DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
Daga haka iyayensu maza suka yi musu nasiha sannan Baba Adamu ya sa aka shigowa da kowanne ango ledar kajinsa da ledar drinks haka ya basu gabaɗaya. Daga nan suka fice sannan aka ɗauki amare aka kai su ɗakin mazajensu. Dubu sai da aka zo tafiya da ita ta sa kuka wai dole su tafi da Yaya babba, wannan kalamai na Dubu ya sake karya zuciyar Yaya babba da ƙyar aka lallaɓa Yaya babba ta yi shiru aka wuce da Dubu ɗakin mijinta Aseem.
Ɗakin Dubu ya yi kyau sosai Baba Abubakar shi ya yi mata kayan ɗaki irin na ƴan birni, kayanta ba a yi ƙarya ba daidai rayuwar rufin asiri. Ɗan gidan gwanin birgewa komai sabo sai ƙamshi yake, Dubu aka kai aka ƙara yi mata nasiha sannan suka fito aka bar daga Dubu sai ƙawayenta biyu A’ilo da Raliya. Su Nasir sune kan gaba wurin rako ango, Aseem na gaba Nasir da abokansu biyu na rufa masu baya. Suna shiga Dubu ta ɗago kai ta mayafi tana satar kallonsu, tana ganin sun haɗa ido da Aseem ta mayar da kai cikin mayafi tana ƙyalƙyalewa da dariya. Nasir na zuwa ya ce, “Amaryarmu ga ango mun kawo miki da fatan za ki riƙe mana shi amana, don so muke nan da rana iya yau mu ga wannan ramin wuyan nasa ya shige.” Aseem ya watsa masa kallo ya ce, “Nasir ranka zai ɓaci.” Bai rufe baki ba ya ji Dubu ta ce, “Ai wallahi ko sati ba za a rufa ba sai kun yi mamakinsa, don baka san Laminu mijin ƙawata Zuwai ba yadda ka ga Me lob (My love) haka yake amma yanzu ko tunbinsa aka ɗora ma ka ji…”
Tsawar da Aseem ya buga mata ne ya sa sauran maganarta maƙalewa, ya dubi Nasir fuska ba walwala ya ce, “Bar min gida dama ban gayyace ku ba.” Nasir na dariyar ƙeta ya ce.
“Ɗan iska ba sai ka nuna min ba matsayinmu ɗaya ba, ni ma kwanannan zan yi wuff da wata ka ga mun yi one-one.” Ya ƙrasa maganar yana dire ledar da suka yi wa Aseem siyayya na shiga ɗakin Amarya, suna fita ya kalli su A’ilo da suka yi zuru-zuru ya buga musu tsawa, tun bai rufe baki ba suka miƙe suka fita, sai da suka yi gware ya kai sau biyu sannan suka samu ƙofa suka fice da gudu.
Suna fita Dubu ta fige mayafinta haɗe da ɓata rai ta ce, “Wallahi ka kunyata ni akan me za ka korar mun ƙawaye ko ladan siyan baki ba a ba su ba…” Ba ta ƙarasa magana ba ya bige mata baki ba shiri ta ja baki ta yi shiru.
Drower ya buɗe ya ciro sabuwar doguwar rigarsa ya fita falo sannan ya faɗa toilet ɗin tsakar gida. Yana fita Dubu ta yi maza ta buɗe akwati ta sauya kaya cikin doguwar rigar bacci, kannan nata ranƙwal babu gashi a kai kuma babu abin da ta sa a kan. Ledar kazar ta fizgo ta buɗe ta fara ci tana shan youghort ban da lumshe ido babu abin da take yi. Tana nan zaune Aseem ya shigo ya same ta, ba ƙaramin mamaki ta bashi ba binta yake da kallo yana ƙarewa kayan jikinta kallo, mamakinsa ɗaya yadda Dubu take da wayewar ido wai har ta san ta sa wasu kayan bacci, zama ya yi a bakin gado yana watsa mata kallo cike da takaici.
Bai tsinke da lamarin Dubu ba sai gani ya yi ta turo masa cinyar kaza saitin bakinsa ta ce, “Me lob kazar masoya.” Ta ƙarasa maganar tana wani irin farfari da ido. Rasa abin yi ya yi yana juyawa ya fisgo wayar cazarsa da ya ajiye akan gado, Dubu na ganin haka ta yi tsalle ta fice daga ɗakin tana ihu, Aseem ya rufa mata baya ba su tsaya a ko’ina ba sai ɗakin Yaya babba.
Da gudu Dubu ta kwakume Yaya babba hannunta ɗaya ɗauke da kaza bakinta shane-shane da mai.
Yaya Babba ta rungume Dubu ta dubi Aseem tana faɗin, “Kayya Soja kai a komai sai ka nuna halin yahudawa da rashin imani. Dubu fa ƙaramar yarinya ce, a’a rabani da wannan falsafar yarinya ko kaza bata gama cinyewa ba kake niyyar afka mata.”
ME KUKE TUNANI ZAI KASANCE? YAYA ZA A BUGA RAYUWA TSAKANIN SOJA DA DUBU????? WAI SHIN TA DAINA SHAƘIYANCINTA BAYAN AUREN KO KUWA SABON SHAFI ZA TA BUƊE???????????????? DON ALLAH KU HANGO MIN RAYUWAR AUREN SOJA DA DUBU MU JI YA ZATA KWASHE.
