DANGI DAYA HAUSA NOVEL

DANGI DAYA HAUSA NOVEL

Bai san lokacin da yasaki sabulun ba yacafki bakinta yanasha, daqyar suka gama wankan, suka futo, amma kana ganinsa kasan akusa yake, domin kuwa kalar Idanunsa ma kadai ta isa shaida

Haka de yake kokarin sharewa, har suka shirya suka dawo falon, Daddy yadawo gidan ya gansu yace “a a, kukuma yau kuntuna da kenan”

Murmushi sukai baki dayansu

Yace “Abba ai yakirani awaya dazu, Allah ya sauke ta lafiya”

Abba da Momy sukace “Amin”

Wajan dining Daddy yawuce, Momy ma tabi bayansa, Abba yamatso kusa da Nihla har jikinsa na gogar nata, yayi qasa da murya yace “ai yau adakina zamu kwana ko”

Cikin sauri ta kalleshi tace “wanne irin dakinka ya Abba, ka Manta agida muke ne”

Momy tana daga nesa take hango su, taga sai kallan fuskar Nihla yake yana magana qasa qasa, amma batasan me suke fadaba

Abba yace “to menene Dan muna gida, bafa haramun bane”

Tace “duk da haka, su Momy zasu iya tunanin wani abu muke”

Yace “to idan suka sani dinma ba dadi zasuji ba, bakiga yanda kowa yake murna kinsamu ciki ba?”

Tace “nide gaskiya kunya nakeji ya Abba”

“wai kunyar me, ko bakyajin dadinne?”

Shagwaba tafara masa tace “tokuma ya Abba Dan inajin dadi saimuyi agabansu Momy”

Kansa yadafe da hannunsa ????????‍♂️”to yanzu ke saboda kunya saimuqi yin abinmu, ai sunsan da hakan shiyasa suka mana aure ko, kinga Dan Allah tashi Muje kici abinci, babu komai acikin ki”

Haka tatashi ta nufi wajansu Momy amma bawai Dan ta yarda da maganar tasaba

Bayan sun gama cin Abincin falo suka dawo dukansu, yau harda Daddy azaman

Daddy yajuyo ya kalli Abba yace “Abubakar wata nawane cikin nata ne”

“wata daya ne Daddy, haka de nagani ajikin takardar txt din nata”

Daddy yayi Murmushi yace “to Alhamdulillah, Allah ya sauke ta lafiya”

Daga nan yatashi yawuce daki, itama Nihla Miqewa tayi ta kalli Momy tace “Momy saida safe”

“to Nihla saida safe”

Abba yazuba mata ido yana kallan dakin da zata shiga, kawai sai yaga tashiga nata dakin
Kallan sukaci gaba dayi shida Momy itama tagaji tayi masa sallama tatafi

Hamdala yayi daya ga tafiyar Momy, dama jira yake tatashi yabi bayan matar sa

Kayan kallon ya kashe, kai tsaye yatafi dakin Nihla, wutar dakin nata akunne, ya kashe, sannan ya cire kayansa shima ya kwanta

Cikin baccinta taji ana shafa ta, ahankali tafara bude idonta harta budeshi gaba daya, sai ganin Abba tayi yana kokarin dage mata riga

Kallanta yayi yace “kin tashi?”

Tace “ya Abba nide Dan Allah katashi kafita”

Rigar yagama dagewa sannan yatura hannunsa ciki yana wasa da Kirjinta cikin salon da yasan tanaso, ahankali yace “kibari mana to ko sau dayane muyi, kinji”

Babu yanda ta’iya haka tabarshi, saida tafiya tayi nisa yafara yimata ihu, yana kiran sunanta, sai sambatu yakeyi, tasan cewa su Momy ma sunji shi, dama kuma shine abinda take gudu

Hannu tasa tarufe masa bakinsa, amma saiya qwace yaci gaba da wasu irin maganganun da bai kamata ajisu ba, cikin dabara tahade bakinsu waje daya, to anan ne tasamu lafiya yayi shiru

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Washe gari kuwa haka yake ta al’amuransa ko ajikinsa, itace ma Dafarko take ta takure kanta, amma da taga Babu Wanda ya lura da itama kawai saita share, ta warware taci gaba da abun gabanta
Haka Rayuwar su take tafiya cikin kwanciyar hankali har cikin ta yacika wata hudu, a lokacin Dida haihuwa yau ko gobe, kowa yaga Dida saiya tausaya mata, saboda cikin yana bata wahala sosai idan tazauna bata iya tashi, awajan take wuni, saboda girma da kuma nauyin cikin nata

Nihla kuwa fitinar Abba ce tasa suka tattara kayansu suka koma gidansu, a lokacin cikin yadena bata wahala, saide kwadayi datake yi kawai
Shima idan akwai agidan zata tashi tayi abinta, idan Babu kuma zatayi wa Momy waya akawo mata

