BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Da sauri Nasir ya yi baya haɗe da zaro ido waje, kamar wanda ya yi arangama da kumurcin maciji. Ya fara gyaɗa kai kamar kosasshen ƙadanfare sannan ya ce, “Lallai gumi ta yi gumi arniya da ambaton Allah. Aseem kai da kake hanani busawa yau kai ne kake neman kara ɗaya? Abokina bana fatan ka fara wannan harkar muma da muke busa sigarin Allah ya ye mana, meye labari.”

“Aure za a yi mini.”

Aseem ya faɗa murya na rawa kamar zai yi kuka. Nasir ya riƙe baki tare da bushewa da dariya ya ce, “Shegen kaya ka ce kakarka ta yanke saƙa, ɗan iska sanyin bana sai dai ka ji a bakinmu.”

Aseem ya sake tamke fuska ya ce, “Nasir don Allah fita ka bani wuri.” Nasir ya yi murmushi ya ce, “Tuba na ke abokina ya ake ciki?” Nan take Aseem ya zayyana masa duk abin da yake faruwa, kasancewar Nasir abokin Aseem ne tun kafin su shiga aikin Soja, kusan kowa ya san cikin ɗan’uwansa game da harkokin yau da kullin. Lokaci ɗaya Nasir ya buga tsalle ya ce, “Shi ne kake wani marairaicewa kamar mace, kai fa ba wayis ba ne. Wallahi irin ƴan shilolin nan sun fi saurin ɗaukan darasi sai ma ka yi…” Aseem ya katse shi da cewar, “Kai dama duk in da iskanci ya zo ya sameka shi kenan zai shafawa ransa salama.” Suna tsaka da magana Daddy ya kira shi ya sanar da shi maganar Mommy, ba a ɗauki lokaci ba Mommy ta kira shi, tashi ya yi tsam daga ɗakin zai fita, ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya yi ƙasa da murya ya ce, “Ka ga Ango ya kusa shan mai, a miƙa min gaisuwa idan an gama yayyafawa fure ruwa mai sanyi.” Aseem bai bi ta kansa ba ya fice daga ɗakin.

Kamar kazar da aka tsamo daga kogi haka Aseem ya dawo cikin ɗakin a sanyaye, kan katifa ya haye ya kwanta yana jin maganganun mahaifiyarsa na sake dawowa masa sababbi fil a cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa abokinsa Nasir ya fita ya bar shi domin ya fahimci abokin nasa na cikin wani yanayi.

Bahaushe ya ce, “Sanin hali ya fi sanin kama.” Tun bayan da kace-nace ya faru tsakanin Baba Abubakar da Hajiya Nafisa, washegari ya kwashi su Nabila a mota ko su bai sanar da su inda zai kaisu ba, sai da suka je ƙofar gidan Baba Adamu sannan ya kalle su fuska a tamke ya ce, “Ku shiga gidan Baffanku za su wuce da ku Ɗangwauro, duk wacce ta saɓa umarnina zan gauraya da ita.” Duk abin da yake faruwa Mommy ta sanar da su, don haka sun san duk halin da ake ciki. Sun san waye mahaifinsu domin mutum ne mai matuƙar haƙuri, amma idan ransa ya ɓaci kallon fuskarsa kaɗai zai sa ka shiga taitayinka. Ko kaɗan ba sa son komawa Ɗangwauro, amma babu fuskar da za su yi wa mahaifinsu musun maganar. Sai da ya ga shigar su da jimawa sannan ya tada mota ya bar ƙofar gidan, saboda tuni sun gama magana da ɗan’uwansa akan zuwan na su Nabila. Baba Abubakar da biyu ya yi wa Hajiya Nafisa haka, saboda ya san yanda take da matsanancin son yara ba za ta taɓa jurar ya rabata da su ba. Shi kansa yana son matarsa saboda wani hargitsi bai cika haɗa shi da ita ba, hasalima tun da suka yi aure ba su taɓa wani gagarumin tashin hankali kamar wannan ba. Ya santa sarai idan ya ce zai biyota ta lallami ba za ta taɓa komawa ba, amma idan ya biyo mata ta wannan sigar za ta fi ɗaukan abin da muhimmanci kuma za ta aminci cikin ruwan sanyi.

Tun a ranar ta kira Aminiyarta Hajiya Ikilima ta sanar da ita duk abin da yake faruwa, sam abin bai ɗaga mata hankali ba sai ma mamaki da tayi lokacin da ta ji Aseem ya amince da maganar auren. Abin da ya sa bata damu don bata da ƴa mace, saboda a koyaushe ta kalli Aseem rayawa take da tana da ƴa mace, da ko sama za ta faɗo sai ta yi duk yanda za ta yi Aseem ya aure ta. Rufaida ƴar yayarta ta so haɗata da shi, amma da ta ga Rufaida ta samu wanda ya fi Aseem kuɗi shi kenan ta watsar da maganar Aseem.
[7/2, 3:24 PM] Ameera Adam????: DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 12

Duk wata huɗuba mara amfani Hajiya Ikilima sai da ta ɗora Hajiya Nafisa a kai kala-kala, sai dai suna saƙa ta gaba ta baya na warwarewa domin a lokacin da suke tsaka da maganar tuni Baba Abubakar ya kwashi su Nabila ya fice da su daga gidan. Kuma ko da ya dawo bai bi ta kanta ba bare ma ta sa ran zai sanar da ita wurin da suke. Ganin bata ga wulgawar ɗaya daga cikinsu ba ya sa ta kira wayar Nabila tana kira bugu ɗaya ta ɗauka, baki na rawa Nabila ta ce:

