BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Duk cikin ƴaƴan Inna Furai babu wanda ya fi farinciki da tafiyarsu irin Auwalu saboda zuciyarsa gabaɗaya hankalinsa yana wurin Yahanasu don ya san a wannan lokacin tuni ta yi fushi sai ya yi aikin rarrashi. Yana tafe yana haska fitila har ya ƙarasa ɗakin, sai dai turus ya yi a ɗan tsorace yana karewa ɗakin da Yahanasu kallo. Fitsarin da ya ƙarasa gangarawa ƙafarsa ne ya dawo da shi daga duniyar tunani, matsawa ya yi gefe yana leƙa fuskar Yahanasu da ke manne da bango ya ce,

“Yahanasu lafiya kuwa?” Yahanasu na jin muryar Auwalu ta rushe da kuka tana cewa, “Auwalu fatalwar Baba na gani wallahi shi ne har cewa ya yi za su tafi da ni.” Cikinsa ne ya bada wani sautin ƙulululu! Da sauri ya ja baya yana dafe ƙirji ya ce, “Kina nufin da gaske kema kin ga fatalwar Baba?” Yahanasu ta nuna masa gadon bayanta ta ce, “Duba ka ga shatin carbinsa a bayana har dukana ya yi da shi kuma ya ce daga yau kar sake buɗe idona.” Tsoro ne ya mamaye zuciyar Auwalu musamman da idanunsa suka yi tozali da shatin carbin Mahaifinsu ruɗu-ruɗu a jikinta. Hankalinsa bai ƙara tashi ba sai da ya hango wani guntun likkani a gefen ƙafar Yahanasu. Da sauri ya fisgota suka faɗa gado jikinsa na rawa ya ce, “Yahanasu wallahi maganarki haka take kin ga Likkafani can a ƙasa.” Yahansu na jin haka ta ƙara rintse ido tana kuka kamar hawayenta za su ƙare. Auwalu ne ya yi ta maza ta miƙe cikin sanɗa ya banko musu ƙofa da ƙarfi ya sa sakata.

Duk abin da yake faruwa a kunnen Baba Sule da Sahura har zancen Likkafani, wannan maganar ba ƙaramin ɗaga musu hankali ta sake yi ba. Don da har bacci ya fara yunƙurin awon gaba da su kukan da Yahanasu ta rushe da shi ne ya wartsakar da su tare da sa su yin carko-carko kamar masu shirin ko ta kwana.

Dubu tun da ta koma ta yi luf sakamakon motsinta ya so tashin Hasiya Matar Rabe, don haka ta yi kasaƙe daga haka ba a jima ba bacci ya yi gaba da ita don hatta sallar Asuba sai da aka yi da gaske sannan Dubulliya ta samu gabatar da ita.

Washegari.

Jama’ar gidan gabaɗaya kowa ya tashi an ci gaba da harkoki kamar ba taron mutuwa ba. Sai dai gabaɗaya labari ya watsu a ko’ina Inna Furai ta yi ido huɗu da fatalwar Maigaidansu, labarin da wasu suka riƙa ganin kamar tsufa da rikici ne yayin da wasu suke ganin tsabar dukan da mutuwar ta yi mata ne. Sai dai babban abin da ya ja hankulan mutane ganin ɗakin Baba Sule da Auwalu ya rufe. Ko motsinsu babu wanda ya ji bare a sa ran za a ga fitowarsu.

Ɗakin Baba Sule aka fara zuwa ana bugawa, Sahura ta zabura za ta miƙe saboda ta ji muryar mutane don ta yanda ta ayyanawa zuciyarta muddin ta samu ta fice daga ɗakin to ba za ta ƙara kwana a gidan ba sai gidan Mahaifinta. Sai dai tana miƙewa caraf Baba Sule ya damƙi hanunta yana cewa, “Ina za ki tafi ki bar ni?” Sahura ta ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce, “Ai mutanen gida sun tashi ka ga muma sai mu fita zaman ɗaki ba zai kai mu ba.” Baba Sule ya yi fakare yana nazari sannan ya ce mata, “Sahura yau ko bayan gida za ki shiga wallahi sai dai mu tafi tare, don ba zan bari matattu su tafi da ni da kwana na a gaba ba.” Bugun ƙofar ne ya tsananta don haka suka taso riƙe da hannun juna suka zare sakata, sai dai suna buɗe ƙofa kyallen likafanin da Dubu ta soka musu ya faɗo. Daga waɗanda suke tsaye a ƙofar ɗakin har su na cikin ɗakin bazama suka yi a guje, suka yi cikin gida. A cen ɗakin Yaya Babba suka yada zango sai dai har lokacin Baba Sule yana riƙe da hannun Sahura. Yaya babba sakin baki ta yi tana kallon Baba Sule da ya yi tsamo-tsamo a cikin mata ta ce, “Sule me kake yi a kan cinyar Uwani?” (Uwani ƙanwar Mahaifiyar Sahura ce.) Baba Sule gabaɗaya zuciyarsa a dagule take saboda gani yake rayuwarsa ta zo ƙarshe.

