DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

WhatsApp readers, ina qara godia sosai yanda kuka bani hadin kai, kuka bani lokacin ku wajan karatu da kuma sharhi, ana mugun tare????

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/15, 2:27 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI ‘DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook

https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

7&8

Zaune suke acikin Babban falonsa dayake tarbar baqi, Babban falo ne daya hada komai da Komai najin dadin rayuwa, tsaki yasaki yakalli Agogon hannunsa fuskarsa Babu alamun wasa yace “me Basiru yakeyi ne har yanzu baizoba, bayan Tun jiya nasanar dashi da kaina cewa akwai meeting karfe tara nasafe”

Kafin sauran biyun su bashi amsa aka turo kofar falon aka shigo, kana ganinsa kaga cikakken magidanci, fuskarsa adaure yadubeshi “mekake yi bakazo a lokacin dana sanar dakai ba?”

Yace “yaya Abubakar ai lokacin yayi, gani kuma nazo akan lokaci” ????

Kai tsaye yace dashi “duba agogo karfe nawa?”

Kallan Agogon dakin yayi “goma da rabi”

Fuskarsa adaure yace “kuma karfe nawa nace kazo?”

“karfe tara kace, aini to inajin agogo nane yasamu matsala, karfe tara ya nunamin wallahi, inajin matsala yasamu, duba kagani” ya qarasa maganar yana nuna masa hannunsa

Harara ya watsa masa yace “lusari, Wanda mace tagama shanye shi”

Shiru falon yasakeyi, ba qaramin girma suke bawa Babban yayan nasuba, hakan yasa Wanda aka kira da lusari baice komai ba, yanemi waje Yazauna

Gyaran murya yayi yace “munyi magana da hajiya dangane da wani abu Mai girma Wanda ni kaina bansan menene ba,….” nan take ya sanar dasu yanda sukai, sannan yaqara cewa “nasanar daku ne saboda nima korai zaiyi halin sa,”

Hajiya Farida datake zaune, wadda ita kadai ce mace acikinsu tace “Amma yaya Abubakar meyasa ba’a fadawa Aisha ba? Itama fa tanada ‘ya, kuma ‘yarta tana daya daga cikin wannan family, Kamar yanda Iyayenmu suka bada wasiyyar dabamusan kota mecece ba akan yaranmu, ai yakamata ace tasani”

Kallanta yayi fuskarsa adaure “da Aisha da abin data haifa duk suna qarqashin iko nane,”

Jinjina kanta tayi, sannan tasake cewa “to amma yaya ai yakamata ace munjata ajikin mu, Kamar yanda aka fadawa yaya Basiru itama…”

Kafin ta qarasa magana yadaga mata hannu tareda fadin “Farida!!!”

Lokaci d’aya ta nutsu Kamar ba itace take zuba surutu ba, kallansu yayi yace “daga yanzu kuma daga rana irinta yau, doka zata fara,” yana fada musu haka yatashi yafice, yabar kowa da tarin tambayoyi, Alhaji Baqir yatashi yana gyara Babbar rigar jikinsa yace “koma menene bazai wuce maganar rabon gado ba, ni wannan bata gabana,” shima yafice daga falon ????

Hajiya Farida ta kalli Agogon hannun Basiru dayake zaune kusada ita batare daya saniba, taga karfe tara da kwata, ta kalli Agogon dake manne afalon taga goma da arba’in da biyar, tasaki daria tasan sarai aikin matar sa ne wannan, wadda ya Auro musu ita tazame musu baragurbi acikin family, Kallanta yayi “me kikewa dariya?”

Tace “yaya Basiru Babu komai, nina wuce gida sai anjima” ????

Daganan shima yatashi yadoru a bayanta yana darurar sanar da matar sa abinda yaya Abubakar yace

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Labarinsu

Mazawaje family Babban family ne dayake da tarin mutane dayawa, Abubakar shine jigo na wannan family yanada mata biyu Hauwa’u dakuma Fatima

Hajiya fatima itace babba, tanada yara biyu, Babban danta shine Yaci sunan babansa Wato Abubakar, sai qanwarsa Aisha, sun taso sunasan junansu sosai da sasai

Sai Hajiya Hauwa’u, wadda suke kira da hajiya sak, tana da yara uku, Baqir shine Babban danta, sai Basiru da kuma qaramar su Farida

Abubakar yayi aure ya auri daya daga cikin family dinsa na uwa, maisuna Rahma, suna zaune lafiya saide murdaddan halin sa datake hakuri dashi wani lokacin, sunada yara hudu, Usman shine babba, sai Aliyu,Sai farouq, Sannan Abubakar Wanda yaci sunan kakansa suna kiransa da Abba,

