DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Batasan wanne mafarki yake magana akaiba, haka tasa hannu ta rungumeshi, nan take yayi ajiyar zuciya

Saida yaqara yin yanda yaso da’ita, sannan suka samu suka huta, washe gari kuwa suka lula qasar saudia, saiga Nihla har wajan tuqin jirgi itada Abba, yana nuna mata abubuwan sosai, itace harda yimisu pictures

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tsawon wata daya sukayi a qasar saudia, babu abinda Abba yake sai addu’ah akan Allah yabashi yaya nagari, sunsha addu’ah sosai, ba subar kowaba, zuwa yanzu kam Nihla tafara murjewa, hankalinta Akwance yake yanzu, tunda tafara sabawa da Abba dakuma yanayin yanda yake, saida sukai wata daya da sati biyu sannan suka dawo gida, ta qara cika sosai, komai nata yasake futowa saima abinda yaqaru Wanda ada bata dashi, kana ganinta zakasan hutu Yazauna, jikinta Kamar ka latsa jini yafuto, dasuka dawo gida ma Abba baya barin ta haka kawai, kullum yana buqatar matar sa, satin su daya dawowa suka tafi Abuja gidan Yusuf

Gidan mamy suka fara zuwa suka gaisa da Adala dakuma mamy, sannnan suka tafi gidan Yusuf din

Abba kam amota Yazauna Nihla tashiga ciki kanta tsaye, sai sallama take kwalawa

Rafi’ah tana daga cikin daki tafuto, tana ganin Nihla tafada jikinta cikin murna, anan falo suka zauna Nihla tace “ke tareda ya Abba fa nake, yana compound amota”

Rafi’ah tace “kuma akan ki fadamin dawuri, bari na fadawa ya Yusuf yana ciki ai”
Cikin dakin tashiga tafada masa, yafuto suka gaisa da Nihla sannan yafita yashigo da Abba cikin falon
Rafi’ah takawo musu abun motsa baki, suna firarsu cikin farin ciki, kai ba zakace wani abu yataba shiga tsakanin suba
Cikin daki Rafi’ah ta janye Nihla, ta dubeta tace “ke naga auren ya karbeki Nihla, sai wata uwar qiba ma dakika hada”

Tace “ke wacce qiba, yanzu nefa nadan ciko, da baki ganni ba wallahi, duk na rame”

Rafi’ah tace “um abin kam Babu sauqi gaskiya, ga ya Yusuf ba haquri, ke ni Tun ina kuka yanzu nadawo ma na haqura”

Nihla tace “sai hakuri kam Rafi’ah, Allah dai yabarmu tareda mazajanmu”

“amin Nihla, kinga wani turare da aka aikomin shi daga lagos, kiyi amfani dashi zakiji da dinsa”

Tureren Nihla ta karba tace “nagode Rafi’ah”

Anan gidan suka wuni, sannan suka koma gidan mamy sukayi wa su baba sallama suka tafi gida

Basuzo gidaba kuwa sai wajan magrib
Gajiya tataru tayiwa Nihla yawa, nan take zazzafan zazzabi Yarufe ta, Abba yadawo daga masallaci da daddare yana zuwa dakinta yaganta cikin bargo, yana yayeta yaga tana rawar sanyi
Cikin sauri yace “subhanallah, menene yake damunki?” yafadi haka yana janyo ta jikinsa

Idanunta ne suka fara lumshe wa tazube ajikinsa, jikinta yafara tabawa yace “zazzabi ne ai yakama ki, kode mutafi asbiti”

Girgiza kanta tayi, tabude baki zatai magana wani irin akai yataho mata, cikin sauri tatashi tayi cikin toilet tafara kwara amai
Shima toilet din yabita yariqe ta yanayi mata sannu, tana Dagowa tazube ajikinsa, yasaka hannu yadauko ta, ya kwantar da ita yanayi mata sannu
Duk yanda yaso sutafi asbiti qin yarda tayi, yarasa menene tsakaninta da asbiti
Haka ya haqura suka kwanta tana jikinta, amma basu runtsa ba, kwana tayi tana amai
Da sassafe kuwa yasaka mata kayanta, suka tafi asbiti, sai kuka take masa ita batason allura
Suna zuwa kuwa aka daura mata qarin ruwa, sannan akayi mata text na jini dana fitsari, ba’a dade da saka mata ruwanba bacci ya dauketa
Doc. Yazo har dakin yabawa Abba sakamakon txt din, cikin sauri ya kalli fuskar Doc. Yace “Doc. Mafarki nake kokuma gaskiya ne? Kafadamin gaskiya da gaske Nihla tanada ciki?”

