DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Share Fisabilillah????
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
© AMEERA ADAM
Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.
FIRST CLASS WRITER’S ASSO…
LAST FREE PAGES 10
Ilahirin jikin Mommy ban da karkarwa babu abin da yake yi saboda tsananin tsoro, firgici da tashin hankali. A takure take a ƙuryar gado ta sunkuyar da kanta ƙasa saboda tozali da ta yi wata shirgigegiyar mummunar hallita, girman hallitar ta zarce goggon biri ga wasu irin ƙwala-ƙwalan idanu da suka zazzago kamar za su faɗo ƙasa. Bakinta ban da fiƙoƙi babu komai a ciki sai ƙaton hancinta mai ƙofofi takwas, tare da manyan ƙahunhuna guda biyu. Sautin takun Hallitar kan iya nakasta dodon kunne don haka Mommy ta sa hannuwa biyu ta toshe kunnenta da take jin sa kamar zai tarwatse, Hannuwan hallitar kama suke da ƙafafuwan doki don haka a duƙushe take tafiya rafkeken kanta shi ne a gaba. Jin shirun takunta ya sa Mommy ta ɗago da kanta a zatonta ko hallitar ta ɓace daga wurinta, sai dai tana ɗagowa suka haɗa ido da hallitar nan take ta hango Raihan maƙale a hannun hallitar tana kuka tana miƙawa Mahaifiyarta hannu, jikin mommy har rawa yake yi ta yunƙura don zuwa wurin hallitar tana faɗin, "Don Allah ki bani ƴata ita kaɗai na mallaka karki hallakata, Hallitar ce ta fara ja da baya tare da Raihan ta fara yunƙurin kai kan Raihan zuwa bakinta don ta laƙumeta, da sauri Mommy ta yunƙura cikin tashin hankali ta furta, "Raaaaihaaaaan."
(Allah sarki Uwa kenan???? Duk tsanani Mahaifiya ba za ta so ganin abin da zai cutar da Ƴarta/Ɗanta ba.)
Firgigita Mommy ta farka daga mummunan mafarkin da take yi, har lokacin da ta farka jikinta ban da rawa babu abin da yake yi. Da allon gado ta jingina a hankali bakinta na furta Ayatulkursiyyu don ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin ba. Raihan na gabda da yankar ɗan yatsan mahaifiyarta ta ji wani irn turiri ya yo kanta da sauri ta ja da baya don kaɗan ya rage bata ƙone ba. Farkawar da Mommy ta yi ba ƙaramin ɓata mata rai ya yi ba don ta yi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta aiwatar da abin da yake tafe da ita. Daddy ne ya ajiye takardar hannunsa ya ɗago yana kallon wurin da Mommy take ya ce, “Lafiya dai Mommyn Raihan na ji kina ambatar sunan Raihan cikin dare.” Mommy ta yunƙura da ƙyar jikinta gabaɗaya a sanyaye yake ta zauna a kujera mai kallon ta Daddy ta ce, “Daddyn Raihan wani mummunan mafarki na yi akan Raihan, ina jin tsoro matuƙa kar wani abu ya faru da ita. Maganar gaskiya ina tunanin babu shaiɗanu a lamarinta kuwa, kana gani ƙa’ida bana iya kwanciya ba tare da alwala ba kuma addu’a bakin gwargwado ina yi amma idan mummunan mafarki na tashi yi sai na da yarinyar nan a ciki…” Daddy ya yi murmushi sannan ya katseta da cewar, “Zainabu kenan, duk fa abin da kafi sawa zuciyarka yana tare da kai. Ba tun yau ba na sha gaya miki ki bar danganta ciwon yarinyar nan da wasu shaiɗanu, ki gaya min Raihan ina take zuwa da za ta kwashi shaiɗanu? Ƴarmu a killace take ban da makaranta tana zuwa wani wurin? Karki manta silar ciwon yarinyar nan tun bata fi shekara biyar a duniya ba muka wayi gari da shi, ta yaya za a ce wai wasu shaiɗanu suna bibiyarta kamar wacce take bin kwararo tana jari bola a kan sharar kasuwa.” Mommy