DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
Dubu na gaba ya yi yana haske mata fitila suka fita daga cikin ɗakin, sauran yaransa kuma suna tsaye a bakin ƙofar sai dai gabaɗaya yanzu sun kasa taɓa likkafanin da suka gani yashe a gefe wanda ake ce musu fatalwar ce ta ɗaure ƙafafuwan yaran da shi.
Sai da suka yi ta fi me ɗan nisa da yake banɗakin na da nisa da wurin ɗakuna kamar yanda al’adar ginin ƙauye yake. Suna ratsewa ta bayan ɗakin Marigayi Dubu ta zabga ihu tana yin gefe da sauri haɗe da faɗin, “Wayyo Allah hannuna.” Durƙushewa ta yi a ƙasa tana murza hannu haɗe da yamutsa fuska. Duna ba ƙaramin tsorata ya yi ba don idan idonsa ba gizo yake yi masa ba gani ya yi kamar wurgar da Dubu aka yi gefe. Gyaran murya ya yi yana kallon hagu da damansa a ɗan tsorace, amma sai ya basar don kar Dubu ta fahimci tsoron da yake ciki ya ce, “Ke Dubu lafiya, me ya samu hannun naki?” Dubu da ke satar kallonsa ta gefe ta sake shafa hannu ta ce, “Wani abu ne mai kaifi kamar farata na ji yana niyyar fisgata daga baya sai ji na yi an hakaɗa ni.”
Wata irin karta cikin Duna ya yi nan take gumi ya fara neman game jikinsa amma sai ya ɗaga gorarsa yana ƴan haske-haske ya ce, “Yana daga wurin ina.” Kusurwar ɗakin Marigayi mai carbi ta nuna ta ce, “Daga can ne.” Duna ya coge daga wurin da yake ya ce, “Wuce mu je ki nuna min to.”
Dubu tsabar mugunta ji ta yi dariya na neman suɓuce mata don haka ta miƙe sai kuma ta fara tafiya a dudduƙe tana riƙe ciki alamar fitsari ya matseta. Ganin haka ya sa Duna ya ce,
“Fitsari ko? Wuce muje idan mun dawo ma duba koma meye.” Shima da biyu ya faɗi haka saboda a lokacin da za a kuma yin wani ƙwaƙƙwaran motsi mai ƙarfi yana iya fita da gudu. Suna zuwa ta shiga banɗaki ta yi fitsari ta fito don kafin ta fito tuni Duna ya ƙagu saboda gani yake kamar wani abu zai kama shi. Suna tafe har suka bar wurin banɗakin suna yin gaba Dubu ta buga tsalle tana cewa, “Duna kanka ga shi nan zai warci kanka.” A guje Duna ya zuba yana ƙwalla ƙara haɗe da dafe kansa, don fitilar hannunsa sai da ta yi tsalle uku sannan ta tarwatse a ƙasa, batiran ciki suka yi gabas, kan fitalar ya yi yamma. Gangar jikin fitilar ta yi arewa gorar hanunsa ta yi Kudu. Dubu na ganin haka ta rufa masa baya sai dai tun a tsakar gida suka raba hanya don tuni Duna ya dafe katanga ya dire yayin da Dubu ta yi cikin ɗakin Yaya Babba a guje, Yaran Duna na ganin haka suma suka zuba a guje kowa ya kama gabansa. Su Barira da sauran mutane ɗakin Yaya babba suka hau gwara kan ƙananan yara aka rinƙa ƙwallo da su kamar yanda ake gara ƙwallo a filin wasa. Cikin ɗakin ban da kukan yara da ihun manya babu abin da yake ta shi a ciki.
Daga ɗakinsu Inna Furai suma tashi suka yi don tun lokacin da suka ji ihunsu Barira, gabaɗaya suka watssake. Lantan ce ta fara miƙewa a zabure mai bin bayanta Inna Furai sai kuma ragowar mutanen ɗakin kowa ya yi tsuru-tsuru. Jin maganar ƴan bijilanti ne ya sauƙaƙa musu damuwar da suke ciki. Sai dai ihu da gudun Duna ya yi ya fi komai kaɗa musu ciki don, a wannan lokacin sun gama sadaƙƙarwa da indai Fatalwar ta fafake su babu mai tsira daga hukuncinta. Lantan hawaye ne ke zuba a kan dakalin fuskarta ga wani irin kaɗawar ciki da take fama da shi. Cikin kuka ta dubi Inna Furai ta ce, “Furaira sai da na gaya muku ku bar ni na tafi amma aka hanani tafiya ni da zuri’ata, yanzu don Allah idan tsautsayi ya ritsa da ni fa? Maganar gaskiya idan na mutu ta wannan hanyar ranar gobe ƙiyama sai an yi mana hisabi da Garba don shi ne sila.” Ta ƙarasa maganar tana son jin ta bakin Inna Furai amma sai gani ta yi ta zura mata ido tana kallo, Lantan dafa mata hannu ta ce, “Furaira ko bakya ji na ne?” A wannan karon ma gani ta yi Inna Furai ta sake zura mata ido tana kallo ko ƙiftawa bata yi ba. Lantan na jijjiga Inna Furai sai gani ta yi baya luuu!