Ba baka sai kunne. Baba sule ban da hawaye babu abin da yake yi. Wannan shirun da Baba Sule ya yi ba ƙaramin ɓata ran Yaya Babba ya yi ba, don haka ta dube shi ta ce, “Bana son iya shege kai Sule idan ba za ka yi magana ba, ka fice mini daga ɗaki ko na kwashe maka albarkar da ta yi saura a kanka.” Baba Sule ya sake matsar ƙwalla ya ce, “Inna wallahi Fatalwar Baba ce za ta tafi da ni matukar na saki hannun Sahuwa ƴan sama jannati ne za su tafi da ni.” Ku san mutuwar zaune Yaya Babba ta yi saboda labari ya risketa daga wurin kishiyarta ga shi Ɗan cikinta ma ya sanar da ita.

Nan fa gida ya hautsine hantar cikin kowa ta kaɗa saboda fargaba, Sai da Yaya babba ta yi da gaske sannan Baba Sule ya saki hannun sahura. Ai kuwa yana sakin hannunta ta ranta ana kare. Baba Sule na ganin haka ya rufa mata baya. Sai da ƙyar aka samu aka tsayar da su a soron gidan tare da tura Baba sule cikin ɗaki don Yayan Mahaifinsu gani yake kamar gamo ne suka yi. Dubu ban da dariyar mugunta ƙasa-ƙasa babu abin da take yi.

Sai daga baya aka farga da su Auwalu da suke ɗaki don haka da sauri Yayan Mahaifinsu ya je ya sa suka buɗe ƙofar da ƙyar, Auwalu yana maƙale da Yahanasu don gani yake idan ya sake ta kamar Fatalwar Mahaifinsa za ta yi awon gaba da ita.

Malam Idi shi ne yayan Mai Carbi, tara mutane gidan ya yi gabaɗaya yana yi musu nasiha da nusar da su illar yarda da amincewa abin da suka yi tozali da shi. Sai da ya gama wa’azin sannan ya bawa Inna Furai damar ta yi magana.

Inna Fuarai ta karkace ta ce, “Yaya Idi yadda na ga Fatalwar Malam na ga Annabi. Ganin idona na ganshi kuma har umarnin shayar da su Auwalu ya yi.” Sai da suka gama jin jawabinta tsaf sannan aka ce Yahanasu ta yi faɗi abin da ta sani, Yahanasu da ta buɗe ido da kyar tana sunne kai ƙasa don duk yanda hankalinta ya ɗan kwanta har Yaya Idi ya sa ta buɗe ido bata gama sakewa ba. Ta fara yi musu bayani dalla-dalla sanna ta ɗora da cewa, “Kuma da bakinsa ya sanar da ni duk wanda ya wayi gari da likkafani a ɗakinsa to gaba shi za su ɗauka. Shi ya sa na ce tawa ta ƙare.” Auwalu ya rumgumota yana cewa, “Ba za ki mutu ba Yahanasuna” Yaya Idi ya yi jim sannan ya ce, “Idan na fahimta wani ne kawai yake son razanar da mutanen gidan amma babu damuwa ku bar mini komai a hannuna zan san yanda zan ɓullowa lamarin.

Dubu tana gefe tana jin duk wainar da ake toyawa don haka ta saci jiki babu wanda ya lura da ita, kuma babu wanda ya taɓa kawo ita za ta aikata wannan abin. Dubu na tafiya ta wuce ɗakin Marigayi ta zaro wasu kayansa da yake zuwa sallar juma’a da su. A wanke suke a goge fari ƙal da su, sai da ta bubbuɗa su ta je bakin katangar banɗaki wacce mutum zai iya haurawa ta wurin ta ajiye, hularsa ta saƙale a jikin wata itaciyar tunfafiya sai kuwa ta kwaso a guje ta shiga wurin taron da suke gabda kammalawa. Ihu take kwarawa kamar wacce ake ɗanawa wuta tana cewa, “Wayyo Allah na ga Fatalwar Baffa na gani zai tafi da ni. Kafin ka ce wani abu tuni wurin ya watse sai takalma da ɗankwalaye da aka barsu suna cin karen su babu babbaka. Yaya Idi sai da ya yi kusan adungure biyu sannan ya samu ya shige ɗakin Inna Furaira. Hularsa kuwa ta yi tsalle ya fi sau biyar kafin ta samu sukuni faɗuwa can bakin ƙofa.
[7/11, 7:44 PM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

© AMEERA ADAM

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button