BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Baba Adamu ya yi sallama sannan ya fara fa cewa, “Inno don Allah ki yi haƙuri. Amma kafin a yanke wani hukunci ya kamata a ji ta bakin yaron nan bana jin Aseem zai aikata abin da ake magana akai…” Yaya Babba ta yi farat ta katse Baba Adamu da cewar, “Ado ƙarya na yi kenan? Ku tashi ku fice daga gabana idan ba so kuke na yaye falsafar albarkar da ke kanku ba.” Baba Adamu ya yi ƙasa da murya ya ce, “Inno don Allah ki yi haƙuri ba haka nake nufi amma duk yanda kika ce haka za a yi.”

“Ke Dubu me soja ya yi miki bayan ya tafi da ke.” Dubu da har lokacin da sauran tsoron Aseem a zuciyarta ta saci kallonsa aikuwa suna haɗa ido ya watsa mata mugun kallon. Sai a kan idon Yaya babba ta ga irin kallon da Aseem ya yi wa Dubu, ai kuwa wani irin gumi ne ya fara yayyafowa Dubu ta fara inda-inda. Yaya babba ta fara salati tana tafa hannuwa ta kalli Aseem ta ce, “Ittaƙillah Soja ka ji tsoron rabbissamawati, idan ka zare mata ido a nan duniya a cikin kabari za ka zare wa Mala’iku ido ne. An ya Soja haka ka koma ban sani ba?” Ta mayar da kallonta wurin Dubu ta ce, “Za ki yi wa mutane bayani ko sai na sa Munkaila ya zane miki jiki ciki da bai.” Dubu ta muskuta gefe ta fara cewa, “Da ya kaini mota bindiga ya ciro wai zai harbe ni ya wurgar da gawata a gefen hanya.” Da sauri Yaya Babba ta dafe ƙirji ta ce, “Kun ji ko? Na gaya muku tuni ya riga da gama da ita.” Hajiya Nafisa saboda ɓacin rai ji ta yi kamar ta shaƙo Dubu da Yaya Babba ta shaƙe su. Dubu ta ci gaba da cewa, “Muna zuwa gidan ya yi mini aski kuma wai da har billen gobirawa zai yi mini. Daga nan ya sani tuƙin babur shi ne muka taho gida.” Yaya babba jikinta ne ya fara sanyi ta ce, “Daga haka bai yi miki komai ba?” Dubu ta ce, “Eh”

A ɗan ƙufule Yaya babba ta ce, “To da kika ce ɗan iska ne?”

Dubu ta ɓata fuska ta ce, “Eh mana ba ke kika ce mini duk mace mai bin namiji, ita da shi duka ƴan iska bane?” Wata gwauruwar ajiyar zuciya Hajiya Nafisa ta sauke, Yaya babba cikin jin haushi ta ce, “Amma Allah wadaran halinki Dubu da za ki iskanta mini jika, ina ji ina gani a gaban iyayensa. Kedai an yi makira yanzu ba sai ki sa Garba ya ce ba na son Ɗansa ba. Ni dai kin cuceni za ki haddasa gaba a tsakanina da ƴaƴana. Tashi ki bani wuri makira in Allah ya yarda ba zan ga ɗan iska a kan jikana ba. Don Allah ku gaya mini abin da Soja ya tsare wa Dubu da za ta yi masa mugun fata haka?” Kowa ya yi shiru a ɗakin bai tanka mata ba. Yaya babba ta dubi Aseem da fuskarsa ta yi murtuk saboda ɓacin ra ta ce, “Soja ka gafarce ni wallahi wannan makirar ce ta ingiza ni, ni dama sai da zuciyata ta raya mini babu abin da za ka yi wa Dubu.” Ci kanki Aseem bai ce mata ba, sai kuma ta fara matsar ƙwalla ta ce,

“Garba kana gani Soja ya ƙullace ni har ya ɗau fushi da ni. A gidan duniya idan ban yi wa jikana magana ba wa zan yi wa? Kana gani hakkin Soja zai bar ni kwanciyar kabari?” Baba Abubakar ya ce, “Inno bai ƙullace ki ba ina jin bai jiki ba ne.” Ya faɗi haka ne don kar wutar rikicin Yaya babba ta ƙara tashi. Yaya babba ta saki murmushi tana goge hawaye ta ce, “Soja!” Ya ɗago ya dube ta har lokacin fuska babu walwala ya ce, “Na’am” ta ci gaba da cewa, ” Allah dai ya yi maka albarka. Wallahi ka biyani da ka askewa yarinyar nan kai.” Da sauri duk suka ɗago suna kallonta don ba su taɓa zaton haka daga bakinta ba.

