DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
Wannan kenan!
Aseem ya shiga cikin matsananciyar damuwa, har wata ƴar rama ya yi sai dogon wuya, fuskarsa ta yi fayau. Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci rashin kwanciyar hankali ya samu matsuguni a jikinsa. Ko sati ba a rufa ba aka yi masa canjin aiki shi da Nasir, Nasir aka kai shi Kaduna shi kuma Aseem a ka kai shi garin Kano. Abin da ya daɗe yana so ne ya samu amma kuma wannan canjin aiki ya zo masa lokacin da baya buƙatar zamansa a kusa da gida. Amma babu yanda ya iya haka suka haɗa kayansa kowa ya koma wurin da aka yi posting ɗinsa.
Hajiya Nafisa tun da ta koma gida ta sanarwa da Mahaifiyarta abin da yake faruwa, da farko mahaifiyarta ta ji zafin Baba Abubakar amma daga baya ta riƙa nunawa ƴarta kuskurenta amma da yake idonta ya rufe, sai dai ta bi da Mahaifiyarta ta yanda take yi mata faɗa. Ƙanin mahaifiyarta Malam Mudam ne ya je gidan ake sanar masa da abin da ya faru, shi kansa ya ji haushin abin da ya faru don haka ya dubi Hajiya Nafisa ya ce, “Ke Nafisa saki nawa ya yi miki? Idan da kome zan nemi Abubakar ɗin mu yi magana. Ita rayuwa ai ƴar haƙuri ce, tun da ƙuruciya ba a yi wannan shashancin ba sai yanzu da girma ya zo.” Hajiya Nafisa ta ɓata fuska ta ce, “Kawu ka barshi kawai ai sai ya ga kamar gajiya na yi da zaman nan ɗin.” Daƙuwa ya yi mata da hannu ya ce, “Wannan sakarcin banza ne ai, duk abinki ke da Abubakar kun zama ɗaya.” Hajiya Nafisa ta ce, “Ai ni tun da na sa takardar da ya bani a jaka ban ƙara bi ta kanta ba, tun da haka ya ga ya fi ai shi kenan.” Ba don ta so ba haka ƙanin mahaifiyar tata ya tilas mata ɗauko takardar, tana buɗewa kunyar duniya ta isheta. Babbar takarda ce sai kuma ƙanana guda biyu da basu kai ta farkon girma ba, sai kuma cheque ɗin kuɗi a tsakiya. Takardar farko rubutu ya yi mata kamar haka:
“A kodayaushe ina gaya miki girma ya riga da ya kama mu, tsayawa kace-nace bai da amfani. A lokuta da dama abin da muke ƙi shi ne mafi alheri a gare mu, don haka Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Kada a tsananta soyayya kuma kada a tsananta ƙiyayya.” Bakin uwa na da matuƙar tasiri akan ƴaƴanta don haka ki yi wa Aseem fatan alheri, shi ne abin da ya fi alheri. Ni Abubakar ina ƙaunarki fiye da tunanin mai tunani, don haka idan na sake jin kalmar rabuwa a bakinki sai na hukuntaki da hukunci mai tsanani.” Takarda ta biyu kuma gabaɗaya kalaman soyayya ne dattijon mijin nata ya cika mata da su, sai cheque ɗin kuɗi masu yawa da ya bata ya ce ta riƙe saboda sha’anin biki.
Lokacin da ta karanta wata irin soyayyar mijinta ta ji na ratsata, nan take ta sanarwa da Kawunta abin da yake faruwa. A take a wurin ya ɗaga waya ya kira Baba Abubakar ya sanar masa da abin da Hajiya Nafisa ta yi tare da sheda masa ya zo ya ɗauki matarsa a ranar nan take.
Bayan tariyarsu da kwana biyu Yaya Babba ta nemi ganin iyalan gidan gabaɗaya a sashenta ita da Inna Furai, kusan gabaɗaya iyalan gidan sun hallara, sai ƴan tsirarun da suke aiki a nesa da gida irinsu Aseem, da waɗanda suke fita fatauci garuruwa. A ƙalla iyalan da suke zaune a tsakar gudan sun haurewa mutum tamanin, kowanne yana zaune da matansa da ƴaƴansa sai Yaya babba da Inna furai da suke zaune akan wani dogon benci. Sanye suke da tamfarsu iri ɗaya tare da hijabinsu ruwan toka iri ɗaya kamar yanda suka suba tun farkon rayuwarsu a gidan marigayi.
Bayan buɗe taro da addu’a Inna furai ta fara da cewa, “Da farko za mu ce Allah ya jiƙan malam ya haskaka kabarinsa.” Yaya babba ta saci kallonta a ɗan ƙufule don bata so ta yi mata katsalandam ba, gabaɗaya mutanen wurin suka amsa da, “Amin ya rabbi.” Inna Furai da bata lura da irin kallon da Yaya babba take yi mata ba ta ci gaba da cewa, “Mun tara ku ne domin mu ƙara jan kunnenku domin gabaɗayanku babu yara a ciki, don haka babu wanda zai kawo mana zazzagar rashin ɗa’a a wurin nan.”
