DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL
“Sai mu kashe Huzaifa idan zai kawo mana matsala.” Hatsabibiya ta faɗa kanta tsaye ba tare da ji shakku ko shayi ba.” A firgice Intisar ta ɗago cikin tashin hankali ta zubawa Hatsabibiya ido, bakinta na rawa ta furta. “Kin manta wanene Huzaifa a wurina? Mijina ne fa.” Hatsabibiya ta wara hannuwa cikin halin ko’inkula ta ce, “Ci gabanki ya fi zamantakewarki da shi don haka bana ganin zai amfane ki da komai.” Intisar ta turɓune fuska ta ci gaba da cewa, “Ba zan lamince a kashe mijina kuma uban ƴaƴana ba, amma tabbas dole a nemi wata hanyar da za a samu mafita.”
???? NA SAN DA YAWA ZA KU YI MAMAKIN JIN INTISAR MATAR HUZAIFA CE, KO KUN TUNO MUGAZA???? ITA CE INTISAR. AMMA MAI YA SA HUZAIFA BAI GANE TA BA HAR SUKE TAKUN-SAƘA, SHIN WACCE RIBA MUGAZA ZA TA CI DA TA JEFA RAIHAN A ƘUNGIYAR ASIRI? IDAN SU MOMMY SUKA KOMA SHARAƊA SUN TSIRA KO DA SAURAN TAFIYA?
Share pls????
[7/14, 5:09 PM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
© AMEERA ADAM
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
FREE PAGE 7
Daddy yana tafe Raihan na riƙe a hannunsa har suka shiga cikin gidan ayyane-ayyane yake yi, yana mamakin wane irin macijine da nan take zai naɗe mutum ya kashe shi, kuma a ce ya fito daga ɗakin Raihan ɗin sa. Kwafa ya yi yana tunanin irin matakan tsaron da zai ƙara akan na da, har suka shiga ciki. Mommy jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba don tun lokacin da abin ya faru ta fahimci macijin ɗakin Raihan ba ainihin dabba ba ne. Sai dai a wannan karon ta ci alwashin faɗawa Daddy gaskiya duk irin ɓacin ran da zai yi, don haka suna zuwa ta nemi ganawa da shi a sabon ɗakinsa dama gidan ya gina shi ne da sunan bayan wasu watanni su tare, amma kasancewar ba a gama masa ƙaƙale-ƙaƙale ba ya sa suka dakata da komawar, amma dole ta sa suka tashi a rana tsaka suka koma. A gaggauce Daddy ya dubi mommy ya ce, "Faɗi ina jin ki, kin san yanzu aka yi mini waya wai ankai su Inno da Goggo Hisba dole sai na zo, wani tashin hankali wai an tsinci su Inno a cikin masallacin Malam Isa na ƙarshen layi." Sai a lokacin Mommy ta zaro ido don bata san abin da yake faruwa ba, ganin ta shiga tashin hankali ya sa ya dube ta fuska ba walwala ya ce, "Ba fa wani abu ne na ɗaga hankali ba, komai ya zo da sauƙi yanzu dai ina zuwa." Yana gama maganar ko jiran cewarta bai yi ba ya fice daga ɗakin, jigum Mommy ta yi abu goma da ashirin ya haɗe mata.
