DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Ta kalli fuskarta yace “kinji”

Gaba daya yafara kashe mata jiki da salonsa,
Cikin shagwaba tace “ya Abba nide kabari”

Yace “to kin yafemin?”

Ahankali tadaga masa kanta, sannan tace “Allah yayafe mana baki daya”

Yayi Murmushi yace “Amin, kinga wani abu”
Yabude wayarsa ya nuna mata wasu pictures
Kanta ta matso tafara ganin pictures din, shima yaturo nasa kan domin su gani tare,tana gani tace “laaaa pictures dina”

Murmushi yayi ya kalleta, yanda kansu yahadu ne yasa yaji Kamar yayi kissing Dan qaramin bakinta, musanman yanda ta bude shi dinnan tace laaaa, amma bazai yiba, gara yabi komai Ahankali

Yace “yes, Tun lokacin da mukaje garinku nayi miki pictures din, kin tuna? Abakin ruwa, har ruwa yadakemu”

Cikin murmushi tace “wallahi na tuna, bani na gansu gaba daya, waye yatura ma?”

Dadi yafara kama Abba, yanda yaga tafara sakewa dashi, yace “ya Usman ne yatura min”

Tace “wayyo,lokacin banda qiba wallahi”

Kallan qasa qasa yayiwa cikakkun nashanunta yace “yanzu ai kinyi” ????

Nihla bata gane komaiba tace “wallahi sune, zaka tura min kuwa”

Kallanta yake yanda take jin dadi sai yaji dadi shima, gashi shiba wani surutu ba, kuma bayaso firar taqare,bayaso yadena jin daddadan qamshin dake tashi a jikinta, bayaso yayi nesa da’ita, yarasa mezaice mata domin tasake jin dadi shikuma yaga farin ciki akan fuskarta, ya kalleta yace “nagoyaki?”

Cikin sauri ta kalleshi, cikeda mamaki, wanne irin goyo kuma ana zaune lafiya? Saikace Wanda zai iya goyon, tasan kawai fada yayi, amma domin taga gudun ruwansa sai tace “eh”

Cikin sauri yace “to zo ki hau”

Yadauke hannunsa akan cinyar ta ya tsugunna a gabanta

Mamaki yagama kashe Nihla, anya ya Abba ne kuwa wannan? Yau ya Abba ne zaice tahau bayansa ya goyata? Ta ajiye wayar tasa agefe sannan tafara tattare rigar jikinta, tad’ane bayansa, lokaci daya yamiqe tsaye, beji nauyin taba kokadan, hanyar kofar dakin yanufa da ita yace “muje nakaiki falo saina dawo dake?”

Zaro ido tayi tafara girgiza kanta tace “laaaa a a babu ruwana”

Ganin yanda ta tsorata yasa yayi Murmushi yace “Allah Muje”

Riqeshi tayi sosai tace “dan Allah kar Muje”

Lumshe idonsa yayi, numfashin sa yafara sauyawa, qarfin jikinsa yafara raguwa, kasala ta lullube shi sakamakon jin nashanunta agadon bayansa yanda tasa hannu ta rirriqeshi

Nihla taji shiru, tayi tunanin bai haqura ba, tasake jijjigashi tace “dan Allah”

Nan take yaqara daukan caji, yashiga cikin yanayi, yaji qafafunsa suna neman gaza daukarsu, sai gyara kafafunsa yake, ita kuma takasa gane komai

Yana motsawa kuwa suka tafi kan gadon nata gaba dayansu suka fada kai

Nihla tayi tunanin da niyya yayi hakan, batasan yanayi ne yasa ba ????
Nan take tafara dariya, yajuyo da kansa yana Kallanta, yajima rabon daya ga tana dariya Kamar haka, ahankali yadago hannunsa ya dora shi akan dimple dinta

Sharhi, share please ????

Amnah El Yaqoub ✍????
[7/15, 11:04 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

57&58

Juyowa tayi tana kallansa, cikin murmushi tace “Aidama nasan bazaka iya daukana ba, shiyasa nahau banyi ma musu ba, yanda nake d’innan”
Ta qarasa maganar tana jijjiga jikinta

Shima murmushin yayi mata “nayi tunanin zan’iya ne, bansan haka ake jiba”

Nihla kwata kwata bata gane maganar dayayi ba, Dan haka tayi shiru, hannunsa dake kan dimple dinta yadauke yadawo dashi dede karan hancin ta, yace “kinada kyau”

Cikin sauri ta kalleshi, tayi Murmushi sannan ta yunqura tatashi zaune, ta kalli Agogon dakin tace “kaiiii shadaya saura, ya’akai lokacin yayi gudu haka, bari de in shiga wanka”

“to kitashi kishiga mana”

“to ai baka fita ba”

“idan kika shiga Zan fita, kona kaiki?”