ta yi guntun tsaki tana sauke ajiyar zuciya ta ce, “Na rasa ya akayi idonka ya rufe haka, kana tunanin shaiɗanu sai a waje ake samun su Daddyn Raihan? Ganin su muke yi da za mu shaida kamanninsu? Idan a baya ta wayi ido da ciwo shin muna da lasisin da za mu tabbatar da cewar babu haɗin jinnu a jikinta…” Daddy ya ɗaga mata hannu da cewar, “Zainabu ni da ke muka haifi yarinyar nan, don haka ki nema mata maganin Aljanu tun da so kike ki jawo mana wata masifar muna fama da wannan, shi kenan ki sakar min mara na yi fitsari.” Daddy ya ƙarasa maganar a fusace yana tattara kayan gabansa, ya miƙe ya wuce kan gado, jiki a sanyaye Mommy ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala sannan ta saka hijabinta ta nufi ɗakin Raihan don zuciyarta ta gara amincewa ta bari har gari ya waye, a hankali ta fara sauka daga bene sai dai duk taku ɗaya idan ta yi sai ta ji kamar ana bin ta a baya don sai ta ji takun tafiya, sai da ta kusa sauka daga bene ta yi ƙarfin halin juyawa amma wayam babu wanda ta gani. Idanunta ne suka sauka a kan agogon bangon da ke jikin bango wanda ya yi nuni da ƙarfe biyu da rabi na dare, wucewa ta yi hanyar da za ta sadata da ɓangaren su Raihan don gabaɗaya sashensu ɗaya idan aka cire sashen Daddy da yake ɓangarensa daban, a hankali wata sanyayyar iska ta fara kaɗawa mai haɗe da walƙiya tun iskar na kaɗawa kaɗan-kaɗan har ta fara ɗaga labulaye, ƙofofin ɗaki da na window suka fara rufewa da buɗewa a ƙarfi, da sauri Mommy ta fara waigawa don har lokacin bata daina jin alamun takun tafiyar da ake bin ta a baya ba. Tana cikin tafiya ta ga ƙwan fitilar ya fara ɗaukewa yana kawowa, ba shiri ta fara lalube har ta samu ta taɓa jikin bango ta ci gaba da tafiya a jikin bango. Daga bayanta ta ji ƙarar fashewar kwalba tuuuush, a firgice ta fara lalube tana ƙwalawa Daddy kira don iya tsoro ta gama tsorata uwa uba ga shi har lokacin bata daina jin takun tafiya a bayanta ba. Ƙwan fitilar ne ya tsaya cak ya daina ɗaukewa, mommy ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba da tafiya a gaggauce cikin sauri. Tana zuwa ta wurin windon da ya fita ta harabar gidan ta hango wata matashiyar budurwa a zaune ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, da mamaki Mommy ta tsaya tana kallonta sai jikinta ya fara bata kamar Raihan ɗinta don kusan yanayin jikinsu ɗaya, hatta doguwar rigar baccin irinta Raihan ce. Gashin kan yarinyar a barbaje yake ya rufe fuskarta ta yadda ba kya iya ganin ainihin fuskarta.
Duk abin da yake faruwa tsakanin Raihan da Mommy Abar bauta tana kallo a cikin Kogon dutsen ƙungiya, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi da ganin Mommy na son bata matsala ba. Abar bauta na ganin Mommy ta fito don zuwa ɗakin Raihan ta yi wa Raihan magana da cewa, “Ki hanzarta domin samun nasararki, a yanzu a wanni ne kaɗai suka rage miki don samun ci gabanki. Mahaifiyarki za ta fita ki yi ƙoƙari jan hankalinta zuwa harabar gidanku, sauran aikin ki bar min komai a hannuna ki dawo min da ƙashin bayan mahaifiyata don sauran aikin yana gare ni.” Raihan da ke biye da a bayan Mahaifiyarta ta furta, “Biyayya gare ki ta zama wajibi fansar iyayena na gareki ya abar bauta.” Raihan na rufe baki ta ci gaba da bin bayan Mommy, tana zuwa ta zauna a harabar gidan kamar yadda abar bauta ta tsara mata.