Wani irin zafi Kabiru ya fara ji a jikinsa kamar wanda yake gaban wuta, hajijiya ya ji ta fara ɗaukansa ga wata irin matsa da macijin yake yi masa, tun yana daga tsaye har ya durƙushe a wurin yana son furta ayar Allah, amma macijin ya matse masa maƙogaronsa. Kakari ya fara yi kamar wanda ransa zai fita, a zuciyarsa yana son biya ko da ayatulkursiyyu ce amma wani abu mai nauyi ya ji ya tokare masa ƙirji kamar dutse. Yana cikin wannan halin ya ga ɗaya daga cikin macizan ya miƙe tsaye cak ya fasa kai, a hankali fatar jikin macijin ta fara saɓewa tana fita daga jikinsa sai kuma ya fara rikiɗa daga siffar maciji zuwa siffar bil’adam. A hankali wata matashiyar mace ta bayyana ilahirin jikinta gashi ne tun daga kanta har zuwa ƙugunta, ya yin da ƙugunta yake a nannaɗe cikin surar maciji. Harshe ta fara zaro masa nan take wani jaririn maciji ya faɗo, ta damƙe shi a hannunta ta kalli Kabiru da yake cikin mummunan hali ta fara magana, “Kai matashin bafulatani, wa yace maka takun saƙa da ni sauƙi gare shi? Ka san wa ka illata kuwa? Ka san wa ka kashe min kuwa? Ko kana tsammanin ka ci bulus ne?” Kabiru ya ɗago yana sauke numfashi da ƙyar idanunsa jawur ga gumi na ci gaba da tsiyaya daga jikinsa. Baki yake son buɗewa amma ya kasa, ganin haka ya sa ta sake bushewa da wata mahaukaciyar dariya sai da ta yi mai isarta sannan ta fashe da matsanancin kuka, ta jima tana yi sai ta tsagaita da kuka ta sake kallonsa ta ce, “Ba kai kana taƙama da addu’a ba ka yi ta mu gani, har za ka kashe min miji kana tunanin za ka zauna lafiya?” Macijiyar na gama maganar ta fara rarrafowa zuwa gaban Kabiru, ganin ta nufoshi gadan-gadan ya sa Kabiru ya ƙara yunƙura yana ja da baya, ya fara bude baki yana ƙoƙarin karanta addu’a haɗe da motsa baki sai dai ko kaɗan muryarsa bata fitowa, tana tunkararsa hushin numfashinsa ya doki gangar jikinta ba shiri ta ja da baya saboda wani irin zafi da ta ji yana fita daga bakinsa. Kallon-kallon suka fara yi a tsakaninsu, bata daddara ba ta sake yunƙurowa a kashi na biyu da niyyar hallakashi. Duk yadda Kabiru ya kai ga buɗe muryarsa ya yi addu’a abin ya gagara. Dabara ce ta faɗo masa ya fara biya ayatulkursiyyu a zuciyarsa, tana tunkaro shi ya fara tofa masa. Ganin tana niyyar hallaka ya sa ta sake yin baya, nan take macizan da ke gewaye da shi suka ɓace. Ƙaton da ya naɗe shi tuni jikinsa ya saki da ƙyar ya rarrafa ya bi ta jikin bangon ɗakin ya ɓace. Ɗakin Kabiru ya rage daga Macijiyar sai Kabiru, ya yin da ta sake kafe shi da ido tana ƙare masa kallo don ta fahimci makasar da za ta samu a jikinsa ta yi masa illa. A wahalce Kabiru ya faɗi can gefe yana mayar da numfashi, jikinsa gabaɗaya ya yi ja saboda irin tsananin matsar da macijin ya yi masa. A hankali jikinsa ya fara raɗaɗi, yana kai idanunsa kan fatarsa ya lura da yadda ta fara sauya launi zuwa fatar maciji. Macijiyar kallon Kabiru ta yi ta fara ƙyaƙyacewa da wata irin shu’umar dariyar ƙeta, hankalin Kabiru ba ƙaramin tashi ya yi da ganin abin da yake faruwa da fatar jikinsa ba. Yana tsaka da tunani ya riski muryar macijiyar tana faɗin, “Ka kashe min mijina ba tare da wani dalili ba, Huzaifa ya nemi tallafin mijina akan ya zo taimakonsa ka kashe shi, zafin mutuwarsa ta sa na ji tamkar na kashe ka amma ba zan kashe ka yanzu ba sai na gama wahalar da ruhina da gangar jikinka sannan na hallaka da hannuna. Ka je ko da wannan hallitar fatar macijin na barka ƙuncin rayuwar duniya ya ishe ka.” Tana gama maganar ta sake naɗewa ta koma murtukekiyar macijiya, juyi ta fara yi daga wurin da take nan take ta baje a ƙasa ta fara nutsawa cikin ƙasa har ta ɓace ɓat. Ilahirin jikin Kabiru ban da rawa babu abin da yake yi, babban tashin hankalinsa yadda ya ga fatar jikinsa ta koma ta maciji illa iya fuskarsa, hannu da ƙafarsa ne kaɗai basu rikiɗa ba da yake macijin bai taɓa masa nan ba.
