DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
“Duk wacce ta sake ta fito daga gidan nan wallahi-wallahi a bakin aurenta. Tun da kun riga da kun yanke hukunci shi kenan, rasuwa dai Mahaifina ne ya rasu bana buƙatarku kuma komawa Ɗangwauro kamar mun koma mun gama, duk wacce ta ga za ta koma bismilla wacce ta ga ba za ta iya ba za ta iya komawa gidansu. Ita ma waccen zan kira na shaida mata.” Yana gama maganar ya katse bai jira cewarta ba. Lokaci ɗaya ta ji duniya ta yi mata zafi don ita kanta ta san abin da suka yi ba su kyauta ba.
Gidan Baba Abubakar.
Hajiya Ikilima ce zaune cikin mamaki ta dubi Hajiya Nafisa ta ce, “Wai wannan maganar da kike gaya mini da gaske ne ko kuma zolayata kike yi?” Haushi ya fara kamata da jin kalaman aminiyar tata ta ce, “Ƙawas kin san bama irin wannan wasan da ke. Serious ki bani shawara Allah dana koma Ɗangwauro gara aure ɗna ya mutu da bawan Allahn nan.” Cikin zuciyar Hajiya Ikilima ƙyal saboda farinciki don ta jima tana hangen kanta a gidan wannan baƙin bafulantin mai cike da kwarjini, amma ina ƙawarta ta yi mata shamaki. Ta dube ta da fuskar tausayi ta ce, “Gaskiya dole ki ɗau mataki kika koma ƙauye wallahi kin faɗo, yanzu abin yi ki shirya na raka ki Ƙauyen tudun-wada akwai wani Malami yana taimako wallahi, zai taimaka miki sosai ke ko kashe tsohuwar nan kike son yi murus za a gama da ita.” Hajiya Nafisa ta zaro ido waje tana faɗin, “Kin san fa ni bana haɗa hanya da ƴan tsibbu shawarwarin da kika saba bani dai su za ki bani. A kashe ta, ta rataya a wuyana. Ba za a yi haka ba kedai…” Bata ƙarasa maganar ba Aseem ya shiga falon don sarai ya ji abin da suke tattaunawa, sai ya wuce kan daininga da kofin shayi a hannu yana danne-dannen waya. Hajiya Ikilima ta saci kallonsa cikin ƙasa da murya ta ce, “Ko dai ya ji mu?” Hajiya Nafisa ita ma kallonsa ta yi sai ta ƙanƙance murya ta ce, “An ya kuwa amma bari ki ga.” Hajiya Nafisa ta kalli Aseem ta ce, “Aseem jeka ɗakina ka ɗauko kuɗi akan mudubi ka tsallaka titi ka siyowa mamanka fura.” Babu yanda ya iya haka ya tashi ya tafi kamar zai yi kuka don ya so jin ƙarashen hirar tasu. Dama ya jima yana zargin wannan matar da zuga mahaifiyarsu ashe kuwa ita ɗin ce take zuga ta.
Yana fita Hajiya Ikilima ta ci gaba da ɗora Hajiya Nafisa akan shawarar banza. Sai dai abin da kullin yake ɓata mata rai duk yanda take son ɗora Aminiyar tata akan biye-biyen malamai taƙi bada kai bori ya hau, kuma da haka take son cimma ƙudurinta akanta amma bahaushe ya ce a juri zuwa rafi watan tulu zai fashe.
Bayan Sadakar Bakwai.
Dubu ce tafe za ta tafi makarantar Islamiyyar Malam Jafaru, tana tafe da ƴar maƙalaliyar jakarta ta buhu tana rera waƙar Bureka (Breaker) ta Jaruma, idan ka ji yanda take rairawa sai ka rantse ita ta biyawa mawaƙin waƙar. Ɗan’iya da ke tafe da Mahaifiyarsa ya ƙwala mata kira. “Dubu!”
Dubu ta juya hagu da dama sai a can daga nesa ta hango Ɗan’iya ai kuwa ta yashe baki, tana ɗaga masa hannu. Ɗan’iya sai da ya ga sun ɗan yi nisa da Dubu sannan ya ce, “Dubu mai kan Silba mun san komai ashe ƙwaryar molo aka yi miki.” Lawandi da taron abokansa da ke bakin bishiyar dalbejiya me za su yi idan ba dariya ba. Ma’azu har da tuntsirawa kamar zai faɗi ƙasa. Wannan abu ba ƙaramin ɓata ran Dubu ya yi ba, ta tattakura ta ɗaga murya da cewa, “Eh na ji ɗin Ɗan gidan Balaraɓe kwarton dare” Da sauri su Lawandi suka riƙe baki kasancewar dama ana ta raɗe-raɗin wannan zargin da ake wa Balarabe ashe har kunnen yara ya fara bazuwa.
