DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
“Idan baki rufe mini baki ba zan harbe ki na wurgar da banza a wurin nan.” Wata ajiyar zuciya da Dubu ta sauke idan ka ji za ka yi tsammanin numfashinta na ƙarshe ne zai fita. Bata san lokacin da ta haɗiye kukanta ba, ban da raba idanu babu abin da take yi, haɗe da jin wata irin da-na-sanin zuwanta duniya. Saboda ta san da ba’a haifo ta ba babu wata ƙaddara da za ta haɗo ta shi har ya nemi kashe ta da bindiga murus ya wurgar a gefen hanya. Don tun da take bata taɓa ganin bindiga ido da ido ba sai dai ko idan tana daga moto ta hangota a hannun Sojoji ko ƴan sanda. Amma yau har ita ake yi wa iƙirarin harbewa da ita da rana tsaka. Tana son tambayarsa inda zai kaita amma tsoro ya hanata, tana cikin tunani ta ji ya sake fisgar motar da wani irin matsanancin gudu, ai kuwa ta ƙwalla uwar ƙara tare ta ƙanƙame jikin kujera.
A wannan yanayin suka ƙarasa gidan Mahaifinsa da ke unguwar Na’ibawa. Yana zuwa ya ciro mukulli ya buɗe gate ɗin gidan ya shiga da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fisgi hannun Dubu, ai kuwa tana ganin zai shiga gidan da ita ta riƙe ƙofar gate ɗin gidan da sauri tana cewa.
“Wallahi ni ba ƴar iska ba ce da za ka kawo ni gidan nan.” Maganarta ba ƙaramin dariya ta so bashi amma ya sake tamke fuska ya ce, “Ni ko ɗan iska ne an gaya miki zan yi iskanci da kucaka irinki?” Yana gama maganar ya sake fisgar hannunta aikuwa ta rungume wani ƙarfe tana cewa, “Kwarankwatsa dubu ba zan shiga ba, dama Inna ta ce ƴan iska ne suke bin maza.” Tsugunnawa ya yi cikin ɓacin rai zai yi mata magana, ita kuwa Dubu tuni ta shagala da ƙarewa fuskarsa kallo don tun bayan fitowarsu ta lura da abin da yake jikinsa. Ai sai tsoro ya sake kamata saboda bata taɓa zaton haka garin masarar ya yi masara furfurar da bai shirya ba. Ta maza ya yi ya tsugunna a gabanta don wani tsami ne yake bugar hancinsa, saboda tun da aka yi rasuwa Dubu bata ƙara saka ruwa a jikinta ba. Dama wankanma sai Yaya babba ta yi da gaske take yi to rurumar jama’a ya sa ta basar ta ci gaba da harkokinta. Zaro bindigar aljihunsa ya yi ya ɗora mata akan goshinta nan take kuwa ƙirjin Dubu ya fara bugawa da ƙarfi, da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta shiga Dubu ta soma hawaye tana cewa, “Don Allah ka yi haƙuri idan saboda na zuba maka garin masara ne. Wallahi ban kana kusa ba.”
Idan ka ji yanda Dubu take magana a ladabce za ka rantse da Allah mutuniyar kirki ce. Iya nadama Dubu ta shige ta don ta gama tsorata gabaɗaya, amma duk da haka bata jin za ta bi Aseem cikin gidan saboda ba za ta taɓa manta Baraka da ta yi ciki ba aka riƙa tsangwamarta ƙarshe sai sayar da gidansu Mahaifinta ya yi suka bar garin. Ita kuwa idan ta yi ciki ai ta san ko sama da ƙasa za ta haɗe babu wanda zai yarda a sayar da gidan Mai carbi.
“Idan kika bari na ƙirga uku ba ki tashi ba zan baki mamaki.” Maganar Aseem ta farkar da ita daga dogon tunanin da ta tafi. Cikin hawaye Dubu ta ce, “Don Allah me za ka yi mini a ciki.”
Banza ya yi mata yana buga bakin bindigar a ƙasa a hankali cikin sigar, idan baki tashi ba kin san sauran. Dubu bata yi ƙasa a gwiwa ba ta sake tambayarsa. Bai ɗago ya kalle ta ba ya ce, “Idan kin shiga kya gani.”
“Wallahi ko me ka ce zan yi amma ni ba ƴar iska bace.” Dubu ta faɗa lokacin da gumi da hawaye ya gama mamaye ilahirin fuskarta zuwa wuyanta.
“Ni ɗan iska ne.” Ya bata amsa yana miƙewa a fusace ya fisgi hannun Dubu tana ihu tana fisge-fisge ya wuce da ita ciki. Yana shiga ya datse ƙofar ya wurgar da ita gefe sannan ya faɗa wani ɗaki da ke ɓarin hagu. Dukda gidan ba baƙon Dubu ba ne amma a wannan ranar gabaɗaya bata da nutsuwa. Bai jima da shiga ba ta ga ya fito da wani abu a hannunsa na dama, ɗayan hannun hagun kuma wata ƴar ƙaramar wuƙa ce, ai kuwa ta zabura kamar wacce aka ɗanawa wuta za ta gudu. Fuska a murtuke ya fisgi hannunta ya wuce da ita cikin banɗaki. A wannan karon Dubu duka ta fara kai masa tana cewa.
