BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Cikin Dare.

Wata irin guguwa mai ɗauke da amsa kuwwa marar daɗin sauraro ta fara karaɗe lungu da saƙon da ke cikin dodon kunnuwanta, a hankali iskar ta fara kaɗa labulayen ɗakinta. A hankali ta fara ratso bangawayen da gidan tana raɓewa ta jikin ƙananan shukokin da ke harabar gidan, ta jikin bangon ɗakinta ta ratso jikinta ɗauke da jajayen kaya masu ratsin baƙi haɗe da ɗishi-ɗishin busasshen jini a jikinta. Tana shiga ɗakin Raihan ta tsaya cak a bangon gudu, ta fara huro mata iska nan take Raihan ta miƙe zaune hannuwanta toshe a kunnuwanta ta dubi Intisar. Cikin wata irin girgiza ta ƙaraso wurin Raihan ta kama hannuwanta tana shirin yin magana Raihan ta ce, “Intisar me kika zo yi yanzu gidanmu?” Intisar bata bi ta kanta ba ta hura mata iska a fuska nan take ta fara layi tana shirin faɗuwa, da sauri Intisar ta tarota tana dafe kafaɗarta ta ce, “Za ki bi ni?” Babu musu Raihan ta gyaɗa mata kai, Intisar bata bi ta kanta ba ta riƙe hannunta nan take suka ɓace daga ɗakin.

Gudu suke zabgawa cikin sararin samaniya a can wani ƙasurgumin dajin wani makeken gida suka sauka, Raihan ban da ido babu abin da take bin ƙawarta Intisar da shi. A wani katafarn kogon dutse suka dira mai ɗauke da wasu irin mutane masu mummunar hallita, ɗauke suke da jajayan sitiru sai zanen jini a jikkunansu. Wata mummunar hallita ce a tsugunne mai ɗauke da kan barewa da manyan ƙahunhuna ga wani irin jini da yake ɗiga daga bakinta a cikin wani ƙaton faifai. Zuwansu ke da wuya wani tiƙeƙe da ya kasance babbansu ya dubi Intisar ya ce, “Hatsabibiya Bungulu na maraba da baƙuwa mai daraja.” Intisar da dubi Raihan ta ce, “Ki yi gaisuwa ga Habibiya Bungulu ta saka miki albarka.” Kamar bawa da uban gidansa haka Raihan ta dubi wannan hallitar ta duƙa kamar yadda ta ga suna yi ta miƙa gaisuwa. Da wani ƙaton sirinji wani ɗan tsamurmuri ya zuƙi jinin da wannan hallitar take ɗigarwa daga bakinta, a shammace ya samu damtsen hannun Raihan ya kafa mata har sai da ya juye jinin jikin sirinjin a jikinta, sannan ya zuƙo nata ya fesa a jikin hallitar. Lokaci ɗaya ta fara rawar ɗari kamar mai jin sanyi, tun tana daga tsaye har ta duƙushe a wurin tana karkarwa. Tana jima tana abu ɗaya sannan ta tsagaita da rawar ɗarin, a zabure ta miƙe tsaye cikin wani irin ƙarfi ta zurawa mummunar hallitar tana jiran umarninta.

Buɗe bakinsa ya yi nan take wasu baƙaƙen macizai suka fara fitowa daga bakinsa, suna faɗowa suke fasa kai suna zagaye Raihan. Cikin wani irin yanayi hallitar ta miƙe tsaye tana girgiza sannan ta fara magana da wani irin yare har sai da ta yi yare ya fi kala goma, sannan ta yi magana da harshen hausa.

“Tabbas mun yi babban kamun da muka jima muna jiran wannan rana. Domin ƙara tabbatar da abin da muke zargi goɗiya za ta kawo mana jini mafi muhimmanci wanda zan shayar da mai gidana domin samun lafiyarsa.” Tun bai rufe baki ba Raihan ta russuna tana faɗin, “An gama Hatsabibiya Bungulu.” Mummunar hallitar ta nunawa Raihan wata ƙatuwar ƙwarya mai cike da tafasasshen jini ta ce, “Babu buƙatar haka domin da alama ke shugaba ce, muna buƙatar jinin wannan matar yanzun nan…” Raihan ta amsa mata tun bata ƙarasa maganar ba da cewar, “Jininta ya halarta a gare ki, duk duniya babu jinin da za ki buƙata ya gagara a wurina.” Tana rufe baki Hatsabibuya Bungulu ta miƙa mata wani busasshen ƙashi da alama ƙashin jikin bil’adam ne. Raihan na karɓa ta wuce cikin sararin samaniyar iskar sihiri bata tsaya ko’ina ba sai a katafaran cikin gidan Mahaifinta, sai da ta zaga ɗakunan gidan sannan ta dira a ƙofar ɗakin mahaifiyarta.

???????????? WASAN YANZU YA FARA, MAZA HANZARTA KI BIYA NA KI DON JIN WACECE AINIHIN ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ƊIN, SHIN A CIKIN SU WACECE ƳAR GABAN GOSHIN ALJANIN SOYAYYAR? SHIN WACECE WANNAN INTISAR ƊIN KUMA WACECE HATSABIBIYA BUNGULU? ???? AMSOSHIN NA GABA DON JIN ƘULALLEN ƊAURIN DA KE CIKIN LABARIN.