MAZA HANZARTA???????? KI SIYA ƊARI BIYU BA YAWA????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️ NA TABBATA BA ZA KI JI KAICO BA, KI SIYA KI SHA NISHAƊI DA BAN DARIYA????????♀️????????????????
[7/9, 9:22 AM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
© AMEERA ADAM
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
FREE PAGE 1
Girma da nauyin cikin da ke jikinta kamar an kifa ƙwarya, bai hanata gudun da take yi na ceton rai ba. Gudu take zabgawa saboda miyagun hallitun da ta yi tozali da su, masu kawo mata farmaki da zimmar cafkar tsohon cikin da ya yi tsini tamkar zai fashe.
Zuwanta bakin wata bishiyar kuka mai duhun gaske ya bata damar tsugunnawa cikin haki, saboda ji take kamar bayanta zai ɓalle gida biyu saboda azaba, ajiyar zuciya take saukewa akai-akai kamar wacce ta shekara tana matsanancin gudu a tsakiyar rani. Dafe bayanta ta yi wani irin azabar ciwon baya da mara ya sarƙeta kamar ana tsaga marar tata da kaifaffiyar aska. Sannu a hankali ta waiga bayanta don ganin mummunar halittar da ke bibiyarta kamar yanda inuwar mutum take bibiyarsa. Kukan jarirai ne ya fara yi mata amsa kuwwa kamar saukar aradu a tsakiyar ka! Ta ko ina take jin sautin kukan na su kamar kunnuwanta za su tawatse.
Kuka haɗe da dariya ne suke ta shi a cikin dajin, zuwa can ta hango inuwar wata hallita na tunkaro ta, matsananciyar guguwa ce ke tashi bishiyoyi na kaɗawa da ƙarfa yanda kasan za su jijjigo daga jikin jijiyoyinsu.
Cikin wani irin gwamamman yare ta riski muryar inuwar tana cewa, “Sai kin halaka ke da abin da yake cikinki, kin zama halakakkiya keda tsiron da ke cikinki.” Ba ta yi aune ba ta fara jin abu na bin ƙafarta zuu! A daidai lokacin da ta ji wani irin nishi ya taso mata.
Durƙushewa ta yi a wurin tana murƙususu, nan take wani irin kukan Jarirai mai haɗe da kukan Jaki ya fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dajin tamkar zai tsage gida biyu. Sannu a hankali Jarirai suka fara rarrafowa suna zageta kamar ana zagaye wainar gero. Duk da halin da take ciki bai hanata yunƙurin tashi domin tseratar da rayuwarta ba, amma ina! Haihuwa ta tunkarota gadan-gadan nan take jaririn ya faɗo.
Sannu a hankali ya rinƙa bin duk wurin da jini ya zuba yana lasa shi da sauran ‘yan uwansa Jarirai, tamkar waɗanɗa suke da’irar ƙungiyar asiri. Raihan da ke durƙushe da sauri ta zabura kamar wacce aka ɗanawa ruwan dalma, tana yunƙurin tashi nan take mabiyiya ta faɗo. Kamar yanda Kura take ƙishirwar nama haka suka afkawa Mabiyyar kafin wani lokaci tuni suka gama da ita.
Kamar haɗin baki haka suka waiwayi wurin da take tsaye, tamkar 'ya'yan Birrai haka suka fara tsalle suna ɗane jikinta har Allah ya basu nasarar hawa jikinta. Lokaci ɗaya suka fara lasar jikinta, ihu take kurmawa kamar zautacciya amma babu ɗaya daga cikinsu da ya yi alamun dakatawa. Daga can ƙafarta ta hango Jaririn da ya fito daga jikinta yana bin jinin ƙafarta yana lasa. A haukace ta ƙwalla ƙara tana ambatar sunan Mahaifiyarta kamar wacce ake zare wa rai.
Firgigit ta farka daga bacci tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta ci gasar tseren gudu, jikinta rawa yake kamar mazari, ta haɗa gumi sharkaf kamar wacce take gaban maƙera.
“Barka da tashi ranki shi daɗe.” Ba ta yi aune ba ta ji kalaman Mama Uwani a tsakiyar kanta. Da sauri ta ɗago ta kalle ta har lokacin jikinta rawa yake, sai da ta jingina da bangon gadon ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya ta ce, “Yauwa Mama Uwani.”
“Kina buƙatar wani abu?”
Girgiza mata kai ta yi tana murza idanu, hamma ta yi haɗe da miƙa sannan ta dubi Mama Uwani tana faɗin, “Mama Uwani ki haɗa min Tea kafin na fito.” Cike da girmamawa Mama Uwani ya russuna tana faɗin, “An gama shalelen Uwani, gabanki gata bayanki gata. Duk abin da kika faɗa haka za a yi uwar ɗakina.” Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Raihan miƙewa ta yi tana ɗan waƙe-waƙenta sannan ta faɗa toilet don ɗaura alwalar sallar asuba. Sai dai rana ta buɗe sosai wacce take nuni da gari ya waye tangararan don ƙarfe tara har da kwata a lokacin.