“Mommy tun ɗazu nake yi miki filis kwal mi (Please call me) amma na ji ki shiru, ni kuma wayata babu kuɗi.” Mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ce, “Wallahi ban lura ba ina kuka shiga ne.” Nan take Nabila ta sanar mata da abin da ya faru, Mommy ban da surfa bala’i babu abin da take yi. Suna gama wayar ta nufi sashen Baba Abubakar fuuuu tana tafe tana surfa faɗa kamar za ta ari baki. Ko sallama bata yi ba ta doka ƙofar ɗakin tana faɗin, “Daddyn yara wai yaushe ka zama haka ban sani ba? Waye ya haifamin su Nabila da za ka kwashe mini su ka kaisu gidan su Fauziyya, na lura zaman lafiya ne baka so amma wallahi a wannan karon zan nuna maka ɓacin raina.” Sai da ta kammala ya juya ya kalle ta ya ce: “Na ji kin ce ba za ki koma Ɗangwauro ba shi ya sa na kwashe yarana na kaisu gidan ɗan’uwana, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne.” Taku biyu ya yi ya buɗe durowar kayansa ya zaro wata doguwar takarda ya ɗora mata akan gado yana faɗin, “Don haka na yanke wannan hukunci ina ganin zai fi zama masalaha, ki tattare kayanki wuri ɗaya saboda gobe zan turo a ƙarasa kwashe kayan gidan nan.” Yana gama maganar ya fara ɗaura agogon hannunsa, ya ci gaba da harkar gabansa kamar ma bai san da mutum a wurin ba.

Tuni jikin Hajiya Nafisa ya yi sanyi idanunta suka ciko da ƙwalla ta kasa ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Daddyn yara sakina ka yi saboda abin da bai taka kara ya karya ba?" Turare ya fesa a jiki sannan ya ɗauki wayoyinsa zai fita ta sha gabansa ta ci gaba da cewa, "Wallahi indai akan maganar auren Aseem ne bana ɗar ko dana-sanin hukuncin da ka yanke, tabbas na yadda Namiji ƙudan zuma ne (Littafin Maman Islam ne, ku neme shi don jin yanda labarinta yake mai tafe da ɗaukan darasi.) Na yarda duk yadda mace ta kai da shekaru a gidan aure, dole akwai shafin da namiji zai iya buɗe mata ba tare da inkiya ba. Na gode sosai da wannan son zuciya da kuka nuna min." Hawaye ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasa maganar bakinta.

Murmushi ya yi da jin kalamanta saboda ya san dama muddin ta yi tozali da takardar da ya ajiye mata abin da za ta kawo kenan, shi kuwa gani yake wane laifi za ta aikata masa wanda zai saka mata da hukuncin saki? Matar da ta aure shi tun yana malamin makarantar firamare har Allah ya ɗaga dajarasa ya zama babban malami a makaran jami’a. Yana tsaka da tunani ya ji ta ci gaba da cewa:

“Kai namiji ne ba lallai ka fahimci ɗacin abin da nake ji na mahaifiya ba, ace ina matsayin mahaifiyar Aseem a yi masa mata ba tare da sanina ba har sai bikin ya rage ƴan kwanaki. An ce za mu koma ƙauye rayuwar ƴaƴana za ta nakasta, duk wannan bai isa ba har sai da ka raba ni da ƴaƴana me ya sa ahalinku suka fiye san kansu ne?” Maganganunta sun taɓa shi sosai kuma tabbas kowacce mahaifiya ba za ta so abin da aka yi mata ba, amma hakan shi ne mafita tun da shima yana yi ne domin biyayya ga mahaifiyarsa. Tana shirin sake magana ya ɗaga mata hannu tare da cewa, “Maganar auren Aseem fatan alheri za ki yi masa, domin bakinki kamar yankan wuƙa yake idan kika aibanta auren ba Dubu kawai kika yi wa ba, bakinki zai iya faɗawa har kan zuri’ar da za su haifa.” Yana gama maganar ya fice daga ɗakin. Sai da ta zauna ta ci kuka ta godewa Allah sannan ta ɗauki takarda ta wuce ɗakinta, ta fara haɗa kaya sannan ta wuce unguwar Ɗorayi gidan mahaifiyarta.

Duk abin da ka ga bai zo ba sai dai idan ba a ƙayyade masa lokaci ba, ranar juma’a iyalan Yaya babba suka tarkato gabaɗaya suka koma sabon muhallinsu da ke cikin gidan Marigayi mai carbi. Hajiya Fauziyya ban da cika da batse babu abin da take yi, duk yanda ta kai ga biye-biyen malamanta akan komensu gidan abin ya faskara, sai dai ta ci alwashin sai ta gasawa Yaya babba aya a hannu cikin kisan mummuƙe ta yanda babu wanda zai gano ta. Hajiya Rahama dama macece mai sauƙin kai, tuni suka shirya da mijinta ta fauwalawa Allah lamuranta tare da neman alkairin komawar tasu. Sauran surukan cikin gidan murna a wurin abin baya musaltuwa saɓanin ƴaƴan Baba Abubakar da Baba Adamu da suke jin su kamar waɗanda suka koma rayuwar ƙunci. Yaya babba bakinta har kunne har wani annushuwa take ji da farinciki ganin kan zuri’ar Mai carbi ta haɗu wuri ɗaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button