DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
Tana fita Jabun Raihan ta miƙe tana kaiwa da kawowa don gabaɗaya zaman wurin ya gundureta, abin da ya sa ta bi umarnin Huzaifa don biyan tata buƙatar amma ba don haka ba babu yadda za a yi ta amince da rayuwa cikin siffar bil’adam.
Huzaifa bai tsaya ko’ina ba sai cikin wani ƙasurgumin daji mai ɗauke da jajayen furanni, da jajayen ƙoramu. Komai na wurin ja ne hatta ciyayin da suke wurin, sai waɗansu korayen kifaye da su kaɗai ne suka bambamta da jajayen abubuwan da ke wurin. Kan wani jan dutse ya kaita ya kwantar da ita nan take ya fara gyara mata jikinta, kafin wani lokaci tuni ya gyara mata jikinta ya ɗauko wani ƙaramin jariri da ke kwance cikin wata ƙorama mai ɗauke da siffar kunkuru, sai dai kansa ɗauke yake da kawuna huɗu kowanne da surarsa. Akwai kai mai siffar jaki, agwagwa, mage da mai siffar kifi, a kowanne kai akwai manya kahunhuna guda biyu, daga jelar hallitar ɗauke take da tafkeken kan maciji. Yana zuwa ya ɗora shi a gefenta sannan ya ɗaga hannunta ya tura shi ƙarƙashin jikinta kamar yadda uwa take rungume jaririnta. Nesa da su ya koma yana sakin murmushin farinciki a fili ya fara faɗin, “Na jima ina burin haka ban samu dama ba domin gudin abin da zai ɓata miki rai, sai dai a wannan karon dole na ɗau wannan matakin domin haka ne kaɗai sai tseratar da ke daga kaidin Mugaza, idan ba haka ba duk yadda za ta yi sai ta halaka min ku. Ni kuma ba zan juri rabuwa da ke ba wanda ya nemi raba ni da ku zan iya hallaka shi ko wanene, ko da kuwa Mahaifina ne Jingas.” Yana gama magana ya ɗaga dutsen da Raihan take kwance da jaririnta, naɗe su ya yi cikin wani kogon dutse sannan ya hura wani kogi da korayen kifayen nan suke ciki, nan take ruwan ya dare Huzaifa ya jefa su ciki ya sake hura ruwan ya haɗe gabaɗaya.
Mommy na daga falo ta fara jiyo muryar Goggo na ƙwala mata kira, da sauri ta nufi wurin da ta ji muryar Goggo tana zuwa ta yi turus ganin Goggo na rarrafe daga ita sai ɗan fatari. Da sauri ta sunkuya tana faɗin, “Goggo lafiya kuwa ko ƙafar ce ta motsa?” Tun bata rufe baki ba Goggo ta ci gaba da faɗin, “Abu ki dubi Allah da ma’aiki ka mayar da ni Albasu wallahi na yafe zaman gidanki, ki maida ni Albasu na mutu cikin aminci tun bata tsaface ni a gidan nan ba.” Goggo na maganar hawaye da majina na zuba, a gefe ɗaya fitsari ne ke zuba don Goggo ta yi fitsari daga ɗakin Raihan zuwa babban falo ya kai sau uku.
A ɗan tsorace Mommy ta waiga tana faɗin, “Goggo lafiya kuwa wace ce ta zama matsafiya?” Goggo ta fyace majina da gefen zaninta ta ce, “Wa kuwa kika sani idan ba Rehanu ba. Wallahi yadda na ga tana tsafi ido biyu na ga Annabi haka…” Tun bata ƙarasa maganar ba Mommy ta fara waige tana katseta da sauri cikin ƙasa-ƙasa da murya.
“Goggo don Allah ki daina faɗin haka wallahi Alhaji yana gida kar ya ji abin da kike faɗa, kin san fa baya kawaici a kan yarinyar nan Raihan.” Tana rufe baki Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, “Allah ya tonu asirinku, ashe gulmar Ɗana kuke da jikalleta to ahir ɗinku wallahi ke Zinaru ki yi ta kanki arziƙi kika zo ci ba zan miki baƙin ciki ba, gida dai gidan Ɗana ne ba a isa a sawa jikata ido.” Goggo takaici ya sake cikata tana ganin kamar gori Inno take yi mata, don haka a zafafe ta ce, “Allah ya sa ni na haifi Abulle har ɗan naki ya aura, magana ce na gama ta yau za a mayar da ni Albasu don wannan sheɗaniyar jikar taki ba za ta sayar da kaina ina ji ina gani ba.” Inno na jin haka ta yi zaman ƴan bori daɓar sai kawai ta fashe da kuka, da sauri Mommy ta koma wurinta tana rarrashinta amma fir taƙi yin shiru. Suna nan zaune Alhaji Abdallah ya sauko cikin dakakkiyar shadda ruwan toka da hula baƙa, kayan ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Tun kafin ya ƙaraso Mommy ta fisge ɗankwalinta ta rufawa Goggo, yana ƙarasowa ya ce, “Lafiya dai Inno mai yake faruwa?” Inno na jin haka ta rushe da kuka tana faɗin, “Audullahi ka dubi irin sitirar da ka yi wa Zinaru ita da ƴarta amma da yake sun samu wuri wai cin naman ka suke da ƴarka ɗaya tilo a gidan duniya. Don Allah ko don darajar haihuwa Abulle ai da ɗagawa yarinyar nan ƙafa ina dalili tana uwarta tana cin namanta?” Goggo ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce:
“Audullahi wallahi tun wuri ka san halin da kake ciki, kwarankwatsa dubi Rehanu ta shiga ƙungiyar asiri.”