A fusace Hatsabibiya ta ɗago da ta sake kallon Intisar ta ce, "Idan ba mu kashe shi ba kina da hanyar da za mu ɓullo masa? Ko kuma kina da shawara akan yadda za mu kawar da tunaninsa akan Raihan?" Intisar ta yi shiru tana nazari don ita kanta ta san wanene Huzaifa da tsananin bincike irin nasa, ta san tun da ya kafa mata ƙahon zuƙa dole zai bi diddigin wacece ita da asalinta. Ta san muddin ya gano ta ba ƙaramar ƙura ce za ta tashi a tsakaninsu ba, a baƙar zuciya irin tashi yana iya hallakata. Don ma tana amfani da sirrin tsafi da sihiri ko a yanzu yadda ya ɗora ransa akan Raihan da tuni ya gama da ita. Tana cikin tunani ta sake riskar muryar Hataabibiya ta ci gaba da cewa, "Idan har baki da wata dabarar ga tawa shawarar." Intisar ta dubi Hatsabibiya tana sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina jin ki Uwargidana maganin kukana, da ke da Abar bauta ku kaɗai na dogara da ku duniya da lahira (Wa'iyazubillah) ke kika saba ɗauke min duk wata damuwata a yanzu ma ina biye da ke don jin mafitar da za ki kawo mana kafin abar bauta ta bayyana."
Hatsabibiya kanta ya sake girma, ta miƙe daga wurin da take ta ɗauki wani dogon ƙaho mai faɗi da tsawo ta kafa shi a bakinta sannan ta durƙushe a gurin. Ta kafa tsinin ƙahon a doron ƙasa sannan ta busa shi da ƙarfinta, lokaci ɗaya tsibirin ya ɗauka tsananin ƙararsa kamar zai tsaga dajin gida biyu. Tun bata rufe baki ba aljanu masu ɗauke da munanan hallitu suka fara fitowa wasu daga ƙarƙashin ƙasa wasu daga cikin duwatsu ya yin da wasu suka fara fitowa daga ɗakin tsafi. Kafin wani lokaci tuni sun taru suna masu sujjada a gabanta, tare da yi mata kirari kamar yadda suka saba sannan suka ƙame wuri ɗaya suna jiran umarninta.
Wani irin kuka haɗe da dariya ne ya fara tashi, lokaci ɗaya tsibirin ya fara girgiza suna nan tsaye wannan mummunar hallitar mai ɗauke da kawuna (Abar bauta.) Ta ziro kawunanta zuwa harabar wurin da take. Suna yin tozali da ita suka kwanta a wurin har hatsabibiya suna masu yi mata sujjada, haɗe da kirari. Kafin ƙiftawar ido Wani baƙin aljani ya dira a gabanta cikin girmamawa yana tambayarta.
“Ya ke uwargijiyata shin jariri kike buƙata, uwar jariri tsoho ko tsohuwa kike buƙata.” Ɗago da kawunanta ta yi, sai ta saki kuka kamar na bujimin sa. Jin kukan San ya sa aljanin sake rissunawa yana faɗin, “Kin samu kin gama.” Yana gama maganar ya ɓace daga wurin.
