BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Yaya babba ta katse masa tunani da cewar, “Ka ga da Zulfa da Bintu duka Dubu fa ta girme musu.” Baba Abubakar ya gyaɗa kai ya ce, “Ai suma Yaya don kun matsa ne amma duka nawa yaran suke?”

Nan take Yaya babba ta ɓata fuska ta ce, “Yara dai Allah ya kawo musu mijin aure kar ka yi musu buƙulu, kai da ɗan’uwanka ba kun ɗorawa kanku bokon jaraba ba. To gaskiya bana son hassada Garba kuma na yanke shawarar haɗa Dubu da Soja don gaskiya ba za a zo ana yi mata gori ba tun da ƙawayenta kusan duka sun yi aure wasu ma sun haihu.”
DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 10
https://youtube.com/c/DuniyarHausaNovels

Ku dannan???????????????????????????????????????? subscribe tare da alamar kararrawa domin samun shirye-shirye da sauran littafai.

Baba Abubakar da Aseem lokaci guda suka ɗago suna kallon Yaya babba, da ta ci gaba da zayyano zance ko a jikinta. Dubu na maƙure a gefe sai raba idanu take don ita kanta ba ta san da wannan shawarar da Yaya babba ita da Inna Furai suka yanke ba. A madadin fushi sai ma wani murmushi da Aseem ya ke yi, wanda kana gani za ka tabbatar da murmushin mamaki ne da tsantsar baƙin ciki. Yaya babba da bata kawo komai a ranta ba ta ci gaba da cewa, “Allah ya sani dama wannan ne dalilin da ya sa na aika kiranka kai da Soja, don kune maganar ta shafa ba su Munkaila ba. Waye ya haifa maka Soja bayan kai da uwarsa Nafisa?” Yaya babba ta tambayi Baba Abubakar. Shiru ya yi yana murmushinsu na manya, sannan ya ɗago da kai ya ce,

“Inno na ji daɗin wannan maganar ta ki, kuma ni zan fi kowa farinciki da wannan haɗin domin abin da ya yi Dubu shi ya yi Aseem. Amma wani hanzari ba gudu ba…” Da sauri Yaya babba ta katse zancensa da cewar:

“Don Allah Garba ka faɗi alheri ko ka yi shiru. Wannan fa abin farinciki ne, kuma me ye aibun Dubu yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa. Ƙwaranƙwatsa dubu babu abin da Soja zai nunawa Dubu, kyau ya fita ko tsafta? Yarinyar da sai ta yi wanka sau uku a rana ko ba haka ba Furaira?” Inna Furai ta taɓe baki ta ce, “Ina dalili tun ba a ji ta bakin yara ba Garba za ka kawo mana hanzari, wannan kamar zazzage albarkar da ke cikin auren za ka yi. Gaskiya karka ɓata auren yara tun ba a je ko’ina ba, yoo Allah na tuba wane hanzari gare ka da ya wuce ka sa albarka?”

Baba Abubakar ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, “Inna ni fa baku fahimce ni ba. Ina nufin su yaran a fara ji ta bakinsu don kar ayi abu ba da son ransu ba. Amma idan kuna faɗin haka sai in ga kamar kuna nuna Dubu da Aseem ba ɗaya ba ne a wurina.” Yaya babba ta washe baki ta ce, “Shi dai Soja na san ai ba zai ƙi ƴar uwarsa ba, ita kuwa Dubu kar ku ji ta, na san ta yanda zan shawo kanta.” Aseem saboda takaici miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin, Yaya babba na ganin haka ta saki dariyar farinciki tana faɗin,

“Ai na gaya muku wannan shiru-shirun da yake yi wallahi aure yake so, ja’iri ga shi nan kunya ta kama shi ya fita yana sunne kai, yoo waye zai samu Dubu bai yi farinciki na? Alƙur’an ana auren ku basu wata tara sai dai ku ji haihuwa, Soja wai mu zai yi wa hikima bai san na daɗe da gano lagwansa ba.” Baba Abubakar ya yi shiru yana nazari domin ya san ba ƙaramin ruwa Yaya babba ta kunto masa ba, saboda ko makaho ya shafa fuskar Aseem ya san yana cikin yanayi marar daɗi. Saɓanin Dubu da ba za ka tantance ainihin halin da take ciki ba, na farinciki ne ko baƙinciki ba.