Yau Tun asuba Dida tatashi da naquda, Fawaz yarasa yaya zaiyi gashi gari anata kiran sallah, haka yakira mamansa awaya yafada mata, tace gatanan zuwa
Kafin ma ta qarasa gidan kan Baby yafuto, Dan haka tana zuwa tace Fawaz yabasu waje, haka yafuto yana jin ihun Dida, Tun yana daure wa harya kasa hakura yashiga dakin, ummah tanata mata sannu, shigarsa dakin kenan Allah ya sauke ta lafiya

Ummah ta kalli Fawaz tace “Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya”

Fawaz yayi mutuwar tsaye ganin irin wahalar da Dida tasha, sosai yaji tausayin yarinyar, tasha wahala a rayuwa kuma tayi hakuri sosai, idanunta sunyi jaga jaga da hawaye, cikin sauri yayi wajanta yanayi mata sannu

Da qyar ta kalleshi tace “ya Fawaz, ka yafemin, jinake Kamar Zan mutu”

Umma data gama yankewa Baby cibiya tace “karna sakeji kin fadi wannan maganar Dida, kiyi hakuri keda Allah yasa bakiyi doguwar naquda ba” ta goge wa Babyn jinkinsa tamiqawa Fawaz tace “ungo riqe Babyn Fawaz, kayiwa Allah godia ansamu namiji”

Hannunsa har karkarwa yaje yariqe babyn yana kallansa, Dida tariqe hannunsa tace “ya Fawaz, kabawa Diyana shi ta kula min da yarona, wallahi ciwo nakeji Kamar na mutu”

Jikin umma yayi sanyi, tace “Dida haihuwar kenan, bazaki mutu kibarmu ba kinji, da kanki zaki kula da yaronki”

Cikin ciwo Dida tace “wayyo… Allah na ummah Zan mut…kafin ta qarasa wani gagarumin ciwon yakamata, Umma tataba cikinta tadubi Fawaz tace” tashi kuje falo kayi mata addu’ah, wata haihuwar ce “

Zaro ido Fawaz yayi ????yace” ummah wai saita kuma shan wata wahalar? “

” banason shirme Fawaz, da abanza ake samun yaran? Tashi nace “????

Haka yafuto da yaron a hannunsa sai waiwayen Dida yake

Tun tana naquda cikin duhun gari, har aka idar da sallar asuba gari yayi haske, Umma tafara tunanin su tafi asbiti, domin kuwa qarfinta yaqare, haka lokaci daya tana qwaqqwaran nishi, wani Babyn yafuto

Sai a lokacin Dida tasamu damar yin wani bacci Mai nauyi, Umma ta gyara yaron sai kuka yake, sannan ta gyara Dida, Fawaz yana jin kukan Baby yamiqe yashigo dakin, hannunsa dauke da babyn, yaro yanata shan baccin sa ????????

Umma ta kalleshi cikin murmushi tace “to Alhamdulillah, tasauka lafiya, shima wannan din kaga namiji ne”

Hawaye yazubowa Fawaz, yasa hannu yadauki dayan yaron yazuba musu ido yana kallansu, yace “umma yanzu duk nawane?”

Tace “gashi kuwa Fawaz, Allah yaraya muku yaranku”

Tasa hannu ta karbi yaran tayi musu wanka ta gyara su tsaf, sannan ta kwantar dasu agefen Dida, itama ta zauna ranta fari tas
shikuwa Fawaz wajan Dida ya koma Babu kunya yasa hannu yana shafa kan matar sa ????

Babu Wanda ya tasheta acikinsu saida tasha baccinta sannan tatashi, tana tashi kuwa Fawaz yabata yaran yace “ga Baby’s dinmu Dida, kinyi kokari sosai Allah yayi miki albarka”

Cikin farin-ciki tasa hannu ta karbi yaran tana kallansu, wata irin soyaiyar su tana qaruwa acikin ranta, Umma kuwa tashi tayi tsaye tace “to Dida kihuta sai Muje asbiti adubaki, bari naje nakira yan gida afada musu”

Daga nan tafice daga dakin domin ta basu damar sakewa, tana fita kuwa Fawaz ya rungumeta ajikinsa, sai kissing dinta yake, cikin shagwaba tace “ya Fawaz haihuwa akwai wahala”

Yace “ai mundena daga yau, wannan wahala haka har kina cewa abawa Diyana yara” ????

Murmushi tayi takai masa dukan wasa a qirjinsa

Yace “nagode sosai Dida, haqiqa ke alkhaairi ce acikin Rayuwar Fawaz, kin dawo dani hanya madaidaiciya, kinyi hakurin zama dani a lokacin dakowa yake fadar mugun halina, babu abinda Zan saka miki dashi Dida sai godia, Allah yabarmin ke amatsayin mata ta ke kadai aduniya dakuma lahira, Allah ya rayamana, Aslam da Adam “????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81Next page

Leave a Reply

Back to top button