BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

https://chat.whatsapp.com/KQd6gkViAXfKDTv7iWLJpV

FREE PAGE 3

Ƙananan yaran da aka bari a ƙofar ɗakuna ban da kiran sunayen iyayensu babu abin da suke yi, ƴan madaidaitan cikinsu waɗanda suka fara sanin ciwon kansu ne suka samawa kansu mafita suka nemi maɓoya. Sauran marasa wayo sai ihu suke suna buga ƙofar ɗakin da iyayensu suka shiga. Yaya Idi saboda firgita bai san lokacin da ya wuce can ƙarshen gadon Inna Furai ba, mutumin da ko falon Inna Furai baya iya ƙwaƙwaron tsayuwa, a cewarsa yana Yayan miji haka sam bai kamace shi ba. Rabon shi da shiga ɗakin Inna Furai tun wata doguwar rashin lafiya da ta yi sama da shekara goma, lokacin da ya je dubata amma a wannan ranar shi ne har tsakiyar gadonta. Ban da ɗigar da gumi babu abin da gemunsa yake yi saboda tashin hankali. Lantan can ƙarƙashin gado ta shige ban da ƴan idanuwanta babu abin da kake iya hangowa, ta ƙwale kai a jikin ƙarfe gado ya fi sau biyar duk don ganin ta ɓoye kanta ba tare da an hangota ba bare tawagar fatale su kawo mata farmaki.

Inna Furai zaman ƴan bori ta yi zanin jikinta ya jiƙe sharkaf da fitsari don gani take wannan zuwan da Fatalwar nan ta yi zuwanta ne, don a ganinta saɓawa umarnin fatalwar da tayi na sake shayar da ƴaƴanta ne ya sa, fatalwar nan ta yi dirar mikiya domin ƴan sama jannati su tafi da ita. Badariya tuni ta ƙwaƙume Yaya Idi da ke gefenta, duk yanda Badariyya ta kai ga jin ƙyanƙyamin gemun namiji sai ga gumin gemun Yaya Idi na ɗiga a sai tin fuskarta. Gabaɗaya mutanen cikin ɗakin ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Ita ma Dubu tuni ta bi yarima don kar wani ya yi saurin gano shirinta saboda ko kaɗan bata son ta samu matsala, ta tabbata muddin ta ci gaba da razana su babu wanda zai ƙara koda nan da kwana biyu ne.

Bayan wasu ƴan mintuna Yaya Idi ya ɗago sai a lokacin ya lura da wacce take gefensa a maƙale da shi suna haɗa ido ya watsa mata harara, da sauri ya matsa gefe yana cewa, “Subhanallah! Astagafirullahi wa’atubu’ialhi ke matsa gefe matsa-matsa” A razane ita ma ta ja baya tana yamutsa fuska alamar ƙyanƙyami, don ita kanta bata san lokacin da ta ƙwaƙume Yaya Idi ba don ta san kowane ne shi. Ya kalli Dubu da ke can bakin ƙofa da yake ita ce ƙarshen shiga sannan ya ce, “Ke Dubu wai da gaske kike kin ga Fatalwar Mamman?” Dubu ta yi wani fakare sai kawai ji suka yi ta rushe da wani irin kuka har tana wani furjin yawu kamar wata ƙaramar yarinya.” Yaya Idi ya yi zuru yana kallonta a zuciyarsa yana fatan kada Allah ya sa ta tabbatar da abin da ta faɗa da farko. A ƙagauce Yaya Idi ya sake cewa kamar zai yi kuka, “Ke Dubu wannan kukan ba ke kaɗai za ki yi shi ba ki sanar da mu musan halin da mu kanmu muke ciki.”

Dubu ta tsagaita da kukan sannan ta fara cewa, “Na ga fatalawar Baffa ido da ido don har cewa suka yi za su fara ɗaukan Innarmu da Innar su Sabi’u. Kuma wai sun ci alwashin duk wanda ya haure shekara Arba’in a gidan nan sai sun naɗe masa ƙafafuwa kamar alkaki.”

