BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

 Abar bauta ta dube su ɗaya bayan ta ce, "Na wakilta guda ɗaya daga cikinku da ƙadangare da mage, kuma ya zama wajibi a yau ba sai gobe Raihan ta kawo mana ziyara, shi kuma Huzaifa ku bar min lamarinsa a hannuna amma ba zan cutar da shi ba ko halaka shi alfarmar Mugaza da take kawowa ƙungiya ci gaba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Intisar/Mugaza ta saki tana lumshe ido, ɗaya bayan ɗaya suka fara darewa daga wurin, Hatsabibiya ta yi wa abar bauta rakiya zuwa turakarta sannan ita ma ta ɓace daga wurin.


  Daddy shi da abokinsa Alhaji Mustafa suka ƙarasa ofishin Hisbar da su Inno suke, yana zuwa ya samu su Inno a zaune duk sun yi zuru-zuru kamar waɗanda suka wuni suka kwana basu ci ba, musamman Inno da take tsaka da jin mutuwar Hasiya. Suna ganinsa Inno ta fashe da kuka ta kalli ɗan hisbar da ke gefe tana faɗin, "Amma dai kai ƙaramin ɗan sanda Allah ya watsa maka albarka, wallahi ku bar ni a ofishinku amma ni da gidan Audullah sai a lahira ma sadu da juna." Daddy yana shirin yin magana Goggo ta tsugunna a gaban ɗan hisban ta ce, "Yaro ka dubi Allah ka dubi Ma'aiki  ko tasha ne ka kaini na wuce albasu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inno me yake faruwa zuwa na yi mu tafi fa." Inno sunne kai ƙasa ta yi kamar ba ta ji me yake faɗa ba, ta kalli Goggo ta ce, "Don Allah ki duba min hallitar jikin Audullahi ta cika ko akwai nasaka, ada na ƙaryata ki amma Allah ya sani gidan Audullahi Makarai ne suke cin karensu babu babbaka a ciki." Daddy zai yi magana ɗan hisbar ya dakatar da shi, don labarin abin da ya faru tuni ya karaɗe ko'ina musamman da ƴan jarida suka samu zancen yaɗawa, Likitoci suka shiga binciken gawar Sulaiman a ya yin da suke neman Kabiru babu inda ba a duba ba amma basu ganshi ba.

Ɗan hisban da kanshi ya yi wa su Inno nasiha, ya sake faɗarkar da su da cewar duk wani abu yana faruwa ne da izinin Ubangiji kuma addu’a takobin mumini ce. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu su Inno suka bi Daddy gidan har sai da ya tabbatar musu da cewar ya sauya musu wurin zama.
Lokacin da su Inno suka koma gida tuni gidan ya yi shara-shara babu mutane sosai, don tun a tsohon gidansu ganin abin da ya faru ya sa mutane da dama kowa ya yi ta kansa. Su Goggo a ɗaɗɗare suka shiga sabon gidan, suna tafe bakinsu na motsi da alama addu’a suke yi don ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Mommy da kanta ta kaisu ɗakinsu, kowacce ta zauna shiru don ƙawayensu da suka zo gaisuwa tuni kowacce ta cika wandonta da iska.

BAYAN MAGRIBA.