Cikin sauri tace “a a, tsaf zaka sake kayar dani” tashige toilet din da kayan ta a jikinta tareda rufo kofar

Yana ganin shigarta ya lumshe idonsa tareda yin ajiyar zuciya, yatashi jiki a mace yafuto daga dakin nata, har lokacin Momy bata falon, ya kashe kayan kallo sannan yawuce dakinsa, cikeda begen matarsa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Acikin satin su Abba sukaje Abuja suka yiwa Yusuf godia, Abba har kunyar sa yakeji akan abubuwan dasuka faru abaya Sosai suka fahimci juna

Tundaga lokacin Nihla tadena zuwa wajan gyaran jiki, dede da falo Momy hanata futowa tayi saide dole, kullum tana cikin hijabi, hatta qafarta akwai safa, data zauna aqasa kuwa Momy zata sata tatashi takoma kan gado ko kujera duk saboda kada sanyi ya shige ta
Magunguna kuwa Momy bata take iri-iri masu inganci, Nihla qwarai ta yaba irin sonda Momy take wa ya Abba, haka kuma duk cikin surukanta Nihla ta daban ce, dama Tun tana qarama soyaiyar Nihla take cikin Zuciyarta, kokadan Momy bata qyashin yiwa Nihla abubuwa, domin kuwa tayi alqawarin zata riqeta Kamar itace ta haifeta, shiyasa take mata duk wani abu da uwa zata yiwa ‘yarta

Abba da Aslam Babu zama, danma wani lokacin su Adam da Fawaz suna yin wani abun ta wani bangaren, gida kam komai yaji, sun qawata shi yanda yakamata da kayan kamfanin A&A Furnitures, yayinda Anty Salama matar ya Usman da hajiya Farida maman su Dida suka shirya sukaje Dubai suka hadowa amarya kayan lefenta

Anty Firdaus kuwa matar ya Aliyu itace tashiga tafita wajan kawo anko, dayake abune na kudi nan take kowa yayi, duk Wanda kaduba yana cikin farin ciki, kuma doki yake wannan rana tazo, andade ba’ayi wani taro a wannan family ba, ko bikinsu Aslam da akayi Babu wani biki da akayi, kasancewar kowa yasan Babu Wanda yake son auren, kowa dole aka masa

Ana sauran kwana biyu biki ‘yan’uwa na nesa dana kusa duk sunzo, yan’uwan mahaifin ta duk sunzo, kuma family anhadu anyi musu kara duk Inda suka so anan suke kwana, yan Abuja ma duk sunzo, mamy kam wajan Momy ta sauka suka hadu suke gudanar da Komai

Yusuf yana wajan angwaye, saide duk abinda yake yana kokarin danne zuciyarsa ne kawai, saboda kada yazobe ladansa, bayan badan komai yayi ba saidon Allah

Ranar kamu kuwa kowa ya shirya, amarya tanata sauya shiga kala kala, Acan gidan sheik Adam kuwa Diyana kuka tasaka masa da qaton cikin ta na wata shida, gaba daya dinku nan sunyi mata kadan, haka tasa Adam agaba tana masa kuka, yarasa yaya zaiyi da’ita haka yadauko mata wasu kayan suka Taho gidan bikin, Dida kuwa normal take harkar ta, domin kuwa har yanzu batada komai ????

Washe gari da rana amare suna zaune a part dinsu Ilham, cikin tsohon dakin Ilham datake ciki kafin tayi aure, bayan angama yiwa amarya kwalliya, zuwa dare za’a tafi wajan dinner

Diyana tana gefe, da ciki agaba tana karanta wani littafi, Nihla ta kalleta tace “meciki”

Diyana tace “saura ke ai”

“A a, aini ya Abba yana sona, saiya qara reno na, sannan”

Gaba dayansu suka saki dariya, Dida tace “tab, ina Ruwan yaudaran kai”

Dariyar dasuka sa ne yasa lil Abba kuka, Nihla tace “kai Innalillahi… Dan Allah Ilham ki dauke wannan yaron naki, gaba daya ya ishemu da kuka”

Ilham tace “angonki nede, yanda kuka sashi kuka yasin kema lokaci yana zuwa saiya saki kuka” ????

“ni Ilham Dan Allah kidena min irin wannan maganar, Allah banaso”

Wayarta ce tadauki qara, Dida tabata tace “ga Ango yana kira”

Karbar wayar tayi, ashe yanada number ta, betaba kirantaba, rage murya tayi tace “Hello”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button