DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Hajiya Na’ila tarasa Inda zata dora ranta saboda murna, shi kansa Adam abin ba qaramin dadi yayi masaba, yau shine da dansa na kansa

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Bayan kwana shida suna zaune adaki ta dashi, tadubeshi tace “ya Adam nikam sunan wa zamu sawa yaron nan ne? Nasan sunan Daddynku zakasa ko?”

Adam yace “a a maryam, bazan sa sunan Daddynmu ba”

Tace “to ya Aslam zaka saka?”

“A a, bashi Zan sakaba”

Cikin mamaki tace “towa zaka saka?”

Ajiyar zuciya yayi yace “maryam, Aslam dan’uwana ne, dama can akwai zumunci a tsakanin mu, Karki Manta Allah ne yahadamu maryam, Inda danta iyayen mu ne ba zasuyi tunanin hadamu aure ba, amma gashi kakanninmu sunyi wannan tunanin, badon komai ba saidon su qara danqon zumunci a tsakanin mu, mu jikokinsu, kinga Aslam yasaka sunan Abba, dan haka nima acikin mu jikoki Zansaka sunan wani”

Ajiyar zuciya tayi tace “hakane kam, gashi yanzu atsakaninmu jikokin muna zumunci sosai, haqiqa auren zumunci akwai dadi idan har iyaye suka kauda kai akan yayan su, amma Muddin akace yara sun samu matsala, har aka samu rabuwar kai adangi wannan yana bayan wannan, wannan ma yana bayan wannan, to tabbas dole aure ya lalace, kuma dole kan mutanan wannan dangi yarabu, yanzu de sunan wa zaka saka masa? “

Kai tsaye yace “Fawaz”

Murmushi tayi tace “to Allah ya rayamana ya Fawaz, Dida tayi miji kenan” ????

Gaba dayansu sukai murmushi

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari sunan Diyana, Tun safe Dida take fama da tashin zuciya, komai taci sai amai, hankalin Fawaz yatashi, dan haka yadauketa suka tafi asbiti, suna zuwa kuwa aka gama yimata gwaje gwaje, doc din yafada musu abinda gwajinsu yabasu
Fawaz yace
“Doctor, da gaske kake mata ta tana dauke da ciki harna Tsawon wata biyu?”

“qwarai kuwa Fawaz, matarka tanada ciki, Allah yasauketa lafiya”

Cikin farin-ciki yayiwa Doc din godia, suka Taho, ahanya ma yana driving amma bakinsa yakasa rufuwa, gidan Diyana zai kaita wajan suna amma saiyai kwana suka tafi gida

Wannan ne karon farko daya taba kawota wajan ummansa tunda aka musu aure, ummah taji dadin ganinsu sosai

Suna zaune afalo shida ita, Umma kuma tatafi takawo musu ruwa, yadubeta yace “gaskiya ko Baby Dida, idan kika haifamin Baby me kama dake dakuma halaiyarki zanji dadi” ????

Ta kalleshi tace “ko”

“hakane, wannan shine fatana, naji dadi sosai, Allah ya saukeki lafiya, me kikeso nasiyo miki amatsayin gift ki fadamin pls?”

Kai tace “bana son komai ya Fawaz, kawai sonake karabu da wannan abokin naka Wanda yake daukan hankalinka zuwa shaye shaye”

Murmushi yayi yace “angama hajiya ta, saime kuma?”

Saida tayi farrr da’idonta sannan tace “saikuma zancen aiki, ka daure kafara zuwa Kamar yanda kowa yake tafiya aiki, kadinga temakon Abbanku awajan ajikinsa, zaiji dadi sosai”

Murmushi yayi yace “angama Baby Dida, aini yanzu gaba daya nazama naki, sai yanda kikai dani”
Ya matso jikinta yayi kissing kumatunta

Zaro ido tayi tace “Allah idan ummah tadawo taganka ko Babu ruwana”

Dariya yasaka, adede lokacin ummah tashigo falon hannunta dauke da lemo, bayan ta ajiye musu suka qara gaisawa, Fawaz yace “ummah, please ki fadawa Abba na next week Zanfara futowa aiki”

Farin-ciki yakama hajiya Abida tace “Alhamdulillah, Allah abin godia, toshknn Fawaz, yana zuwa Zan fada masa insha Allah”

Sake dubanta yayi yace “am umma, daga asbiti fa muke, Doc yace Dida nada ciki” ????

Cikin sauri Dida takai Kallanta gareshi, sannan tarufe idonta cikin kunya

Ummah tace “alhmdllh, kuce niyau da labarai masu dadi kukazomin” ta kalli Dida tace “Dida? Allah ya saukeki lafiya kinji yata?”