Share Fisabillah????
[7/10, 10:33 AM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

© AMEERA ADAM

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

          FREE PAGE 4


 Raihan na fita Intisar ta ƙarasa gaban Hatsabibiya Bungulu rai a matuƙar ɓace ta ce, "Hatsabibiya uwar hatsabibai, sai kai mai siffar dabba a bayan fage ki koma bil'adama. Babu hallitar da ta gagare ki rikiɗa duk girmanta duk ƙanƙantarta, yaya ina tunanin lokacin share mini hawayena ya zo amma na ga wankin hula yana shirin kaini dare. Na kawo Raihan domin a salwantar mini da rayuwarta amma da alama tana shirin samun fada a wurin nan, yake Hatsabibiya tun farko kin san ba haka muka yi da ke ba." 

Hatsabibiya Bungulu ta yi girgiza lokaci ɗaya ta rikiɗa zuwa wata kyakkyawar budurwar, zaune take tsirara sai wasu sassan gaɓɓoɓin jikinta da ke rufe. Wani malalacin murmushi ta saki sannan ta dubi Intisar ta ce, “Da mun san kina da wannan yarinyar da tuni mun jima da umartarki ki kawo mana ita, sai dai kash! Silar saninta na daga gare domin biyan buƙatarki. Kin kawota domin mu kashe ta sai dai ba za ta mutu ba.” Da hannuwa biyu Intisar ta sa ta toshe dodon kunnenta saboda yadda ta ji kalmar a kunnenta, a duniya idan da wacce ta tsana to Raihan ce. Lokaci ɗaya ta murtuke fuska tana shirin yin magana Hatsabibiya ta ci gaba da magana.

“Na tabbata baki san wacece Raihan ba, da kin san amfanin da za ta yi mana a cikin ƙungiya da bakinki bai furta kalmar kisa a tattare da ita ba. Shin ko kinsan Muraza?” Da sauri Intisar ta ɗago da kai tana kallon Hatsabibiya tana girgiza kai bakinta na rawa ta ce, “Ina zan santa ya ke Hatsabibiya mu da muke nemanta ido rufe.” Matashiyar budurwar da ake kira da Hatsabibiya ta yi girgiza nan take ta rikiɗe zuwa surar wani ƙaton tsuntsu, sai da ya yi tsalle-tsallensa sannan ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci gaba da magana cikin siffar tsuntsu.

“Tabbas Raihan ita ce Muraza, tun shigowarta kogon dutsen nan alaminta da babban matsafi ya sanar da mu suka bayyana. Ƙofar nasarorinmu ta buɗe ƙarfin iko, tsafi da sihiri da ƙarfin ƙungiyar asirinmu za ta sake dawowa da ƙarfin ikonta, domin haske ya bayyana inuwarta ɗauke take tartsakin wuta mai halakar da magautanmu, za mu riƙe hannu bibbiyu domin saminta tamkar samun lu’ulu ne a ƙarƙashin teku, idan muka yi sake ta kubce mana tabbas mun tafka babbar asara.” Intisar ta faɗaɗa murmushinta sai da ta yi taku biyu sannan ta waiwayo ta ce, “Haƙiƙa zan jinkirta buƙatata har tsawon wani lokaci bayan mun cimma matsayarmu, amma tabbas ko ba yanzu ba akwai ranar da Ya za ta ɗakin ƙanwa, lokaci na tafe zan aiwatar da abin da yake ci mini tuwo a ƙwarya. Ni ma lokaci ya dawo mini da zan karɓo sihirtacciyar sandar mahaifiyata Bokanya Shirzan, a lokacin ne duk wani cikar ikona zai dawo.” Tana rufe baki suka fara ƙyaƙyata wata irin dariya mara daɗin sauraron mai ɗauke da amsa kuwwar kukan jakuna, suna tsaka da kuka sai ga wani matashin saurayi ya diro cikin ɗakin hannunsa ɗauke wani jariri sabuwar haihuwa. Jaririn sai mutsu-mutsu yake ko jikinsa ba a gyara ba balle a yanke cibiyarsa, a kan tafin hannun wani gunkin tsoho da ke tsaye ya wara hannuwansa. Yana ɗora jaririn a kai nan take wannan Hatsabibiya da ke ɗauke da siffar tsuntsu ta taso ta dira a kan cikin jaririn. Wata ƙara ya ƙwalla saboda wata irin azaba da ke ratsa sassan jikinsa, da ƙafafuwansa tsuntsun ya huda ƙirjin jaririn ya kafa kai yana tsotsar jinin jaririn. Kafin wani lokaci tuni idanun jaririn sun ƙafe jikinsa ya saki numfashinsa ya ɗauke, tana ganin haka ta tashi daga kanta sai Intisar ta ƙarasa ta banƙare ƙirjinsa ta ciro zuciyarsa ta wurga bakinta ta cinye.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button