 Raihan na kwance a ɗakin mommy lamo kamar mara lafiya, don gabaɗaya wani sukuku take jin ta kamar ba ita ba tun da ta dawo daga duniyar aljanu. Tana daga zaune ta ga wurgawar abu, da sauri ta tashi zaune tsigar jikinta na tashi. Wani ƙadangare ta gani yana buɗe mata baki alamar dariya, sai kuma ya fara ƙada mata jela yana yi yana tunkarota. Ƙura masa ido ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, ta fisge ɗankwalin kanta nan take gashin kanta ya hargitse, ƙananan kifaye ne suka fara fita daga bakin ƙadangare. Lokaci ɗaya ta yi kukan kura ta fisgoshi haɗe da ƙwalla uwar ƙara, tana ɗaukansa ta tura kansa cikin bakinta nan take ta fisge masa kai ta wurgar a wurin gangar jikin ƙadangaren yana hannunta. Mommy da wata ƙanwarta har rige-rigen shiga ɗakin suke saboda duk wanda yake gidan babu wanda bai ji ihunta ba. Suna tura ƙofar suka ganta a tsaye tana riƙe da gawar jangwalagwada jini yana ɗiga, ga kansa can gefe sai zare ido take tana faɗin, "Duk wanda ya ce zai hallaka mini Ɗana wallahi sai na fidda masa kai.

???????????????? WUYAR AIKI BA’A FARA BA, HAR YANZU FA ASHAFI NA BAKWAI AKE???????? KUN GA KUWA AKWAI SAURAN TAFIYA, AKWAI ƘURA A GABA.????????‍♀️????????

Share Hilis????
[7/16, 12:01 PM] Ameera Adam????: ZAUJATU JINNUL-ASHIQ

© AMEERA ADAM

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

          FREE PAGE 8



 Ilahirin jikin mommy rawa ya ɗauka Aunty lubna ta zaro ido hankali a tashe don ko a mafarki bata taɓa cin karo da wannan mummunan abin da Raihan ta aikata ba. Mommy tana son tunkarar Raihan amma tana gudun hukuncin da za ta zartar a kanta, murya na rawa ta dubi Raihan ta ce, "Raihan lafiya me kike yi haka? Ƙadangare ne fa a hannunki." Raihan da har lokacin idonta jawur suke ta sake kai kallonta kan ƙadangaren hannunta, ta sake saka wurin jelarsa a baki ta cisgeta da ƙarfin tsiya ta kalli saitin da su Mommy suke ta tofar a wurin. Wani irin huci ta fara yi idanunta na sake firfitowa ta ce, "Ɗana yake shirin cinye min don haka dole na hallaka shi." Mommy ta tunkari wurin tana son Raihan ta wurgar da ƙadagaren hannunta amma tsoron abin da kaje ya zo ya hanata. Don a lokacin da take da shekara goma ntana da makamancin ciwon ta ya tashi ta taɓa cirewa wani almajiri ɗan yatsa, a lokacin shi ma zuwa ya yi zai ƙwaci agwagwar malaminsu da ta fito kiwo Raihan da Mommy sun fito daga mota, a lokacin da suka kai ziyara Albasu. Tuno da haka ya sa mommy take son tunkararta amma tana jin tsoro. Daga nesa da ita Mommy ta leƙa fuskarta tana faɗin, "Raihan ki yarda abin hannunki." Cikin wani irin ƙaraji ta nufo wurinsu gadan-gadan da ihu tini ba shiri su Mommy suka fice a guje kowa yana gudun ceton ransa.