Dida tayi Murmushi shikuwa Fawaz yace “Amin ummah” ????
Sun Dan dade suna fira sannan sukai mata sallama suka tafi gidan Diyana

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Taron suna ya qayatar, Diyana da danta Fawaz sun shiga sun fita, wannan karon ma hajiya Na’ila itace tayi kaka gida akan komai, ita ala dole sunan jikanta ake, Kamar de yanda tayi a sunan Ilham ????

Gaba dayansu yaran sukam suna dakin maijego sunata fira, sai bayan sallar magrib ya Abba yazo yadauki Nihla suka tafi gidan Momy
Suna zuwa Nihla tafada jikinta cikin murna, anan falo suka baje kolin firar yaushe gamo, shikam yana kawota yafice

Saida sukai sallar ishsha’i sungama cin abinci, Momy taje daki tahado mata wani tsumi takawo mata tace “ga wannan kisha, rannan Abba yazo namanta ban bashi yakai miki ba”

Jikin Nihla yayi sanyi ta karba tace “Momy ni wannan abun banason sha”

“shirman banza, meyasa zakice ba zakisha ba? Cemiki akai wannan rawar kan na Abba abanza yake miki?”

Cikin shagwaba tace “to Momy shima tambaya ta yakefa wai kona sha wani abu.. ni… ni wallahi Momy auren nan inaa” ????

Ajiyar zuciya Momy tayi, ta kalleta dakyau tace “Nihla, shiyasa naga duk kin fada, kinyi yar kama?”

Cikin in-ina Tace “a a Momy ni kawai….” saikuma tayi shiru

Momy tace “Nihla bakida Wanda ya fini kinji ko, kidena kallo na amatsayin mahaifiyar Abba, ki kalle ni amatsayin mahaifiyarki, fadamin menene yake damunki kika rame”

Ahankali tace “Momy ya Abba ne, kusan kullum fa… Allah Momy rana daidai ne bayayi nikuma zafi nakeji har yanzu, shine yace idan wani abu nake sha yake sake rufewa tona dena”

Momy tayi Murmushi tace “tokuma Nihla saboda wannan sai kiyi shiru? Yanzu kenan badon na tambayeki ba haka zaki zauna ko?, toki godewa Allah ma dayake tsallaken wasu kwanakin”????

Nihla tayi shiru kanta akasa, takasa hada ido da Momy

Momy ta dafata tace “Karki sake boyemin damuwar ki kinji ko? Bari inyi magana da wata qawata ta kawomin maganin dazaki dinga sha insha Allah zaki denajin zafin, tunda nasan ba yanzu Abban zai dawoba harta aikomin ma kafin kutafi, amma yanzu de dauki wannan tsumin kishanye duka “

Nihla ta daga kanta alamun to, sannan tadauka ta shanye shi tas

(eh lalle Momy kin bawa Abba dama sosai ????

Najiya dayau kenan, Mutara zuwa gobe insha Allah ????????)

Amnah El Yaqoub ✍????❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

63&64

Saida Momy taga Nihla ta’ajiye cup din Babu komai sannan tadauki wayarta, takira qawar tata tatashi tayi cikin dakinta tana waya

Nihla tasaki ajiyar zuciya, tabbas barin damuwa acikin zuciya ma wata illar ce, yanzu gashi data fadawa Momy matsalar ta tana shirin tafiya

Tashi tayi daga kan kafet din falon takoma kan kujera ta kwanta tazuba wa tv ido tana kallo
Jitayi yanayin ta yanata sauyawa, kuma tabbas tasan cewa hakan baya rasa nasaba da maganin da tasha yanzu, shigowa cikin falon yayi bakinsa dauke da sallama, ta amsa masa tana kallansa

Kafafunta yadauke Yazauna awajan sannan yadora mata kafar akan cinyarsa yace “muwuce yanzu ko?”

Fuska ta yamutsa alamun tanason kuka tace “ya Abba Dan Allah mukwana anan kaji”

Wani irin shu’umin kallo yayi mata, yasaka hannunsa yana sosa mata tafin kafarta tareda shafa wa yace “kin tabbatar zaki iya?”

Idonta ta lumshe alamun jin dadin abinda yake mata tace “emana to menene”

Ganin bata gane Inda maganarsa ta dosa ba yasa yafuto mata baro baro yace “zaki iya rufemin bakina idan kika sani kuka ko?”

Cikin shagwaba tace “uhm.. To ya Abba basai muhaqura ba”

“muhaqura dame? Bari kiji dama can bansan haka akeji ba, Inda nasani ko kwana daya bazan bari kiyi batare danayi ba”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button