Kallonsu ta yi ɗaya bayan ɗaya sannan ta fara magana da murya mara daɗin sauraro, "Duk abin da kuka tattauna mun saurara don haka babu amfanin maimaitawa sai zartar da hukunci." Jikin Intisar tuni ya fara tsuma nan take gumi ya rufe ta, don bata san irin hukuncin da Abar bauta za ta yanke a kan Huzaifa ba. Tana tsaka da nazari ta riski muryarta tana ci gaba da cewa, "Ba za mu kashe Huzaifa ba sai dai dole a sauyawa taku salo, sanin kanku ne a da ɗanyan kifi yana haukatata. Sakamakon ɗan da ta haifawa Huzaifa yana da haɗin jinsi da hallitar kifi. A yanzu za mu sake haukatata fiye da lokacin baya, a cikinku waye zai iya aiwatar da abin da muke buƙata?" Wata aljana da ta miƙe tsaye tana faɗin, "Abar bauta zan riƙa haukatata da surar mahaifiyarta..." Tun bata rife baki ba Abar bauta ta katse ta cikin tsawa tana cewa, "Kina tunanin wannan mafita ce? Idan kika yi haka dole za su nema mata lafiya, mu kuma duk wanda zai nuna hanyar lafiyarta sai mun tsotse jininsa." Haka aljanun da ke wurin kowa ya riƙa ɗaga hannu yana faɗin abin da zai aiwatarwa Raihan. Duk acikinsu shawarar guda biyu aka ɗauka, ɗaya daga ciki ya ce zai riƙa shiga jikin maguna yana haukatata, sai wacce ta ce za ta riƙa shiga jikin ƙadangaru sai dai kowanne da abin da zai aiwatar.
Abar bautarsu ta ji daɗin abin da suka yi, don haka ta yi na’am da wannan shawarar. Suna nan zaune aljanin da ya tafi ɗauko mata jinin da za ta sha ya dawo hannunsa ɗauke da wani Dattijon tsoho, suna shigowa tun ba su ƙarasa gaban abar bauta ba, ta miƙa hannunta guda ɗaya ya warto Dattijan haɗe da ƙwaƙule masa ido tun bai ƙarasa gabanta ba ya yi fata-fata da shi, sauran kawunan da ke jikinta suka kafa kawunansu nan take suka gama da Tsohon. Aljanin ya sake russunawa yana faɗin, “Abar bauta ya isa ko a ƙaro wani.” Gyatsa ta yi, tana lashe jinin bakinta, sai da ta tsotse ƙashin ƙoƙon kan tsohon sannan ta ɗago ta ce, “A ina ka samu wannan hallitar mai daɗi?” Aljanin ya washe bakinsa yana murmushi bakinsa ya yi girman rijiya saboda wannan ne karona na farko da abar bauta ta yabi naman ɗan’adam. Ya russuna yana faɗin, “Fansar iyayena na mallaka miki abar bauta, ki fanshi wanda kike so. Ke kika hallakawa kike tseratarwa kike kashewa kike rayawa, na samu hallitar bil’adam a cen bakin wata ƙatuwar bola fitowarsa kenan daga wurin Boka Harisu, yana shirin saka laƙanin asirin da aka bashi a ƙarƙashin shara na ɗauko maka shi.” Hatsabibiya ta sake kallon wurin da ƙoƙon kan Dattijon yake tana hura masa iska nan take ƙoƙon kan ya fara mirginawa, har sai da ya yi sau uku sannan hallitar tsohon ta sake dawowa kamar yadda take har da kayan jikinsa. Abar bauta ta kalli Aljanin da ya kawo Dattijon ta ce, “A ɗauke shi a mayar da shi wurin da yake rana ita yau a sake dawo min da shi jinin jikinsa bai ishe ni ba.” A firgice tsohon ya kalle su nan take jikinsa ya hau tsuma, ya tsugunna yana roƙo da magiyarsu, yana cikin haka ya ga anɓace da shi daga wurin.