BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Baba Abubakar suna hanyar dawowa gida daga asibitin da Inna Furai take kwance har an bata sallama, da yake dama likitocin sun ce damuwa da fargaba ne ya jefa ta a halin da take ciki. Bai yi aune ba ya ji kiran waya. Hadiza na jin an ɗauki wayar ta miƙawa Yaya babba, shi kansa Baba Abubakar tun da ya ga kiran mahaifiyarsu ya ayyana dole akwai abin da yake faruwa. Ɗaukan wayar ya yi da sallama jiki babu ƙwari, Yaya babba ko amsa sallamar sa ba tayi ba ta ce, “Garba! Garba!! Garba!!!” Gabansa na faɗuwa ya amsa sannan Yaya Babba ta ci gaba da cewa, “Sau nawa na kira ka?” Ya amsa mata.

“Sau uku Inno”

“Wallahi tun ban kwashe wa ɗanka falsafar albarka ba ka zo gidan nan yanzu-yanzu” Kansa ɗaurewa ya yi don shi ya manta ma da sun yi magana da Aseem akan zai zo gaisuwa saboda haka ya cewa Yaya babba.

“Inno wa kenan?”

Yaya Babba ta fashe da kuka tana cewa, “Karka zo ka bari idan ya kashe mini jika shi kenan.”tana gama maganar ta katse kiran. Da sauri Baba Abubakar ya danna wayar Aseem sai dai ya ji ta akashe don lokacin tuni ya kashe ta saboda ya san dama tabbas za a neme shi.

Wayar Hajiya Nafisa ya kira tana ɗauka ya shiga jero mata tambayoyi, tana jin haka ta saci kallon Yaya babba da ta cika fam sannan ta bashi amsa da, “Ka san dai yarinyar nan Dubu ba kunya gare ta ba, daga zuwan Aseem ta sheƙa masa garin masara. Dama kuma ta cikumi Nabila tun da ta rainata kamar takalmin ƙafarta. Sauran maganar dai sai ka zo.” Yana tafe a mota amma gani yake kamar tafiyar bata sauri don ya san lamari ya gama kwaɓewa gabaɗaya amma gyarawa sai Allah.

Yana zuwa ya samu Yaya babba a zaune ban da hawaye babu abin da take yi, a gefenta ya tsugunna ya ce, “Ga ni Inno.”

“Garba ka raba ni da wancen mai busasshiyar zuciyar. Wallahi ni an cuce ni da aka tura mini jika aikin soja, dama tun tuni na ce bana son wannan aikin saboda cire musu imani ake yi amma aka ƙi yanzu ga irinta nan. Yaro ya koma kamar basamude haka ya riƙa kifawa yarinyar mari babu tausayi barr imani. Wallahi idan ya kashe mini jika ba zan yarda ba shari’a sai ta kaimu har kotun ƙoli.” Sai ta kuma rushe wa da kuka tana ci gaba da cewa, “Saboda Allah me Dubu ta tsare masa da zai riƙa zabga mata mari kamar Allah ya aiko shi. Kana ganin wannan shirgegiyar matar ta min tsaye a ka, ko ta tsawatar masa wa ya sani ba ko ita ta saka shi don na lura ba ƙaunar Dubulliyata take ba. Kaico yanzu yarinyar ko a wane hali take oho.” Yaya Babba ta sake rushewa da kukan da ya fi na farko taɓa zuciya.Nan take aka yi wa Baba Abubakar bayanin abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Da ƙyar ya samu ya lallaɓi Yaya babba ta rage faɗan sai dai bakinta ya kasa yin shiru.

Bayan wani lokaci suna nan zaune Aseem da Dubu suka shiga cikin gidan, fuskar Dubu duk ta yi zurur-zuru tana tafe tana gwale ƙafafuwa. Gabaɗaya mutanen wurin binta suka yi da kallo, Baba Abubakar rai a matuƙar ɓace ya tari Aseem da kyakkywan mari. Dubu kuwa na ganin haka ta sake ɗangalewa ta rushe da kuka ta faɗa kan Yaya Babba.

Da sauri Yaya babba ta matsa baya tana zaro ido ta ce, “Dubu me nake gani kamar aski akanki.” Dubu ta rushe da kuka ta ce, “Inno wallahi aski ya mini kuma wallahi ɗan iska ne.” Cak Yaya Babba ta tana ƙarewa Dubu kallo sannan ta ce, “Dubu je ki can mu gani.” Dubu ta tashi tana ƙobare ƙafafuwa saboda irin gwale-gwalen da ta sha.

