DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Saida yaja wasu second sannan yace “Amarya bakya lefi kokin kashe Dan masu gida”
“to waye Dan masu gidan?”
Murmushi yasaki Mai aji yace “farouq mana”
“Hmm kaiko, shiyasa kullum kuke fada ai”
“muna gidan Aslam, kuma suna jin yunwa”
“toooo, to saide Ilham din tadawo tadafa muku abinci”
“A a, kece zaki kawo mana”
“yanzu ya Abba fisabilillah tayaya Zan Taho ni kadai, idan Momy ta ganni ma zata hanani”
Shagwaba yafara yi yace “uhm.. uhm.. Allah nide yunwa nakeji”
????????♀️Kanta da dafe da hannunta tace “to naji”
qit takashe wayar sai mita take, mutum ana tabashi sai shagwaba, saikace shine autan duk duniya, nida nake wajan iyayena ni kadai banyiba saishi, haba ni wallahi nagaji ????
Mesu Diyana zasuyi inba dariya ba, Dida tace “wai Dan Allah ya Abba ne yake miki shagwaba?”
Tace “tab, ai saide in bamu zauna ba”
Diyana tace “ya birgeni, yanzu ba kowanne namiji ne yake wa matarsa shagwaba ba, saide ke mace kullum ki daddage kiyi, duk saboda ki faranta musu, maganin mata ne, mata ne suke nema, maganin tsumi ne mata ne, shagwaba ce mata ne, ke mace kullum kede kina kokari kiga kinyi Dan ran mijinki yayi fari, amma Ba kowanne namiji ne zaisha magani ba, saboda matarsa taji dadi, komai de saimu, saboda haka idan yafara miki shagwaba kema ki masa, zai dinga tattalinki, Dan kowanne namiji dakike gani Babu Wanda zaice bayason yasamu mace wacce ta’iya shagwaba “
Ilham tace” wallahi gaskiya ne kam “
” salamu alaikum “
Gaba dayansu suka juya suka kalli kofar dakin, baquwar fuska suka gani,yarinya ce qarama da alama zatakaisu shekaru, wata shegiyar gown ce a jikinta datahau jikin nata sosai, kallo daya zakayi mata kasan cewa lalle mace ce har mace, haka kana ganin hancin ta zaka tabbatar ita din bafulatana ce, duk yanda doguwar rigar ta baiyanar da hips dinta hakan baisa tasaka Babban mayafi ba, Dan qarami ne sai tayi rolling dashi
ganin yanda suka zubo mata ido suna Kallanta yasa ta qarasa shigowa cikin dakin ta ajiye jakar kayanta, sannan tazauna agadon ta cire mayafin datayi rolling tana firfita dashi
Tace “ku qaramana esin mana” ????
Ilham tana kallan ikon Allah tace “aqure yake ai”
Tace “to inaga Dan daga rana nake ne shiyasa,”
Ta kalli Nihla tace “amarya, wai baki ganeni bane? Naga duk sai kallona kuke, naje wannan part ance bakwa nan, naje wannan ance bakwa nan, saida nazo nan nayi sa’ah akace kuna ciki, ina qawayen naki naga saiku hudu kawai?”
Nihla tace “banfa gane kiba”
Dida ma tace “amarya batada qawaye, qawayenta yan’uwanta, mune kuma”
Itama tace “to gani naqaru, Rafi’ah cefa, yar gidan yayan baban ki Abdullahi na lagos”
Nihla tace “kut, au Rafi’ah wai kece? To ina Zan gane ki, kinga yanda kika koma kuwa”
Ta kalli su Ilham tace “cousin sister nace, yar gidan yayan babanmu ce, alagos suke dazama, babansu yana canji”
Gaba dayansu sukai murna,Dida tace “to yanzu ai kinga kinsamu qawa yan’mata”
Nihla tace “to Rafi’ah ko zaki kaiwa angwaye abinci, suna gidan Ilham”
Rafi’ah tace “angwaye? Sunada yawa?”
Ilham tace “gaskiya bazasu rasa yawa ba”
Tace “a a toba lalle nashiga ba gaskiya, dade mu biyu ne,bari na gyara fuskata,nikam Nihla ina yusuf Dan unguwar ku? Kwanaki naji baba yana waya da baban ki naji yace kuna Abuja agidan su”
Murmushi Nihla tayi “ya Yusuf, shima yana wajansu ai, idan kinje saiku gaisa dashi”
Tashi Rafi’ah tayi tashige toilet taqara gyara fuskarta dakyau, sannan tafita wajan Momy domin karbar Abincin
Tana fita Diyana tasaki ajiyar zuciya tace “kai duniya akwai kyawawan mata gaskiya, Wato Nihla wannan sister naki Babu qarya tahadu, kice muqara rike kazajenmu hannu bibbiyu” ????