Ta janyo Dubu tana sulle hijabin da ta ɗaura ta rufe kan da shi ta ce, “Wari dai akanta yanda ka san an buɗe shadda, idan Dubu ta buɗe kai a kusa da kai alƙur’an ko yawu ba za ka iya haɗiya ba. Kwanaki haka na saka mata fiya-fiya saboda kwarkwata amma yarinyar nan duk ta watsar a banza. Don Allah ka gaya mini wane saurayi ne zai ɗauki Dubu tana fama da tsamin kai dana hammata?” Hajiya Rahama ta yi murmushi ta ce, “Inno ai har yanzu Dubu yarinya ce tana ƙara zama budurwa duk za a nemi wannan ƙazantar a rasa.” Yaya babba ta taɓe baki ta ce, “Ke Rahama rabani da cewa Dubu yarinya. Yarinyar da tun bara ta fara jini, ki gaya mini ta zama budurwa ko bata zama ba? Ga Ma’awiyya ƙawarta nan tun kwanaki aka yi mata aure wai sai ga ciki, nace kai waɗannan ƴaƴa an yi jarababbu yanda kika san a bakin ƙofa suke cin karo da shi. Yarinyar nan haka ta riƙa kuka da zan kaita ɗakin miji da yake ƙud-da-ƙud muke da kakarta, ina ta zuba ido na ji an ce yarinya tana gudun miji tana dawowa gida, kamar yanda muka riƙa yi muna amare ba sai muka ji shiru ba. Hali ne dai a ƙoƙon rai Dubu ba za ta daina wannan halin ba, ban ƙi ba idan ta haɗu da miji ɗan gayu kamar Soja.” Ai kuwa Aseem na jin haka ya ɓata fuska bai gama tsinkewa da lamarin Yaya Babba ba sai ji ya yi ta ce, “Ai shi ma wannan shirun da yake yi ba banza ba wallahi, aure yake so don dai bai gaya muku bane. Ya yi gadon Kakansa Malam, don haka ya bani labari shi ma yana matashi Allah ya jiƙan Malam babba shi ya fahimci aure yake so, ba a ɗau lokaci ba aka ɗaura mana aure. Shi ma Soja ana haɗa shi da ƴar budurwa kamar Dubu shiru za ku ji sai dai ku ji ciki.” Aseem a daƙile ya miƙe zai fita saboda takaici. Yaya babba ta bushe da dariya ta ce, “Kun ga abin da na gaya muku wai ya ji kunya na tona asirin zuciyarsa.” Baba Adamu ya yi murmushi ya ce, “Yanzu Inno magana ta wuce kenan kowa zai iya tafiya?”

Take ta murtuke fuska ta ce, “Sam ban sallame ku ba wallahi akwai muhimmiyar maganar da nake son yi da ku ko Dubu?” Ta faɗa tana kallon Dubu da ke cika tana batsewa.

Dubu ta gyaɗa kai don fushi take da Yaya babba saboda irin bankaɗar da Yaya babba ta yi mata a gaban mutane, Yaya babba ta gyara zama sannan ta fara cewa.

“Garba wata shawara na yanke don Allah ya sani an daɗe ana shiga haƙƙina.” Gabaɗaya suka kalleta suna mamakin jin kalamanta sai dai ba wanda ya tanka suna jiran jin ci gaban sauran maganar.

“Tun Malam yana raye nake son ganin kan iyalaina a haɗe ba wannan ya yi gabas, waccen kudu wani arewa ba.”

Hadiza ta jinjina kai sannan ta ce, “Maganarki hake ne Inno amma ai kanmu a haɗe yake don gabaɗayanmu babu mai bijirewa maganar na gaba da shi.” Yaya Babba ta washe baki ta ce, “Ai shi ya sa nake son na ƙara haɗa kanku idan na waiga na ga wannan inna juya na ga wannan ko ba haka ba Dubu?” Dubu ta yi murmushi don ta san muddin Yaya babba ta zartar da hukunci to ba fa ba shakka suma sun zama ƴan gayu irin yanda ƴaƴan Baba Adamu da Baba Abubakar suke rayuwa.

“To na zauna mun yi shawara ni da Dubu kuma ta bani shawara mai kyau akan haka.” Wannan kalamai na Yaya babba ya yi daidai da shigowar Aseem zai ɗauki mukullin motarsa. Yaya babba ta yi farat ta dakatar da shi da cewar, “Kai Soja tsaya ayi da kai ka ji alherin da zai same ku don wallahi ba ƙaramin gata zan yi muku ba. To ina dalili in kwanta inmutu zuri’a a tarwatse, a’a sam haka ba za ta faru ba dama abin da na riƙa nusar da kakanka kenan ya ƙi gane wa.” Aseem bai so zama ba don ya san ban da rikici babu abin da za ta yi musu a wurin. Amma gudun tashin hargitsinta ya sa ya koma ya zauna ba tare da ya tofa uffan ba.

“Yauwa magana muka yi ni da Dubu kuma wannan shawara da ta bani na yi na’am da ita. Na yanke hukunci kai Garba da ɗan uwanka Ado za ku dawo gidan nan da zaman. Kowa ya kwaso iyalansa ya kawo su ɓangarensa. Yo ina dalili ace da mahallinku a gidan gado kowa da ɓangarensa sai dai ace wai idan an kawo mana ziyara a sauka a ciki. A’a sam ba da ni za a yi haka ba Dubu ta ce sai mum fi cin daɗi kuma waye baya san daɗi a rayuwarsa Garba.” Ta ƙarasa maganar tana tambayar Baba Abubakar da ya yi suman zaune. Kasancewar ya tafi wani tunani can bai ma san irin tambayar da Mahaifiyar ta shi take yi masa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button