Yaya babba cikin murmushi ta kalli Baba Abubakar ta ce, “Yanzu dai Garba ka je ka shaidawa Nafisa halin da ake ciki don a fita haƙƙinta na mahaifiya, kar ta ji magana daga sama don ma bata da fushi ba kamar Fauziya Matar Ado ba, kai gaskiya Garba duk cikin ƴan uwanka akwai wanda ya yi dacen mace irinka kuwa? Allah ya sani Nafisa macen arziƙi ce idan na zageta sai dai na yi mata ƙazafi. Suma ƴan uwanka zan shaida musu abin da yake faruwa don kar su ji maganar aure bagatatan, na san Sule da baƙar zuciya sai ya ɗau fushi da ni ba gaira babu dalili. Yo ko auren na yi musu ban sanar musu ka ga laifina Garba? Kai ne dai uban soja halak malak, wani ne ya haifa mini kai? Ni ina na iya gaba halin ƴan wuta, ina masoyiyar Annabi (S.A.W) me zai haɗa ni da wuta ana zaune ƙalau? A’a rabani da wannan falsafar zan sanar da su da kaina, kar shaiɗan ya ɗebe ni idan suka ɗau gaba da ni na biye musu, ana zaune ƙalau na tsine musu su ɓalɓace.” Baba Abubakar ya zaro kuɗi a aljihu ya dire musu a gabansu ya yunƙura jiki ba ƙwari ya ce, “To shi kenan Inno Ni bari na wuce.” Cikin haɗin baki Yaya babba da Inna Furai suka fara faɗin, “Ka gaida gida Allah ya yi albarka.”

Yana fita Dubu ta ɓata fuska ta ce, “Wai ke Inno ce miki na yi ina son shi bayan mugu ne, baki ga irin wuyar da ya bani ba rannan.” Yaya Babba ta rungumo Dubu cikin lallashi ta ce, “Ke yi shirunki, kin san me ya sa na yi wannan haɗin?” Dubu zuciyarta ɗaya ta girgiza, Yaya babba ta ci gaba da cewa: “Allah ya sani Dubu idan ba mutuwa ba zan iya rabuwa da ke ba. Idan kika auri Soja a cikin gidan nan za ku zauna, ga wuri nan a gyara masa ku yi zamanku. Amma idan bare kika aura kin san dole ki fice daga gidan nan. Na san irin rayuwar da za ki yi a can gidan? Sam! Ba zan laminta ba a rabani da Marainiyar Allah ina ji ina gani.” Daɗi ne ya kama Dubu lokaci ɗaya ta washe baki cikin farinciki. Lokaci ɗaya kuma sai ta ɓata fuska ta ce,

“Inno idan ya harbe ni da bindiga fa? Wallahi ba shi da tausayi tsaf kashe ni zai yi.” Inna Furai ta hau jinjina kai sannan ta ce, “Wallahi har kotun ƙoli sai mun je a kan shari’ar nan. Ke bar zancen bindiga tsaf za ki saye zuciyar shi, tun da da me na birnin za su fiki?” Dubu ta ci gaba da washe baki tana jin nishaɗi ita a dole za ta auri Soja kuma ɗan gayu.

A ranar Yaya babba da Inna furai suka gama isar wa da Mutanen gidan, hukuncin da suka yanke har suke ɗorawa da cewar, yara tuni sun haɗa kawunansu don Aseem tsabar kunya tun da ya fito bai dawo ba. Ita kuma Dubu ban da murmushi babu abin da take yi, nan fa ƙananan maganganu suka fara tashi a cikin gidan kowa da abin da yake tsakura yana isarwa.

Lokacin da Baba Abubakar ya fita a cikin mota ya samu Aseem, yana zaune ya haɗa kai da sitiyari. Har Mahaifinsa ya shiga bai sani ba ya zurfafa cikin tunani. Da kallon tausayi ya dubi ɗan nasa ya ce,

“Aseem!” Jiki a sanyaye idanu jawuri ya ɗago ya kalli Mahaifinsa, murya a shaƙe ya ce, “Na’am Daddy.”

“Dukda ban shiga zuciyarka ba amma san wannan hukuncin ba lallai ya yi maka daɗi ba.” Kamar mai jira ya shagwaɓe murya yana faɗin, “Yanzu shi kenan Daddy duk abin da su Inno suka faɗa, komai ta ce sai dai ku hau ku zauna? Gaskiya ni kam babu yanda za a yi na auri waccen yarinyar. Yarinyar da kowa ya san bata da nutsuwa, don Allah Daddy ya za a yi ma na auri wata Dubu? Never wallahi.” Ya ƙarasa maganar a shagwaɓe kamar zai yi kuka. Baba Abubakar ya yi murmushinsu na manya ya ce, “Rashin nutsuwarta ba komai ba ne idan har kana sonta, kai namiji ne za ka iya nusar da ita akan abin da ya dace.” Cikin hanzari ya furta, “Ni ba na ma sonta, Allah ya sani ta nemi wani ta haɗa ta shi amma ba ni ba.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button