Dukansu sukai dariya, ” oh Diyana uwar kishi” cewar Ilham
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Suna zuwa gidan iliya driver ya tsaya, tafuto tace “ga Abincin kashiga kakai musu, ni ina jiranka anan”
Iliya yayi dariya yace “ranki yadade aida Kinshiga”
Tace “a a, idan kakai musu kace ana magana da yusuf”
Iliya yaje yakai musu Abincin, yafadi saqonsa, yana fada kowa yafara yiwa Yusuf kallan kallo, Adam yace “iliya kace mace ce take sallama dashi?”
Yace “eh, tare muke da’ita ai, itace tabani Abincin tace na kawo muku, budurwa ce”
Dariya sukayi, Aslam yace “to kode munyi kamu ne” ????
Yusuf yayi Murmushi kawai ya cewa iliya “Muje”
Suna futowa yaganta a tsaye daga nesa, begane taba, cikin ransa yace anya kuwa shi take nema? To Wacece wannan saikace aljana saboda qira? ????
Wajan ya qarasa, ta kalleshi cikin murmushi tace “baka gane niba ko?”
Yace “gaskiya kam, kiyi hakuri bangane kiba”
Tace “Rafi’ah cefa, yar garinku, Wanda suke lagos”
Saida yayi jimmm sannan yace “okeyyyyy nagane ki yanzu, to Rafi’ah aikin girma ina Zan gane ki idan akan hanya ne?”
Tayi Murmushi tace “na tambayi Nihla ina kake, kuma ance min a gidanku suke zaune a Abuja, shine dana tambayeta tacemin kaima kana nan gidan”
“wallahi ina nan, Yaya school, meyasa baki shigoba kuma?”
“ai ance min angwaye suna ciki, nasan kuma suna dayawa,gashi ni kadai ce, shiyasa nace idan yakai muku Abincin yaturo ka mugaisa “
Yace “gaskiya kin kyauta, Allah yabar zumunci, zakije wajan dinner din ai anjima ko?”
Tace “eh zamuje tareda amarya”
“to shikkenan idan bamu wuceba saimu dauke ki mutafi”
“to shikkenan nagode, sai anjima”
Tajuya wajan iliya dake jikin Mota yana jiran su, tashiga suka tafi, Yusuf yabi bayan motar da kallo, ikon Allah, ashe yanzu ana samun yanmata masu sada zumunci haka, Wato ita haka kawai dansu gaisa ta kirashi, amatsayin sa na Dan garinsu
Yayi ajiyar zuciya tareda komawa ciki, yana shiga kuwa duk suka bishi da kallo, Fawaz yace “Malam Yusuf irin wannan dadewa haka, kode kasuwa ta tabbata ne”
Yayi Murmushi yace “yar garinmu cefa”
Abba da tunda aka fara magana baisa bakiba yace “to menene ai ana auren yar gidama” ????
Aslam yace “Kamar yanda kayi ko”
Adam yace “mukayi de” ????
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wajan dinner yayi kyau sosai, an qawata shi yanda ya kamata, kujerun da Amarya da Ango suka zauna sunacan sama, sauran mutane kuma anshirya musu nasu wajan zaman, iyaye mata duk sunzo, nan take aka fara gabatar da Komai bayan shigowar Ango da Amarya, gown din da tasa launin light green tayi masifar yimata iyau, yar qaramar posting din hannunta kadai ma abin kallo ce, yayinda Ango yasaka farin kaya yaci Babbar riga Kamar ba shiba, hannunta yana cikin nasa, mc yafara gabatar da mutane sannan aka umarci amarya da Ango sufuto su yanka kek
Rafi’ah tana gefen Nihla sai tafi ake musu ga kida yana tashi, Dan qarami ta yanko tasaka masa saikawar dakai take taqi yarda suhada ido, waje yadauki ihun murna, shikuwa daya yanko nasa saida yasa hannunsa yariqe waist dinta sannan yamatso da bakinsa dab da nata Kamar zaiyi kissing dinta yace “haa”
Murmushi tayi, takai masa dukan wasa a qirjinsa “sannan tabude baki yasaka mata”
Su Momy suna ganin haka, suka miqe daya bayan daya suna barin wajan, akabar iya yaran su kadai ????
Ana kiran mutane suna fita suna rawa, Diyana tayi tagumi tanajin haushi, taso tayi rawar amma Babu hali,saboda cikin ta ????
Nihla tana zaune awajan dasuke ta hango ya Yusuf da Rafi’ah suna Selfie, taji dadin yanda Rafi’ah take kulashi, ko banza hakan zaisa tarage masa wata damuwar, ita har yau Yaqi bata dama ma suyi magana, amma tunda yakula yar’uwarta ma taji dadi sosai