Hankali a tashe mommy ta nufi sashen Daddy tana ƙwala masa kira. A bakin ƙofa ta ci karo da shi tana ganinsa ta fara nuna masa hanya tana faɗin, “Alhaji Raihan ce…” Maganarta ta maƙale saboda yadda take sauke ajiyar zuciya. A zabure Daddy ya kama kafaɗarta yana jijjigawa yana faɗin, “Me ya samu Raihan ɗin ki faɗa min tana ina?” Hanya ta riƙa nuna masa tana faɗin, “Tana can ta tsintsinka ƙadangare da haƙoranta.” Da gudu ya nufi hanyar ɗakin Raihan hankali a tashe. Nan take ragowar mutanen da ke cikin gidan suka yi tsilli-tsilli, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci tana cikin matsanancin tashin hankali.
Daddy kai tsaye ɗakin da Raihan take ciki ya tunkara yana shiga ya same ta a cen gefe ta faɗi da alama bata numfashi. Kallon ɗakin ya fara yi saboda yadda jinin ƙadangaren ya ɓata saman carpet ɗin ɗakin, daga gefen hannunta ya hangi gangar jikin ƙadangaren hannunta ya jiƙe sharkaf da jini. A hankali ya ƙarasa wurin ya mirgino da ita yana ambatar sunanta muryarsa a raunace, shiru ne ya ratso a ɗakin babu abin da yake tashi sai karar AC da saukar numfashin Daddy. Tsugunnawa ya yi a gabanta ya tallafo da kanta zuwa kan cinyarsa, murya na rawa ya furta: “Me yake samunki ne Raiha? Me ya sa waɗannan abubuwan suke faruwa da ke?” Kuka ne ya ci ƙarfinsa ya kafa kansa a jikinta yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Daga bakin ƙofa Mommy ce ta shiga jiki a sanyaye, ita kanta lamarin Raihan ya fara bata tsoro. Kusan shekara goma sha biyar kenan suna fama da abu ɗaya, babban tashin hankalin da ciwon kullin gaba yake yi baya raguwa. A sanyaye ta zauna a gefen Daddy ta ce, “Daddyn Raihan.” Ɗagowa ya yi ya dube ta idonsa na ci gaba da zubda ƙwallah, ita ma hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta sa hannu ta share sannan ta ci gaba da cewa, “Ka daina kuka don yanzu babu buƙatarsa a gurbin halin da muke ciki…” Tun bata rufe baki ba Daddy ya katseta da cewar, “Ido yana zubda hawaye ne ba don gangar jiki da ruhi suna buƙata ba, sai don samun sauƙi ga raɗaɗin ƙunan zuciya. A da na ɗauka rashin haihuwa babban masifa ne a gare ni sai ga shi a yau na wayi gari Allah ya bani gudan jinina ga kuma masifar da tafi min rashin haihuwar…” Da sauri Mommy ta rufe masa baki tana girgiza kai ta ce, “Bai kamata ka riƙa furta irin kalmomin nan ba, domin duk abin da ya samu bawa yana daga Ubangiji shi ya fi mu sanin dalilinsa na yin haka.” Mommy ta numfasa sannan ta ci gaba da cewa, “Ya zama wajibi ciwon yarinyar nan a koma yin da Islamic don wannan yana da alaƙa da shafar aljanu…” A razane ya katse ta yana faɗin, “Kina hauka ne? Na gargaɗe ki da ki daina danganta jinina da jinsin aljanu.” Wanna karon mommy ita ma hassala ta yi ta ci gaba da cewa, “Kar ka sake furta kalma ta ƙasƙanci a kaina, don duk taƙamar da kake yi ba kai kaɗai ka haifeta. Raihan ƴata ce idan kai ba za ka nema mata maganin Islamic ba dole ni zan nema mata.” Tana gama maganar ta fice daga ɗakin, Daddy ko a jikinsa tana fita ya ɗauki waya ya kira likitan da ke duba Raihan, zayyana masa komai ya yi sannan suka yi sallama ya ci gaba da zubawa Raihan ido yana tunane-tunane a zuciyarsa.

