhada ido dashi
Wayarta tadauka takira Momy, Momy na dagawa cikin shagwaba tace “Momy yaushe zakizo”
Momy tace “Nihla me zaisa nazo asbiti bayan gaki nan? Menene yake faruwa?”
“Momy Babu komai”
“A a ki sanar Dani idan akwai abinda yake faruwa”
“Babu komai Momy, dama ya farka ne”
Momy tace “to Alhamdulillah, Allah mungode ma, yana ina Abban?”
Satar kallan Abba tayi daya zubawa lips dinta ido yana kallo tace “gashinan”
“to bashi wayar”
Ahankali ta miqa masa wayar, memakon ya karbi wayar kadai sai da yahada da hannunta yariqe sannan yazare wayar yayi qasa da murya yace “Momy….”
“Abba na ashe jiki yayi sauqi, to Alhamdulillah bari mu shirya muzo”
“A a Momy, kiyi zaman ki, banajin ciwon sosai, sonake ma yasallame mu”
“to shikkenan idan kana buqatar wani abu de karka yi shiru ga Nihla nan”
Murmushi yayi yace “to Momy”
Wayar ya ajiye gefensa, a lokacin likitan dayake aiki da safe yadawo yadubashi,shima yayi mamakin yanda Abban ya warke
Abba yace “Doc. Ai ina ganin ma dazaka temaka daka sallamemu, saboda banajin komai yanzu, inajin karfi ajikina banajin ciwon komai”
Likitan yace “ka tabbatar?”
“da gaske nake Doc.”
Yace “to shikkenan, zaku iya hada kayan ku, zanje nadawo yanzu”
Yana ganin Fitar likitan ya kalleta yace “madam kira min Abokina mana”
Kallansa tayi, taga wayar tana gefensa, tace “gata nan awajan ka”
“eh nasani, kinsan wayar yanmata, saisu”
Ahankali tamiqo hannunta zata dauki wayar yabi hannunta da kallo gwanin sha’awa dogaye dasu
Tadauki wayar tadannawa ya Aslam kira
Ringing din farko kuwa yadauka, batayi magana ba tabashi wayar
Cikin aji yace “Abokina”
Cikin murna Aslam yace “kaga Ango, Ango kasha qamshi, kace kanajin qamshin amaryar taka kamiqe”
Murmushi yayi kawai yace “naga saqon ka ai”
“Hmm ai addu’ah nayi tayi kada Nihla tagani, amma yanzu de jikin da sauqi ko”
“babu komai, na warke”
Aslam yasaka dariya yace “toganinan zuwa”
Daga nan sukai sallama, doc. Yazo yabasu takardar sallama, sannan Nihla tafara hada musu kayansu, ko minti goma ba’aiba Aslam yazo, suka tafi, sun shiga cikin Mota su agaba ita kadai abaya, wayarta tafara qara, tana dubawa taga baban tane, cikin ladabi tadauka “Baba ina kwana”
“lafiya Nihlan Diddi, Yaya su hajiya”
“suna nan kalau baba, inasu mamy”
“mamy tana nan lafiya, bakya wani abune yanzu ko”
“eh baba”
Gyaran murya yayi yace “to abinda nakeso dake shine ki saurari abinda Zan fada miki,jiya su Alhaji Abubakar sunzo andaura miki aure da Dansa Abubakar”
Gabanta yafadi, cikin sauri tadafa qirjinta tace “Aure kuma baba”
Abba da Aslam dake gaban Mota suna jinta, Aslam aransa yace to fada mata ake kenan
Abba kuwa shiru yayi yana jinta
Daga daya bangaren baba yace “eh aure, Yusuf da kansa shiya fara yiwa mahaifin sa magana akan ya hakura, saide bai yarda ba, saida sukazo jiya muka sake tabbatar wa, ga sadakinki ahannu na dubu dari cif,kiyiwa mijinki biyaiya sannan kiyiwa Yusufa addu’ah Allah yabashi mace tagari, mahaifin sane ya tsaya akai komai aka gama, sannan Alhaji Abubakar yanemi yafiyata da kansa, Dan haka banason wani tone tone, kiyi hakuri Allah yabaku zaman lafiya “