Ba su yi aune ba sai ga ni suka yi Yaya babba ta faɗa ɗaki ta rushe da kuka. Da sauri suka bi bayanta saboda kusan kowa bai ji daɗin abin da Aseem ya yi ba musamman Mahaifinsa, faɗa yake yi masa sosai sannan suka shiga ɗakin. Yaya babba kallonsu ta yi fuska a murtuke ta ce, “Garba ka tara mini ƴan uwanka saboda wannan ba maganar tsaye ba ce. Kuma idan har Aseem ya farke mini Dubu na rantse da Allah ba ita kaɗai ya yi wa illa ba, ya fi kowa shiga uku domin babu makarin maganin ƴan shafi mu lerar da za a bashi. Kai ni wallahi ban lamince ba ke Nafisa ke ce uwarsa wuce ki je ji bincike shi tas, don wallahi Idi ɗan wanzan ya mutu babu wani magani da zai karya laƙanin aikin, saboda aikin har da haɗin ƴan shafi mu lera.” Tana gama maganar ta fisgo Dubu tana shafa mata suɗaɗɗen kanta ta ci gaba da cewa, “Ka ga yanda Kan Dubu ya sulle kamar bayan sulba. To kwarankatsa dubu idan har ka farketa kaima haka wurin zai shafe kamar bayan silba.”

Kallon-kallon aka fara yi da juna, jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi dukda ta san a tarbiyyar da suka bawa Aseem ba zai taɓa yi wa Dubu fyaɗe ba. Amma shaidar ɗan yau bata da tabbas, domin ɗa ne ka haifshe baka haifi halinsa ba. Babban abin da ya fi ɗaga hankalinta da ta ji an ce Aseem ɗin ta ya koma kamar bayan silba. Ita da take yi masa tanadin Yusra ƴar aminiyarta ya aura.

Baba Abubkar ya kalli Aseem da kallon tuhuma rai a ɓace, Aseem ya sunkuyar da kai ƙasa saboda ba ƙaramin takaici kakar tashi ta bashi ba. Da wata irin murya Baba Abubakar ya ce, “Abin da Inno ta faɗa haka ne?”

Aseem ya furzar da iska mai huci ya ce, “Daddy don Allah ka bar biyewa maganar tsohuwar nan ka san dai wasu maganganun nata ba su…” Bai ƙarasa ba Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, “Ka iya bakinka Aseem duk yanda Mahaifiyarmu take furta lafazi Mahaifiyarmu ce.”

Yaya Babba ta wara hannuwa ta ce, “Kuma na fi wannan gajeriyar uwar tashi mai kama da gajeren turmi, na gama maka komai tun da na haifo uban da ya haifeka. Atoh gara ka yi bayani wallahi babu inda zani in wahalar da kaina wurin neman maganin gargajiya. Alƙur’an dama sai da Idi wanzan ya gaya mini ɓat haka za a nemi komai a rasa. Wa ya sani ma ko aljanunsa ne za su ɗauke su cinye su barka a shafe.

Ummou Aslam Bint Adam????
[7/1, 5:59 PM] My Data sim number: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 7
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan???????????????????????????????????????? subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Waɗannan kalamai na Yaya Babba ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Hajiya Nafisa suka yi ba, ciki a kaɗe hankali a tashe ta dubi Yaya babba da babu abin da take yi ban da huci ta ce, "Inno ba mu fahimce ki ba. Shi Aseem ɗin za a mayar kamar bayan silba?" 

“Ke Nafisa ki fita daga idona, dama ban faɗa don ku fahimce ni ba ehe. Hadiza meye laifina don na nemawa marainiyar jikata maganin tsari?” Hadiza ta girgiza tana faɗin, “Babu laifi Inno!” Yaya babba ta ci gaba da cewa:

“Allah ya jiƙan Idi ɗan wanzam ya gafarta masa shi ya bani laƙani na yi wa yarinyar nan Dubu, akan duk wanda ya farketa to shi da sake zama namiji har abada kenan.” Hajiya Nafisa ji ta yi ƙafafuwanta sun yi sanyi har tsayuwar na neman gagararta. Don haka ta jingina ta bango tana bin Aseem da wani irin marayan kallo.

Kafin wani lokaci gabaɗaya iyalan gidan sun hallara a ɗakin Yaya babba dama kuma gidan babu kowa sai iya su ƴan gidan, don haka suka hallara kowa zuciyarsa babu daɗi. Yaya babba ta fara bin su ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara cewa, “Na san dai kun san dalilin tattara ku da na yi a wurin nan. A zahirin gaskiya Soja ya keta mini rigar mutumci, saboda Allah wane mugun abin yarinyar nan ta yi wa yaron nan da zai aikata mata wannan mugun halin…” Kuka ya ci ƙarfin Yaya babba saboda zuciyarta ɗaya ta ɗauka Aseem wani abu ya yi wa Dubu da ta tafiyarta ta sauya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button