Lokacin da Macijiyar ta ɓace daga ɗakin Kabiru, daga gefen hagunsa ya fara jin wani irin gurnani irin na riƙaƙƙun kumurcin maciji, a hargitse ya sake miƙewa yana kalle-kalle bakinsa na furta Amanarrasulu don a tunaninsa macijin ne zai sake bayyanar masa. Ya jima yana jin wannan gurnanin daga baya ya ji shiru komai ya ɗauke daga dodon kunnensa, daga jikin hannun rigarsa wata fata ya ga ta kwakkwaɓo irin saɓar fatar maciji wacce yake yi. Da sauri ya ɗago ta cikin tashin hankali don lamari ya fi ƙarfin tunaninsa, ido ya zurawa gwiwar hannunsa ta wurin da fatar ta faɗo ya ga wurin ya sake yin sheƙi tamkar bayan maciji. Kwalla ce ya ji ta zubo masa saboda duk wanda ya lura da halin da yake ciki ba zai taɓa zama a kusa da shi ba, kallo ɗaya za ka yi wa jikinsa ya firgita ka don bambamcinsa da maciji kai, hannu da ƙafafuwa. A hankali ya ƙarasa wurin buhun kayansa, nan take ya fara zazzagewa yana birkito kayan da zai saka don ya rufe jikinsa. Sanin kansa ne ko masu aikin gidan suka fahimci halin da yake ciki zamansa a cikin gidan ya ƙare balle kuma a ce Alhaji ya lura da yadda surar jikinsa ta koma. Sai da ya tura ƙofarsa ya rufeta ruf don kar wani ya turo, sannan ya tuɓe rigar jikinsa da yake mai gajeren hannu ce. A jikin mudubin ya tsaya yana ƙarewa jikinsa kallo fatar jikinsa ta koma sak irin ta maciji, wani hawayen ne ya sake gangaro masa ya sa hannu ya share sannan ya ɗauko wata tsohuwar rigar shadda mai dogon hannu, ya ɗauko wani tsohon mayafinsa da wanda ya gada a wurin mahaifiyarsa ya naɗe wuyansa da shi. A jikin bango ya jingina a fili ya fara magana cikin karyewar zuciya, "Allah sarki Baffajo ba don rashin lafiyarka ba, da babu abin da zai hanani barin wannan gidan, don da alama wannan ba wurin zama ba ne." Kabiru ya ɗaga hannu sama ya ci gaba da cewa, "Allah ka bawa Baffajo lafiya, da yardar Allah sai na bar gidan nan don na nemawa kaina lafiya." Daga gefensa ya ji an bushe da dariya, yana juyawa ya hangi matashiyar budurwa tana tsaye tsirara babu kaya a jikinta. Hannuwa biyu ta wara masa tana faɗin, "Ina da hanyar da zan kawo maka mafita matuƙar za ka bani dama." Kabiru ya kauda kansa gefe yana faɗin, "Wa'iyazubillah." Ɓangaren da ya juya fuskarsa ta sake komawa tana faɗin, "Indai akan matsalar abin da ya faru da jikinka ne zan warkar maka da shi matsawar za ka bani haɗin kai." Kabiru ya ɗago da kansa yana shirin yi mata magana, karaf idonsu suka haɗu wuri ɗaya nan take ya ji tsigar jikinsa na tashi.  Da ƙyar ya iya saita kansa sannan ya furta, "Ki taimaka min ki raba ni da wannan fatar macijin, ki gaya min me kike buƙata daga wurina yanzu na aiwatar miki?"