Hansatu mahaifiyar Ɗan’iya ta nufo wurin Dubu a fusace tana zuwa ta ce, “Iskancin na ki yau akan mijina ya sauka? Dan uwarki za ki ƙara cewa mijina kwarto?” Bata rufe baki ba sai da ta zabgawa Dubu mari sannan ta ɗora da cewa, “Wallahi ba Balarabe ba ko Bala na sake ji a bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke. Na lura iskancinki ƙara yawa yake saboda baki da mafaɗi…” Dubu ta fisge hijabinta tana cewa, “Allah ya isa kuma wallahi bashi kika ɗauka. Na faɗa waye bai san Balaraɓe kwarto bane har ɗakin Baba Auwalu sai da ya taɓa leƙawa lokacin da Yahanasu tana amarya. Banza kina gida kina tare da ɗan iska…” Kukan kura Hansatu ta yi ta fisgo Dubu ta fara jibga kamar Allah ya aikota. Jin Hansatu na niyyar hallakata ya sa ta fara kiciniyar ramawa, ai kuwa Hansatu ta cukwikwiye Dubu a cikin hijabi ta riƙa dukanta ta ko’ina sai da ƙyar su Lawandi suka ƙwaci Dubu. Suna fisgarta sai ga hijabinta a hannun Hansatu nan fa kan Dubu ya fito ral da shi yana ƙyalli don ranar Yaya Babba ta sharɓane mata shi da man kaɗanya. Nan Ɗan’iya ya fara tafi yana cewa, “Yeeh Dubu mai kan Silba (Silver)” Ai kuwa kafin wani lokaci tuni yara suka taru ana kallo, dukda tsoron da suke yi wa Dubu amma ruruma ta ɗauke hankalinsu suka fara sowa da tafi suna cewa, “Yeeh Dubu mai kan silba.”
Idanun Dubu ne suka kaɗa jawur saboda baƙin ciki, sai dai har lokacin idanun Dubu a bushe suke babu ko ɗison hawaye don gudun kar a ga hawayenta yara su rainata. Cikin takaici ta kalli Hansatu ta ce, “Kwarankwatsa dubu bashi kika ɗauka kuma da ni kike zan cen.” Ta juya ta kalli sauran yaran da suke tsokanarta ta ce, “Ku kuma za mu gauraya da ku kowanne shege sai na sa an harbe Uwarsa.” Tana gama maganar ta suri jakarta da ke cen gefe ta fisgi hijabinta ta ɗora aka ta yi tafiyarta. Sai dai kusan rabin yaran jikinsu ya yi sanyi don suna tuno Yayan Dubu soja ne hantar cikinsu ta kaɗa har da masu bin ta suna bata haƙura amma babu wanda ta waiga, bare ya sa ran za ta amsa masa.
Dubu tun daga soron gidansu ta fara barke baki tana ihun kuka, amma ci kanki babu wanda ya tanka mata saboda sanin hali irin nata. Matan kawunan nata suna gani ta wuce cikin gida. Tana zuwa sashen su Yaya babba Inna Furai ta tare ta da tambaya, “To ƴar nema wa kika tsokano wanda ya fi ƙarfinki?” Dubu ta goge majina da hijabin hannunta sannan ta kuma yage baki tana ihu har sai da Yaya babba ta fito tana tambayarta.
“Inno wallahi daga yau ba zan ƙara fita waje ba. Ki dubi irin cin mutumcin da Hansatu ta yi mini ita da Ɗan’iya yau kashe ni ne kawai ba ta yi ba. Yara suka taru suna ce mini mai kan silba. Ni dai wallahi Allah ya isa da askin nan da azzalumin nan ya yi mini.” Dubu ta faɗa tana sake fashewa da kukan baƙinciki, don abin ba ƙaramin ciwo ya yi mata ba. Yaya Babba ta karɓe zan cen da cewar:
“Wallahi faɗi ki ƙara Dubu Allah ya iskan ki, don Allah me kika tsarewa Soja da zai sauke miki gashi ana zaune ƙalau? Hassada dai ka rasa wa za ka yi wa sai jininka. Na rantse da Allah ko uwarsa Nafisa ba za ta gwada miki gashi ba. Kanta da har gobe kamar hamtar ɗan isa ga uban sanƙo da almajiran ƙeya. Wallahi ni bansan abin da Garba ya gani a jikin gajeriyar matar nan ba ya aura, mace sai faɗin ran tsiya tana baje hanci kamar tattasai ya ji sanyi wuri.” Dubu ban da tuntsira dariya babu abin da take yi har da hawaye saboda ƙeta don tuni ta goge hawayen idonta saboda ko ba komai Yaya babba ta biya ta, da ba’ar da ta yi wa mahaifiyar Aseem.
Inna Furai da ke gefe ta sa dariya ta ce, “Yaya ai ba za ki ga baje hanci ba sai ta shiga gaban mota yanda kika san funkaso.” Sai kuwa suka sake kwashewa da dariya. Yaya Babba ta ce, “Furaira wai dama ranar da muka fita da Garba tana gaba kina ankare da ita?” Inna Furai ta ce, “Ina gani mana wai har ca take ka saya mana wani abin mana a danja wai ita mai miji.” Ai kuwa dubu me za ta yi idan ba dariya.