BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Kan kujera suka ɗorata Likitan ya fita yana yi wa Daddy bayani.

“Wato Alhaji da alama ciwon yarinyar nan ya dawo sabo, domin idan har abin da mahaifiyarta ta faɗa ne za mu iya cewa ya ninku a kan na da, saboda a da tana surutai kawai idan abin ya tashi, amma a wannan karon tana nuna kifi a matsayin ɗan cikinta. Akwai issue mai girma a game da lamarin ciwonta, za mu yi bincike mai zurfi a kai, sannan kar a riƙa wasa da magungunanta ta riƙa sha akai-akai.” Jikin Daddy a sanyaye ya miƙawa Dr Hamza hannu yana faɗin, “Na gode sosai Dr don Allah a yi wani abu kai, ka san ina matuƙar son Raihan ba zan iya jure rashinta.” Dr Hamza ya jinjina kai ya ce, “Insha Allah Alhaji kuma a ci gaba da addu’a everything will be successfully.” Daga haka suka yi sallama da Likita. Yana komawa ciki tuni ma’aikatan gidan suka shiga hada-hadar gyaran falon, kusa da ita ya je ya zauna ya zura mata ido, hannu ya ɗora a kan goshinta zuciyarsa babu daɗi ya ce, “Wish you quick recovery dear, me ya sa al’amuranki basa zuwa da sauƙi why? Allah ya baki lafiya my baby.” Mommy na ƙarasowa wurin ta dubi Alhaji cikin damuwa ta ce, “Habibi ni kam wata shawara gare ni.” Bai furta mata komai ba ya ɗago yana kallonta ya yi mata alamar yana sauraronta. Jingina ta yi da bango ta ce, “Gani nake yi mai zai hana ciwon yarinyar nan a haɗa shi da na islamic chemist ko akwai shafar aljanu a ciki…” Tun bata dire zancenta ya buga mata tsawa da cewar, “Ba na son na ƙara jin kin danganta min Raihan da wani jinsin bayan bil’adam, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci. Me ye wani islamic chemist malaman da kaje wurinsu sai dai su fara yi maka turare da hayaƙi, da sun samu wuri za su fara yi maka maula. Idan ba za ki taya ni mu nema mata magani ba don Allah ki cire hannunki daga cikin maganar, ni kaɗai na isa na nema mata lafiya.” Ran mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, amma babu yadda ta iya haka ta ja bakinta ta tsuke don ta san akan wannan maganar sai su haura sama su faɗo. Daddy ne ya cicciɓi Raihan zai kaita ɗaki da sauri Mommy ta nuna masa ɗakinta tana faɗin, “Ka kaita Toilet ɗina zan gyara mata jikinta a can sai ta kwanta.” Bai tanka mata ba ya wuce ya kaita ɗakin Mommy don har lokacin fushi yake yi.

Mommy da kanta ta gyara Raihan ta kwantar da ita a kan gadonta, zama ta yi a gefe tana kallon ƴartata cike da tausayawa. Idanunta ne suka ciko da ƙwalla, ta sharce ƙwallah ta furta, “Wannan ita ce kalar tamu ƙaddarar, Allah ya baki lafiya Raihan.”

Raihan ta jima tana bacci sai bayan wani lokaci sannan ta tashi, ɗingisawa ta ci gaba da yi har ta fito zuwa falo. A lokacin an gyara falon sai ƙamshin turare yake. A zaune ta hango Mommy Mama Uwani na zaune a ƙasa tana matsawa Mommy ƙafa, cike da farinciki Mama Uwani ta ce, “Uwar ɗakina kin tashi?” Kafin Raihan ta yi magana Mommy ta furta, “Barka da tashi My Princess.” A ɗingishe ta ƙaraso wurin cikin damuwa mommy ta ce, “Me ya samu ƙafar taki?” Raihan ta yamutsa fuska ta ce, “Wallahi haka kawai na ta yi min nauyi. Mommy kamar mun je wani wurin ko? Ko dai mafarki na yi ne?” Mommy a tunaninta lokacin da ciwon Raihan ya tashi take nufi, ita kuma Raihan tana son tuna zuwanta Duniyar su Huzaifa amma kanta ya yi nauyi ta manta. Mama Uwani ta kafeta da ido sannan ta ce, “Uwar ɗakina sannu kin ji, ai ke kin zama ƙadagaren bakin tulu a karki a kar tulu a barki ki ɓata ruwa.” Raihan ta ce, “Yauwa Mama Uwani, don Allah haɗo min ruwan tea.” Ta yi maganar cikin jin daɗin kanbabawar da Mama Uwani ta yi mata, Nan take Mama Uwani ta tashi ta nufi hanyar kitchen. A hankali Goggo ta turo ƙofa ta fito falo, don tun lokacin da ciwon Raihan ya tashi da suka shige ɗaki babu wacce ta fito a cikinsu, kallo ɗaya za ka yi wa Goggo ka tabbatar da tsoro ya mamaye zuciyarta amma sai ta dake ta fara yashe baki tana faɗin, “Rehanu hutawa ake yi.” Raihan ta taɓe baki ta ce, “Ni kam ko karatu ne wallahi Goggo ya ci ki haddace sunana, kullin sai na ce miki ba sunana Rehanu ba amma ina miyar kuka ta toshe ko’ina.” Mommy ta ɓata fuska ta ce, “Gidanku Raihan.” Goggo da ta lura Raihan ta dawo cikin hayyacinta, ta yi mata daƙuwa ta ce, “Gata a zaune ita kika gayawa haka.” Goggo ta nemi wuri ta zauna tana faɗin, “Abu kunna mini wannan shirin da suke na ƙasashen labarawa ko idanuna sa ƙara ƙarfi.” Inno ta ƙaraso wurin tana faɗin, “Allah ya sani ba za mu kalli masu jajayen kunne ba, ni dai ki kai mini shirinsu wannan yaron Adamu zango da Ali Nuhu, ki saka mana sangaya mu kallah.” Mama Uwani ce ta ƙaraso da kofin shayi ta taimakawa Raihan suka wuce ɗaki, don ƙafarta sosai ta yi mata nauyi ɗingisawa take yi.