Doc. Yace “congratulation” sannan yafice daga dakin cikin murmushi

Jikin Abba har rawa yake yakira Momy da Daddy, dasu ya Usman yafada musu
Ruwan yana qarewa kuwa suka Taho gida, kai tsaye taga yayi hanyar gida da’ita, ahankali ta kalleshi tace “ya Abba gida zamuje?”

Cikin murna yace “gida Zan kai ki wajan Momy, daga nan nakoma nadauko mana kayanmu”

Kallansa tayi tace “meyasa zamuje?”

Cikin murna ya kalleta yace “kefa yanzu bake kadai bace, nakusa zama Daddy Abba, dan haka wajan Momy Zan maida ke mudinga baki kulawa harki warware”

Murmushi tayi, batace masa komai ba
Yace “kinyi shiru”

Cikin shagwaba tace “ya Abba ancefa haihuwa da wahala”

“waye yafada miki? to wasa suke miki”

Tace “Allah da gaske ya Abba?”

Yace “baki yarda ba ko?”

Murmushi tayi tace “um um”

Babu Wanda yasake magana har suka qaraso gidan cikin part din Momy, Momy na zaune afalo ta gansu sun shigo, tace “ashe baqi ne dani yau, sannu Nihla, zonan ki zauna”

Nihla ta kalli Abba, yasakar mata wani irin murmushi yana kashe mata ido daya, karde ya Abba harya fadawa Momy komai, tunanin tane ya katse lokacin da Momy take cewa “Allah yaraba lafiya, zoki zauna kinji” ????

Zama tayi, shikuma Abba ya kalli Momy yace “Momy, zanje nadebo mana kayanmu, mun dawo gida kenan saita gama warware wa zamu koma”

Momy ta kalleshi taga sai wani murna yake yana jin dadi, Wato za’azo abaje mata kolin rashin kunya agida, tatuna ranar da sukazo da daddare da abinda tagani, tace “kayan ta, kokuma kayanku?” ????

Comments
Share

Amnah El Yaqoub ✍????❣️DANGI ‘DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook ????
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493

Nasadaukar da wannan shafi ga dukkanin masu karanta wannan labari, i luv u All ????????????

65&66

Zuciyarsa daya yace “Momy kayanmu”

Momy tace “a a, kayan ta zakaje ka dauko mata, idan ta murmure cikin ta yatasa saita dawo, amma yazakubar gida Babu kowa duk kudawo nan”

Cikin sauri ya kalli Momy yace “a a Momy, to tatashi mutafi, dama fa abinda yasa na kawo ta nan din, saboda idan nafita karta rasa Wanda zai dinga bata kulawa, shiyasa na kawo miki ita, idan nafita gaki nan, idan nadawo kuma shikkenan”

Momy tace “bari kaji Babu Inda zataje, ai yanda tazo totazo kenan”

Shima yace “a a Momy, kiyi hakuri kawai, gara mutafi, to haka Zan zauna Acan din ni kadai”

Nihla tayi Murmushi ganin yanda suke yi shida Momy tace “Momy kibarshi yadauko mana kayan namu, can dinfa Babu kowa, Momy kibarshi yadawo nan shima”

Momy tayi saqare tana kallan ikon Allah, tace “to ai shikkenan tunda mijinki kikeso”

Nihla tayi Murmushi tatashi tabar wajan, shima fita yayi da sauri saboda kar Momy ta sauya shawara

Momy tayi Murmushi ganin kan yaran nata yanzu yahadu, dama kuma abinda take fata kenan, yanzu kuma fatansu Allah ya sauki Nihla lafiya

Da daddare suna kitchen itada Momy, suna gudanar da Abincin dare, zuciyarta tafara tashi, cikin sauri tafuto daga kitchen din tana rufe bakinta datake shirin yin amai, dashi taci karo zai shigo kitchen din shima

Momy tabiyota da sauri tanayi mata sannu, Abba kuwa riqeta yayi yana cewa “ko aman ne?”

Kafin ma tabashi amsa tafara yin aman, duk ta bata masa kayansa da wajan

Momy tace “subhanallah, wai haka takeyi dama”

Cikin damuwa yace “Momy to ai yau da sauqi ma naga Tunda mukazo batayi ba”

Tace “kuje daki ta gyara kayan ta, bari agyara nan din”

Kafadunta yariqe yana mata sannu suka wuce dakinta
Kai tsaye suna zuwa yafara cire mata kayan ta, shima ya cire nasa kayan suka shige toilet
Wanka yafara yimata, sai kawar dakai saboda wannan shine karo na farko dasuka tabayin wanka shida ita atare, shikuwa Babu ruwansa shawa ma yasakar musu yariqe ta ajikinsa hannunsa kuwa yawo yake a jikinta yana goga mata sabulu, Tun suna wankan cikin hayyaci har suka fara Manta Inda suke, aka wuce Romance acikin Ruwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button