Dubu da ke gefe ta yi karaf ta ce, “Inna yanzu Ma’azu da ake yi wa shayi shi ma ba yaro bane? Kin ga su Iro fa.” Ta ƙarasa maganar tana nuna Iro da yake kan cinyar mahaifiyarsa yana shan mama. Ai kuwa kamar mai jira Hajiya Nafisa ta ce, “To zaƙin zaƙafere… Ke kaɗai ce mai bakin magana manya na magana za ki sa baki saboda rashin ɗa’a.” Baba Abubakar ya ɗago ya kalli Hajiya Nafisa amma sai ta kalli wani wurin daban don ta san haka za ta iya faruwa. Dubu ta watsawa Hajiya Nafisa harara tana mata fari haɗe da murguɗa baki, Hajiya Nafisa ta cije baki cike da takaici. Dama a ƙule take saboda kiran da Yaya babba ta yi mata ba don san ranta ta je shi ba saboda ko kaɗan ba ta san haɗa inuwa da sauran facalolinta don gani take ba ƙaramin zubewar mutumci ba ne a wurinta. Matan Baba Abubakar ma don ta san babu abin da nata mijin ya fi na su shi ya sa bata cika kawo musu wargi ba.
Baba Abubakar ne ya yi magana hayaniyar da ke tashi ƙasa-ƙasa a wurin ta lafa, amma kallon yanda Hajiya Nafisa take duban Dubu za ka tabbatar da babu ɗigon ƙaunar sirukar tata a zuciyarta.
Inna Furai cike da ƙwarin gwiwa ta ci gaba da cewa, “Fatan mu dai ku zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Allah ya sani bama son tashin hankali da gutsiri-tsoma, gabaɗaya tushe ɗaya kuke sai a ɗorar da zazzagar zaman lafiya. Amma duk wacce ta kawo mana wargi alƙur’an mai hana mu zazzage albarkar da ke kanta sai Allah ko ba haka ba Yaya.” Yaya babba murya can cikin ƙasan maƙoshi ta ce, “Wacce falsafa za ki tambaye ni Furaira? Meye nawa a ciki kuma bayan tun farko baki bani girma da darajata ba. Ƙwarakwatsa dubu ba don kar na baki kunya a gaban su Auwalu da Ado ba, babu abin da zai hana watsa miki falsafar rashin ɗa’a.” Yaya babba muryarta ta fara rawa alamar za ta yi kuka, ta dubi Inna Furai ta ci gaba da cewa, “Alƙur’an ban taɓa sanin za ki yi ɗiban karen mahaukaciya da wasiyyar Malam ba. kaico! Rayuwar duniya.” Inna Furai ta fara zuwa wuya don haka a ɗan hassale ta ce:
“Yanzu me ye ma ba ki yi mini ba, wacce irin albarka ce baki zazzage mini a tsakar ka ba.” Sai kuma ta juya musu baya tana faɗin, “Allah ya sani Yaya kin zazzage mini kwandon ɗiban albarka.” Yaya babba ta taɓe baki ta ce, “Ai kinsan dai ni ce babba a gidan, tun zuwanki gidan nan ni nake fara komai, amma ƙasa ta rufe idon Malam har kina neman kwara mini falsafar rashin mutumci.” Inna Furai ta kusa kaiwa bango, a fusace ta miƙe za ta bar wurin tuni su Baba Munkaila suka fara sa baki ta zauna.
Inna Furai ta harari gefen Yaya babba ta ce, “Dama duk daɗinka da kishiya sai ta yi maka zazzagar rashin mutumci. To ni dai nan gani nan bari, kujera ce dola a zauna a kaina.”
Wannan maganar ba ƙaramin ɓata ran Yaya babba ya yi, ai kuwa nan take ta fashe da kuka. Wurin shiru ya ɗauka ban da sautin kukan Yaya babba babu abin da yake tashi, Inna fura ta ɗauke kai gefe alamun ita ko a jikinta. Sai da Yaya babba ta yi mai isarta sannan ta fara leƙe-leƙe, daga can gefe ta hango Salisu, da ɗan yatsa ta nuna shi tana faɗin, “Salisu zo nan don girman Allah.” Salisu na jin haka ya fara noƙewa don fatansa bai wuce, Yaya babba karta kunyata shi a gaban iyaye da sirikansa ba. Jin ya yi shiru ya sa Baba Sule ya yi masa magana jiki ba ƙwari ya fita ya je gefen Yaya babba ya russuna ya ce,
“Gani Inno.”
Yaya babba ta ruƙo hannuna Salisu tana goge hawaye idonta, ta ce, “Allah shaida kaine shaidata Salisu, daga yau babu ni babu Furaira ko a lahira idan ta nuna ta sanni ban yafe ba.” Tana rufe baki mutane wurin kamar haɗin baki suka ɗauki salati lokaci ɗaya. Yaya babba ta hango Sha’aban Jikan Inna Furai na huɗu shi ma ta ƙwala masa kira, yana zuwa ta riƙe hannunsa ta ci gaba da cewa, “Sha’aban na fasa wakilta Salisu saboda sam bai da ɗa’a bashi da kunya, Kaine shaida ko a gaban Ubangiji ka za ka shede ni.” Salisu zuciyarsa fes har zai bar wurin Yaya babba ta fisgo ƙugunsa ta tana faɗin, “Dawo munafuki babu in da za ka dama da biyu na shirya zaman nan, saboda kai da yarinyar nan Zulfa. Amma dai Allah ya yi wa Soja albarka, yaron nan shi kaɗai yake da kawaici.” Yaya babba ta mayar da kallonta wurin mutanen da ke zaune kowa ya zuba idanu suna jiran abin da za ta faɗa.