“Jama’a ku taimaka min zai yanka ni. Kuma ka rabu da ni na ce maka ni ba ƴar iska bace. Wallah idan ka kashe ni na rataya a wuyanka duk zunuban su Inna Furai dana ɗauka kai za a ɗorawa.” Suna shiga ya sa hannu ya bige bakinta har sai da ya fashe ai kuwa Dubu ta fashe da wani marayan kuka bai bi ta kanta ba ya sa kilifar aski ya ɗora mata akan gaban goshinta. A zabure ta matsa baya ta ce, “Aski za ka yi…” Idanun da ya zuba mata ne ya sa ta haɗiye maganar ba tare da ta ƙarasa faɗa ba. Ta ci gaba da hawayen baƙinciki da nadama.
“Idan kika sake yi mini magana sai na yanke harshenki da wuƙar nan.” Dubu na ji na gani haka Aseem ya sauke mata sumar kanta ban da hawaye babu abin da take yi. Kafin wani lokaci sai ga kan Dubu ya fito ral da shi babu gashi. yana gamawa ya nuna ta wuƙa hannunsa ya ce:
“Wannan da kika gani somin taɓi ne amma matuƙar kika sake shiga hannuna sai na yi miki zanen gobirawa da wuƙar nan a fuskarki.” Ganin wuƙar na sheƙi ba ƙaramin razana Dubu ta yi ba, kuma a yanda ta ga babu ɗigon tausayi a fuskarsa ta san zai iya aikatawa don haka ta hau gyaɗa kai hawaye na zuba. Hannunta ya fisga zuwa falo ya sata tuƙin mashin. Dubu tun tana ganin kamar da wasa yake har ta tabbatar da yau sai ya kusa halakata a cikin gidan. Tana ganin ya ciro belt ta shiga taitayinta. Kuka take wiwi saboda yanda ƙafafuwanta suka ƙage, gashi ko nan da cen Aseem ya ƙi matsawa bare ta samu ta zauna ta huta. Tana zama kuma yake lafta mata belt ba shiri za ta sake miƙewa ta tashi tana soshe-soshe.
Sai da ya ga Dubu ta yi lugub sannan ya miƙe ya faɗa banɗaki ya yi wanka.
A wurin Dubu ta zube tana sauke numfashi da ƙyar, ta jera masa Allah ya isa ya fi a ƙirga. Kamshin da ya game hancinta ne ya ankarar da ita dawowar da Aseem ya yi. Ya yi kyau sosai cikin ƙananan kaya, haushinsa ne ya sake mamaye zuciyar Dubu don bata taɓa yadda da faɗar da ake yi akan sojoji mugaye ba ne sai a wannan lokacin. Kan kujera ya zauna sannan ya kirata, da sauri ta ƙarasa wurin ƙafarsa ta zauna. Danne-danne ya fara yi har sai da Dubu ta gaji da zaman sanna ya kalle ta ya ce, “Har yanzu kina nan da rashin kunyarki ko? Inno ta ɓata ki kina shuka tsiyar da kika ga dama. Wallahi daga yau na sake ji ko ganin kin aikata wani abin na rashin ɗa’a gaba hannu da ƙafafuwanki zan yanyanke miki, wannan bakin naki sai na datse shi na ga ta ƙaryar iskanci.” Kamar ƙosashen ƙadangare haka Dubu ta riƙa gyaɗa kai tana hawaye. Yana gama maganar ya fisgi hannunta suka fice daga cikin gidan.
Yaya babba na ganin irin marin da Aseem ya yi wa Duba ta zuba salati haɗe da dafa ƙirji, don har jin saukar marin sai da ta ji wani iri a jikinta. Tana ganin fitarsa ai kuwa ta zauna daɓar a wurin ta fashe da wani irin kuka. Hajiya Nafisa ci kanki ba ta ce mata ba, sai ma jin zuciyarta da ta yi ta mata fes saboda ta san tun da ta tabo Aseem ba za ta ji da daɗi ba. Saboda ko su Nabila baya musu ta daɗi bare Dubu da kowa ya shaida fitinarta. Yaya Babba wayarta ta zaro ta miƙawa Hadiza tana faɗin.
“Maza kira mini Garba idan shi ya ɗaure wa wannan fitsararren yaron yake shuka rashin matumci, har ina kiransa yana ji na sai ya mini bayani. Wallahi ba Soja ba yau ko Barek ɗin ce da kansa sai an yi mini iyaka da shi.” Hadiza jiki a sanyaye kamar kazar da aka tsamo daga ruwa ta karɓi wayar ta fara lalubo lambar, amma a ƙasan zuciyarta tana ayyanawa irin rikicikin da za a kwasa a cikin gidan.