Kamar wanda aka zagi iyayensa haka Alhaji ya ɓata fuska sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya ce, “Goggo kin san wa kike faɗa kuwa? Raihan ɗina ce ta shiga ƙungiyar asiri?”
“Ƙarya na yi maka kenan Audullahi?” Goggo ta tambaye shi tana ɗage kai gefe. Shiru ya yi don ya san idan ya buɗe baki a kan Raihan za a iya samun matsala shi kuma yana ganin girman Mahaifiyar matarsa, ba zai so wani abu ya haɗa su ta sanadiyyar Raihan ba. Ganin haka ya sa Mommy ta riƙo hannun Goggo tana cewa, “Goggo ta so mu je ɗaki don Allah.” Inno na ganin haka ta fashe da kuka tana faɗin:
“Allah ya fini sanin dalilin da ya sa bai bani ƴa mace ba, amma ya yi mini komai da ya bani Audullahi da ban haihu ba sai na rasa mai kaini ɗaki nima.” Tana gama maganar ta kalli Alhaji ta ci gaba da cewa, “Audullahi nima ka kaini ɗaki ba sai an goranta min ba, kuma wallahi aure za ka ƙara don ba za ka zauna da macen da bata ganin mutumcina ba.”
Daddy na shirin yin magana suka ji Raihan ta turo ƙofa ta fito fuskarta murtuk babu fara’a, da sauri Goggo ta fara ja baya tana leƙenta. Daddy na ganinta ya saki murmushi ya rungumota yana faɗin, “Barka da fitowa habibtyn daddy.” ƙarasowa wurin ta yi ta ce, “Daddy ba dai fita za ka yi ba?” riƙo hannunta ya yi ya ce, “Yanzu ma kuwa don na gama komai.”
Fisge hannunta ta yi ta koma kan kujera tana faɗin, “Na faɗa maka gaskiya za ka yarda?” Murmushi ya yi ya ƙarasa wurinta ya ce, “Faɗi babyna.”
“Ka haƙura da fita da baƙar mota idan ba haka ba za a samu matsala.”
Mommy ta kalle ta tana faɗin, “Raihan me ya sa bakinki baya furta alheri ne? Ke kin san gaibu ne da za ki yanke masa wannan hukuncin.” Goggo da ke gefe tana son yin magana tsoro ya hanata. Daddy ya gyara zaman agogonsa yana faɗin, “Baby sai abin da kika ce da wacce kike son da ita.” Daga wurin da take ta ce, “Kowacce ka yi niyyar fita da ita amma ban da baƙar.” Daga haka sallama ya yi musu Mommy ta wuce raka shi, Raihan na ganin haka ta ƙarasa gaban Goggo ta tsugunna a wurinta tana faɗin, “Wallahi na kuma jin kin danganta ni da ƙungiyar asiri Allah za ki yi mamakina, sai na kaiki Daulatul Jinnul nariy na azabtar da ke.” Inno da ke gefe ta karɓe zancen da faɗin, “Wallahi kema kya gaya mata ai ni wallahi ban yafe wannan ƙazafin da ta yi miki ba. Ni dai wannan larabcin da kika yi ne ban san me kika faɗa ba, amma idan za ki tafi da ita don Allah ki kaini na ga yadda Zinaru za ta yabawa aya zaƙinta.” Raihan bata bi ta kansu ba ta wuce kan dianning table, saboda yadda yunwa take sasaƙar cikinta don abincin da ta ci babu in da yaje mata. Tana zama ta fara buɗe kulolin da ke wurin nan take ta fara tasa kulolin a gaba, ɗaya bayan ɗaya tana cinyewa, kuloli huɗu ne a wurin amma da zaman ta ko minti biyar bata yi ba ta cinye abincin ciki gabaɗaya, tare da shanye shayin da ke cikin fulas ɗin ta kora da ruwa sannan ta dawo falo ta zauna. Lokacin da ta dawo tuni su Inno sun wuce sashensu don haka basu lura da abin da Jabun Raihan ta aiwatar ba.