Alhaji ƙarami ba ƙaramar azaba ya ci a hannun kunamun nan ba, sai da suka ga ya daina motsi sannan suka dakata da azabtar da shi, sakamakon umarnin da uwar ɗakinsu ta basu. Daga wurin da yake Dodon tsafinsu ya ƙarasa cikin takaici don ba ƙaramin haushi ya ji ba ganin ƴan wata ƙungiyar sun azabtar da ta su ɗan ƙungiya ba. A fusace ya kafawa Alhaji Ƙarami haƙora tun yana masa magiya har rai ya yi halinsa, sai da ya tabbatar da baya numfashi ya ɗaga shi yana faɗin, “Da ka mutu ta sanadin wasunmu gara mu ƙarasaka da hannunmu.” Kusan lokaci ɗaya Alhaji Ƙarami da matarsa suka Mutu, Likitoci na kan matarsa ta jima tana wani irin fisge-fisge daga ƙarshe ta ce ga garinku nan.
Kabiru yana tafe cikin zuciyarsa yana saƙa da warwara har ya ƙarasa cikin gidan, a lokacin da ya je ƙofar gidan a buɗe ya samu gate ɗin don haka yana turawa da ya shiga ya wuce ɗakinsa da yake a bakin ƙofa yake idan baka lura ba ma ba za ka san ya fita ba. Yana shiga ya ajiye buhun kayansa ya fito ya ɗaura alwala ya gabatar da sallar Isha'i ya yi shafa'i da wuturi . Ya jima yana addu'a da kaiwa Allah kukansa akan mummunar ƙaddarar da ta same shi daga ƙarshe bayan ya idar ya zauna ya fara tilawar alƙur'ani. Ya kusa awa guda yana karatu sai da ya gama sannan ya fito harabar gidan da babu mutane kowa ya kama gabansa, sai da ya kira Daddy a waya ya tambaye shi ko zai ƙara fita ya tabbatar masa da ya rufe gidan babu inda za shi kuma baƙi duk masu tafiya sun tafi.
Sama-sama Mommy ta fara jin kamar ana ambatar sunanta, har ta yi kamar ta wuce ta ji ba za ta iya giftawa ta bar yarinyar da take ji kamar Raihan ɗin ta ba, don tuni zuciyarta ta fara ayyana mata ko ciwon Raihan ne ya tashi ta buɗe ƙofa ta fita harabar gidan ta zauna. Kai tsaye ta nufi hanyar da za ta sada ta da ƙofar fita, sauri-sauri ta fara yi har ta samu nasarar zuwa barandar harabar waje. Kamar wacce ake fisga haka Mommy ta fara jin zuciya da gangar jikinta na azalzalarta zuwa wurin da wannan matashiyar budurwar take bakin ta na furta, “Hasbunallahu…” Ta fara tunkarar wurin gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, lokaci ɗaya ta ji wani irin tsoro ya mamaye ta sakamakon jin kukan wasu irin tsuntsaye na tashi a saman kanta. Ta maza ta yi ta ci gaba da takawa har ta ƙarasa wurin da Raihan take zaune, Mommy ta fara ƙoƙarin kai hannu za ta taɓa gadon bayanta tana kiranta, “Raihan!” Shiru ne ya biyo baya ba tare da ta amsa ba, Mommy ta sake sunkunyawa ta ce, “Raihan.” A haukace Raihan ta ɗago tana bin Mommy da kallo, da sauru Mommy ta yi baya sakamakon tozali da ta yi da mummunar hallita. A madadin da ga fuskar irin ta bil’adam kamar yadda gangar jikinta ya nuna sai gani ta yi ta yage mata baki mai kamar na kura, cike suke da manyan haƙora da fiƙoƙi ga hancinta tamkar na kare haɗe da idanu jawur kamar garwashi. Mommy da ta faɗi can gefe ta fara ja da baya jikinta na rawa, Gadan-gadan Raihan ta fara takawa gabanta don ta bawa Abar bauta damar aiwatar da abin da yake gabanta. Cikin gigita Mommy ta fara karanta duk wata addu’a da ta zo bakinta, tana yi tana kiran sunan Daddy don ya kawo mata ɗauki. Tana cikin wannan halin sai gani ta yi wannan hallitar da ɓace daga gabanta, da ƙarfin gaske ta ji ana fisgarta kamar za a yagi naman jikinta.