Shigar su ɗaki keda wuya, Mama Hasiya ƙanwar Daddy ta yi sallama cikin falon. Fara’a ɗauke a fuskarta ta shiga cikin falon. Mommy da murmushi ta tarbi Mama Hasiya tana faɗin, “Mai gidan da ba awo ba cefane, ba waya ba labari.” Mama Hasiya ta zame mayafin jikinta tana faɗin, “Mutum da gidansa wacce waya zai yi.” Mommy ta saki murmushi tana faɗin, “Barka da zuwa wai da yamman nan kike tafe.” Mama Hasiya ta ajiye jakar hannunta tana faɗin, “Wallahi dole ce ta kawo ni, kin san Hubbi ya yi tafiya ƙafar Dubai to sun yi waya da DR John wai yau zai shigo gari so kin san matsalar hospital ɗin Dr John idan kana son ganinsa sai dare.” Mommy ta sauya fuska cikin yanayin damuwa ta ce, “Allah ya sa a dace wai wancen karon ba ya ce ƙasa da six months komai zai iya faruwa ba? Ya ce za ki iya samu ciki a kowanne lokaci.” Mama Hasiya ta jinjina kai ta ce, “To kin ga dai shiru, lamarin rashin haihuwar nan ba ƙaramin damuna yake yi ba. Tun hubbi bai fara damuwa ba yanzu na fuskanci abin ya fara damunsa, shekara sama da goma sha biyar ba haihuwa an ya ina da rabon ganin ƙwaina a duniya kuwa?” Mama Hasiya ta yi maganar idanunta na cikowa da ƙwallah. Cikin sigar lallashi Mommy ta dubi Mama Hasiya tana faɗin, “Komai kika ga ya faru da bawa da sanin Allah, ba a nan take ba. Komai fa lokaci ne mutane da dama akwai waɗanda suka fiki daɗewa kuma Allah ya kawo musu mafita, mu ci gaba da addu’a komai ya yi farko zai yi ƙarshe.” Mama Uwani ta ƙaraso cikin falon fuskarta ɗauke da fara’a tana faɗin, “Hajiya barka da zuwa.” Bayan sun gaisa ta fara kawo mata kayan ciye-ciye da shaye-shaye bata jima da barin wurin ba su Inno suka fito falo, nan take suka ci gaba da hira.

Mama Hasiya ƙanwar Daddy ce uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, tana auren wani hamshaƙin ɗan kasuwa a unguwar Hotoro. Sun shafe shekara goma sha biyar da auren saurayi da budurwa, sai dai Allah bai basu haihuwa ba duk wannan tsahon shekarun, sun yi yawon ƙasashe amma duk ba a dace ba har sai da suka fara ganin wani likita Dr John, ta taɓa samun ciki ta yi ɓari har sau biyu daga haka ko ɓatan wata bata sake yi ba, don haka ta nace wa Dr John lokaci-lokaci take zuwa ganin likita.

DR JOHN SPECIAL HOSPITAL shi ne sunan asibitin da Mama Hasiya take zuwa ganin likita, asibitin a bayan gidan su Mommyn Raihan yake. Duk ranar da Mama Hasiya za ta zo ganin likita a gidan Daddy take kwana saboda asibitin sai goman dare Dr John yake fara ganin patient, wannan dalilin ya sa idan ta ga likita take dawowa gidan ɗan’uwanta ya kwana, yawaici tare suke zuwa da Mommy saboda mai gidanta yana tafiye-tafiye, kuma yawo babu inda ba su je ba don neman haihuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button