 Duk wani shige da fice da su Mommy suke yi akan idon Mama Uwani, lokacin da ta ji labarin abin da ya faru ta shiga tashin hankali don ta san wannan abin da Raihan ta aikata baya daga cikin abubuwan da take saka Raihan tana aikatawa. Fitowa ta yi ta fara kaiwa da kawowa nan take wata dabara ta faɗo mata, sai da ta shige ɗakinta da yake babu kowa a ciki sannan ta ɓace daga ɗakin. A lokacin da ta ɓace Dr Hamza yana gidansa ya gama shiri don zuwa gidansu Raihan, Huzaifa na zuwa da ya ga haka don kar ya kawi masa matsala ya bige shi a kan gado nan take bacci ya yi gaba da Dr Hamza. Cikin siffar Dr Hamza ya kira lambar Daddy bugu ɗaya kawai ya yi ya ɗauka, a gaggauce Daddy ya furta, "Dr ka ƙaraso ne?" Huzaifa da ke ɗauke da surar Dr Hamza ya amsa masa, nan take Daddy ya bashi umarni da ya shiga. Daddy da Huzaifa a harabar gidan suka haɗu, Huzaifa sai murmushi yake ƙasa-ƙasa don ko ba komai ya samu damar da zai aiwatar da abin da yake ransa. Suna shiga Raihan tana nan kwance kamar gawa bata numfashi ko hannunta baya motsawa,  ido ya zura mata yana son sanin musababbin abin da ya sa ta tsinka ƙadangare gida biyu don ko kaɗan babu sa hannunsa a ciki. Yana tsaka da nazari ya riski muryar Daddy yana faɗin, "Dr don Allah ayi wani abu ciwon nan sai ƙara gaba yake yi." Huzaifa ya miƙe tsaye yana zare gilashin idonsa, ya yi jim kamar wanda yake damuwa sannan ya fara magana, "Gaskiya yanayin ciwonta ya fara bani tsoro Alhaji, amma abin da ya fi akwai wani abokina a India ina tunanin sai an fita da ita, amma a yanzu zan yi bakin ƙoƙarina na ga ta dawo daidai kafin wani lokaci. Amma idan ba shawo kan matsalar aka yi ba lamarin zai rinƙa yin gaba, tun da sannin kanmu ne a da ciwonta bai yi tsanani haka ba." Daddy kamar jira yake ya ce, "Hakan ma ya yi min daidai, abin da ya sa ma ban sake tunanin fita ba saboda ka san ba irin yawon da ba mu yi ba tun Raihan tana ƙarama."

Hamza yana shirin yin magana Inno ta turo ƙofa tana tafe Goggo na biye da ita, Inno cike da faɗa tana faɗi:

“Saboda Allah haka kawai ace duk wani tashin hankali bai faru ba sai a ranar da Ƴata Hasiya ta kwanta dama, ina dalili yarinya sai rikiɗa take kamar wahainiya. To Allah ya sani idan ban watsa mata albarka ba Mamman mai ƙawa’idi bai haife ni ba, ku bar ni yau ko ni ko Rihanu a gidan nan.” Daddy ya waiga wurin Inno da niyyar zai yi magana, suna gano halin da Raihan take ciki da sauri su goggo suka yi baya cike da tashin hankali. Goggo ta dafe ƙirji jikinta sai tsuma yake yi kaɗan ya rage fitsari bai zubo mata ba, ta nuna wurin da Raihan take ta fara faɗin, “Laƙadi ja’akum yau na shiga uku. Allah ya sani duk garin Albasu babu mayya ko guda ya aka yi aka samu maita a zuri’ata, a’a wannan lamarin dole akwai ayar tambaya wallahi idan Raihanu bata shiga ƙungiyar asiri ba Na koma Albasu a ƙafa.” Huzaifa ya waigo wurinsu yana faɗin, “Iya don Allah ku yi shiru ina kan Patient bana buƙatar hayaniya.” Inno ta riƙe haɓa saboda takaici don gani take abin nasa kamar har da cin fuska, ƴarta ta mutu ba a yi zaman makoki yadda ya kamata ba kuma a kawo mata maganar Patient. A zuciye ta ƙarasa gaban Huzaifa sai da saita daidai fuskarsa ta wara hannunta a kai tana faɗin, “Ƙaniyarka ka ji, fitsararre kana fama da fuska kamar teba.” Huzaifa ya kalli Inno a zuciyarsa yana ayyana idan da ya ga dama wurgi ɗaya zai yi da ita ta baje a ƙasa. Bai dawo daga tunani ba ya ji ta sake nuna shi da yatsa tana ci gaba da cewa, “Kai baƙin munafuki ka gaya min idan da ƴarka ce ta musu waɗannan masifun suke faruwa me za ka yi?” Daddy ya zagayo ta wurinta yana cewa, “Inno don Allah ki yi haƙuri shi fa wannan babu ruwansa a ciki.” Goggo ta leƙa fuskar Huzaifa tana kwaɓe baki ta ce, “Akan wannan baƙin munafukin kake shiga gaban mahaifiyarka?” Ta waiga wurin Huzaifa ta ci gaba da cewa, “Wallahi ka fito ka gaya masa gaskiya ko na watsa maka albarka, ka san dai ciwon Yarinyar nan bana mai jan kunne ba ne.” Huzaifa ya dubi Daddy kamar abin bai dame shi ba ya ce, “Alhaji a kawo min ruwa.” Daddy na jin haka da sauri ya fita daga ɗakin, yana fita Huzaifa ya warto su Inno a hannu ya matse su wuri ɗaya. Kamar waɗanda aka naɗe su da igiya aka ɗaura haka su Goggo suka ji, suna shirin yin ihu bakinsu ya yi musu nauyi. Sai da ya yi hajijiya da su sannan ya watsa su can gefe kamar kayan wanki, zannuwa da ɗankwalen su Inno tuni suka maƙale a saman fanka.