Alhaji Baqir kuwa yaransa biyu, Aslam da kuma Adam

Sai Alhaji Basiru, yanada yara uku, Fawaz shine dansa na farko, bayajin magana kokadan, ga kula abokan banza, sai Aisha qanwarsa wadda aka saka mata sunan Diddi, tanada hankali da nutsuwa, sannan ta fannin kamanni suna kamada Nihla sosai Kamar yan gida daya, sai qaramar Ilham, ita kuma ilham rashin kunya, kowa yasan batada kunya yarinyar

Sai hajiya Farida Mai yara biyu Dida, dakuma Diyana

Qa’idar familyn nasu shine tunda suke Babu wani Wanda yake auren bare, saide ka nema a family ka aura, kowa yabi wannan dokar, kwatsam sai Alhaji Basiru yagano wata wadda bata cikin family yace ita yakeso zai aura, adede lokacin itama Aisha Wato Diddi tace tanada saurayi wani bafulatanin yalleman dake jihar jigawa, tace shi takeso, al’amarin yakawo rigima sosai a tsakanin wannan family, har hakan ya haifar musu da rabuwar kai, wasu suna ganin aiba laifi bane hakan tunda ba haramun bane, wasu kuwa suna ganin cewa bedace ba, tunda dokace ta family, cikin su kuwa harda Abubakar, saida aka kai ruwa rana sannan aka rabu dasu sukai auren, da sharadin duk abinda yabiyo baya su sukaja amma kada su nemi kowa
Babu Wanda yakai Abubakar bacin rai akan hakan, ganin idon qanwarsa Yarufe akan soyaiya, hakanne yasa ya tattara ta yawatsar, yadena shiga cikin al’amarin ta, amma cikin qasan ransa yana qaunar qanwarsa, ita kuma matar Basiru hajiya Abida tunda tashigo family din taga basa sonta saita shanye mijin nata da kissa iri iri, idan tasa doka bai isa ya qetare ba, haka kawai kuma Allah yadora mata kaunar Diddi aranta, tana son Aisha sosai, shiyasa tana haifar yarta qanwar fawaz tace Aisha za’a sakawa yarinyar, babu musu mijin nata yayarda????

Aisha Wato Diddi tana zaune lafiya da mijinta Mai Suna Ibrahim, amma ana kiransa da Mai hakuri kasancewar mutum ne shi Mai mugun hakuri, dukda halin rashin dayake dashi bata taba nuna masa ba, haihuwar ta ta farko tahaifi mace Mai kama da babanta sak, suka sakawa yarinyar suna fatima, Wato sunan kakarta, amma suna kiranta da Nihla (kyauta)

Wannan shine labarin Mazawaje family

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

“Diddi tunda su yaya Abba suka tafi ko, kullum sai nayi mafarkin su”

Dasauri ta kalli yarta ta taga hankalinta yana kan wasa ma Kamar ba itace tayi magana ba, “suwa kike mafarki Nihla?”

Kallanta tayi cikeda qosawa tace “Diddi nace miki su yaya Abba, nayi mafarki shima munata wasa dashi”

Diddi tace “shi Abban ne ya koma yaya Abba?”

“eh Diddi, ai shine yace nadena cemasa Abba, saide yaya Abba”

Diddi ta Jinjina kanta tace “to suma sauran ai yayunki ne, dukansu haka zaki dinga fada musu”

Tace “to Diddi, yaushe zamuje wajansu?”

Daria Diddi tayi tace “kinason zuwa wajansu ne?”

“eh inaso naje, wai a wanne garin suke Diddi?”

“Suna kano, Nihla, kibari idan akai muku hutu saina kaiki, kiga qawayenki su Aisha, da ilham, da Dida, su Diyana”

“Diddi duk agidan suke suma?”

Diddi tace “duk suna gidan Nihla, idan mukaje zaki gani, gidane babba sosai, kowa aciki yake, amma kowa yana part dinsa, kuma akwai nisa atsakani, amma duk gidanmu daya dasu”

Cikin murna tace “to yaushe zamu tafi Diddi?”

Cikin sauri qosawa da maganar ta tace “nace miki idan anyi muku hutu”

Tace “to Diddi”

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Haka Rayuwar taci gaba da tafiya, yara naqara girma, kuma har zuwa wannan lokacin Diddi bataje gidaba, kuma bata taba kai Nihla cikin yan’uwanta sun gantaba, kullum tayi mata maganar Abba saita shashantar da zancen

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button