Lantan ta zuba kabbara haɗe da cewa, “Innalillahi yau me nake gani haka jama’a ku taimaka mana wallahi sun fara ta kan Furaira.” Nan fa suka ƙara ruɗewa sai Mardiyya ce ta yi ƙarfin halin yayyafa mata ruwa don ta fi zargin Inna Furai suma ta yi. Inna Furai na farfaɗowa suka fara jero mata sannu sai ji suka yi tana amsawa da,
“Ashhadu’anlla’ilaha’illallahu, wa’anna Muhammadarrasulillahi.”
Lantan ta yi sauri ta ce, “Furaira me kike faɗa ne?”
Inna Furai da bata cikin hayyacinta ta ce, “Wa saumu ramadana. Amma Hajji kam sau ɗaya na taɓa ziyarta.” Lantan rasa abin yi ta yi sai kawai ta fashe da matsanancin kuka tana yi tana fatar majina ta ce, “Tun da Uwata Mai carbin Malam ta haife ni ban taɓa ganin ƙadaddararrun ranaku kamar waɗannan ba kai jama’a yanzu Furaira daga suma sai hauka.” Inna Furai bata san me ake yi ba don haka suka ƙarasa ganin daren har zuwa asuba Inna Furai na yi musu sumbatu.
Washegari.
Tun asuba da mazan gidan suka fito aka sanar da su abin da yake faruwa, don tun da suka wayi gari da ganin gororin ƴan bijilanti da fitilar Duna sai kuma takalmin ɗaya daga cikinsu, suka tabbatar da babu lafiya. Da aka sanar da su abin da yake faruwa wasu daga cikin mazan zuciyarsu ta fara aminta fa zancen fatalwar, saboda dama da Auwalu da Baba Sule tuni suka aminta da abin da aka sanar da su. Ba shiri aka ɗauki Inna Furai aka wuce da ita asibiti, saboda jikinta wani irin zafi da ya yi ga sumbatu ta take yi ba kai ba fasali.
Kaso casa’in da tara na mutanen da suka halarci gidan mutuwar a wayewar garin duk suka ɗaɗe kowa ya kama gabansa. Lantan dama ko sallama ba ta yi musu ba tana idar da sallar asuba ta fice ko jakar kayanta bata ɗauka. Ta so ta yi wa Autalliyarta magana ta ɗauko Salihu su tafi amma gani take ko ya ta ƙara ƴan sakanni komai zai iya faruwa. Wannan lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Dubu, don gabaɗaya gidan abin da ya rage daga ƴaƴa sai jikokin gidan. Wasu daga cikinsu har sun yi niyyar tafiya aka ce su bari a ga yanda jikin Inna Furai zai yi. Yaya Babba ta sake jaddadawa ƴaƴanta tana son zama da su idan komai ya daidaita akwai maganar da za su tattauna mai muhimmanci.
Wannan zaman da aka ce za su yi ba ƙaramim ɓata ran Hajiya Nafisa da Hajiya Fauziya ya yi ba. Ita kuwa Hajiya Rahama ko a jikinta damuwarta ɗaya fargabar da suke ciki ta rashin kwanciyar hankali.
Asalin Zuri’ar Mai Carbi.
Asalinsu mutanen garin Kano ne cikin ƙaramin ƙauyen Ɗangwaro dake jihar Kano. Mai carbi Su biyar ne a wurin Mahaifi da Mahaifiyarsu. Maza uku mata biyu amma acikinsu saura Mutum Uku rayayyun. Yaya Idi, Malam Munzali sai Lantan wacce dama ita ce ƴar autarsu. Sunan Yaya Babba Aisha wacce aka fi yi wa laƙabi da Indo. Ƴar uwar Marigayi Mai carbi ce ta fannin Mahaifinsa ƴar maza zar suke, an yi musu auren zumunci suka zauna anan cikin garin Ɗangwauro.
Inna Furaira ita ce matarsa ta biyu ita ma ƴar uwarsa ce ta ɓangaren Mahaifiya, ita ma auren zumunci aka yi musu sakamakon Mahaifiyar Mai carbi ta nuna itama dole ya auri ƴar ƙaninta tun da ya auro ƴar ƙanwar Mahaifinsa. Wannan dalilin ya sa aka sake yi masa aure bayan yin aurensa da shekara biyu a lokacin Yaya Babba tana goyon Baba Abubakar.
Ƴaƴan Yaya babba Shida Maza biyar Mace ɗaya. Akwai: Baba Abubakar, Baba Munkaila, Baba Sule, Baba Shehu, Baba Aminu, Baba Adamu sai Hadiza. Inna Furai tana da ƴaƴa biyar akwai: Larai, Baba Sabi’u, Baba Musa, Baba Sha’aibu sai Baba Auwalu.