  Lokacin da Raihan ta faɗi a lokacin ne Abar bauta ta bada umarnin ga Raihan da ta kawo mata ziyara, nan take ruhinta ya fita daga jikinta zuwa tsibirin da ƙungiyar asirinsu take. Tana zuwa ta russuna ta yi gaisuwa ga Hatsabibiya, a take ta turɓune fuska ta dubi Raihan tana faɗin, "Mun aika kiran gaggawa ne don Abar bauta na buƙatar ku sha jinin mai naƙuda tare da ke, kuma yau ita ce ranar da za a yi miki wankan tsarki dole ke ce za ki kawo mana jinin da za mu sha daga jikinki, Muna buƙatar jinin mahaifiyarki daga yau zuwa gobe idan ba haka ba Abar bauta za ta iya yi wa danginki ɓarna." Ruhin Raihan wata irin zabura ya yi da jin wacce aka ce ya kawo daga cikin danginta, sai dai hakan bai hanata amincewa da buƙatarsu ba. Cikin girmamawa Raihan ta russuna tana faɗin, "Fansar Mahaifana yana gare ku na baku wuƙa da nama, mai naƙuda a ko'ina take zan kawo mana ita yanzun nan." Tana gama maganar ta bi ta iska ta fice daga tsibirin. 

Ruhin Raihan na fita bai tsaya a ko’ina ba sai cikin wani babban asibiti, kai tsaye daƙunan majinyata ta fara shiga har za ta fice ta hango wata tsohuwa da alama tana jin jiki, a kan ruwan cikinta ta dira har ta kafa bakinta za ta tsotsi jini majinyaciyarta ta ƙaraso gabanta tana karanta mata ayatulkursiyyu tana tofa mata saboda tuni sun samu bacci ya ɗauketa, ta karanta mata addu’a saboda ita ma bacci take son yi. Da sauri Raihan ta tashi daga kanta ta matsa gefe tana sauke numfashi, daga can gadon ƙarshe ta hango wata mara lafiya bata jinkirta ba ta hau kanta tuni ta kafa bakinta a kanta ta fara zuƙar jini. Nan take jikin matar ya rikice ganin haka ya sa majinyaciyarta kiran nurses, sun kai mutum huɗu a kanta duk yadda suka kai ga bakin ƙoƙarinsu abin ya ci tura, nan take rai ya yi halinsa. Raihan na ganin haka miƙe ta fice daga ɗakin kai tsaye ta wuce can ɗakin haihuwa. Raihan na shiga ta hangi mata kusan uku masu naƙuda, a kan idonta ɗaya ta haihu ta cikin mutum biyun ta dira a gadon ta tsakiya. Tana niyyar kafa kanta a ƙirjinta daga bayanta ta ji an ce, “Jinin Matata ya fi ƙarfinki.” A zabure ruhin Raihan ya waiga don ganin wanda ya dakatar da ita ga abin da take shirin aiwatarwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button