Tashin hankali wanda ba a samasa rana. Inna Furai na jin ance za a tafi da ita da Yaya Babba hantar cikinta ta sake kaɗawa gumi ta ko’ina sai keto mata yake yi. Don har kusan suman zaune ta yi saboda waɗansu irin taurari ta rinƙa gani suna yi mata gizo a tsakar idonta. Tun daga abin da Dubu ta faɗa babu wani abu da Inna Furai ta sake fahimta a ƙwaƙwalwarta, don sama-sama ta rinƙa jin wani yuuuuuu a zatonta wannan abin da ta fara ji ƴan sama jannatin ne suka fara kawo mata farmaki. Cikin fitar hayyaci Inna Furai ta fara cewa, “Ikon Allah Ikon gaske! Kai Auwalu kana ina ne? Ke Larai don Allah a cikinku wani ya ɗauke ni ko a kafaɗe ya fice da ni tun fatalwa bata tafi da ni. Auwaluna! Auwaluna na ci burin ganin Ɗanka amma da ƙyar idan zan samu wannan damar ka kawo mini Yahanasu idan ya so mu tafi da ita ko da Fatalwar sun tafi da mu na yi mata raino a cen barzahun idan ta haihu.” Dubu juyawa ta yi ta rinƙa ɓaɓɓaka dariya ƙasa-ƙasa saboda ta lura tuni Inna Furai ta riga da ta fita hayyacinta, don fitsari ma ta yi ya kai sau uku daga shigarsu ɗakin.

Lantan tun da ta ji labarin naɗe ƙafafuwansu kamar Alkaki, ta sake firgicewa wani buhu da ke gefenta ta fisgo wanda yake ɗauke da dawa kusan kwano biyu, bata bi ta kan dawar ba ta watsar da ita a gefe ta fara tura kanta a ciki. Don yanda Lantan take ji da ace akwai hanyar da za ta fitar da ita daga cikin ƙarƙashin gado ta tuni ta fice ta yi hanyar zariya. Babban abin da ya fi ɗaga mata hankali shi ne zancen naɗe ƙafafuwansu da ta ji ance Fatalwa za ta yi mayar da su kamar alkaki. A duniya babu abin da ta fi so da ƙauna a jikinta kamar santala-santalan ƙafafuwanta, wannan ya samo asali ne sakamakon kirarin da marigayin mijinta yake yi mata akan Doguwa mai tsawon alheri tsawo rabin kyau ƴar fillo.Wannan kirari ba ƙaramin baƙanta zuciyar Lami kishiyar Lantan yake ba saboda ita gajeriya ce, kuma hatta bayan rasuwar mijinsu idan wani abu ya haɗo Lantan da Lami haka za ta yi ta hura hanci tana yi wa Lami habaici. To kuwa idan aka mayar da ƙafafuwanta kamar Alkaki ai ta shiga-uku don ta tabbata idan aka naɗe mata ƙafafuwa, ta san ko tsahon turmin gidansu ba za ta kai tsayi ba.

Lantan bata gama tunani ba ta riski maganar Dubu cikin kuka tana sake cewa, “Kuma har ce mini ya yi a cikin ƴan uwan sa zai aiko a tsotsewa wani ko wata roman da ke cikin Ƙwaƙwalwarsu. Saboda gonar Mahaifinsu da suka taɓa danne masa.”

Lantan na jin haka ta ci gaba da karanto duk wata addu’a da ta san ta taɓa biyata a bakinta. Saboda ta san badaƙalar da suka shuka akan gonar Mahaifinsu. Hatta kalmar larabci indai Lantan ta santa a baki haka za ka ji tana maimaitata ya fi sau goma. Ta yi kiran sallah da tayar da iƙama ya fi sau biyar, idan ta biya addu’ar shiga banɗaki sai ka ji ta fara, “Labbaikallahumma Labaik” Idan ta dire sai ka ji ta sake cewa, “Hayya’alal salah” haka ta rinƙa yin addu’a don neman kariyar Ubangiji, amma addu’a har da ta shiga abin hawa haka ta rinƙa maimaitawa. Tana gamawa sai ka ji ta sake cewa, “Walaƙadkarramna bani adama…” Bata iya direwa sai ta ƙara kamo wata kalmar hatta sunayen Annabawa da Sahabai waɗanda ta san sunansu haka ta rinƙa biyawa.

Ana cikin haka suka jiyo muryar Baba Munkaila a bakin ƙofar Inna Furai yana cewa, “Lafiya kuwa mutanen gidan nan tun daga babban zaure nake sallama shiru ga ƙananan yara suna ta kuka.” Ya ƙarasa maganar yana bubbuga ƙofar ɗakin, da ƙyar Yaya Idi ya ta so ya fara ƙoƙarin zare sakata.

A can ɗakin Yaya babba dirama ake yi da ita akan dole sai an barta ta fito wai sai dai Fatalwar ta ɗauketa ita da Dubu don ba za ta iya jure rashin Dubu ba. Hadiza da ke riƙe da kubar ɗakin ta ce, “Inno don Allah ki yi haƙuri ki zauna na san Dubu ba za ta zauna a waje ba, kuma ni fa gani nake sharrin shaiɗan ne amma babu wata fatalwa.” Yaya Babba ta sake share ƙwalla ta ce, “Kaico rayuwa ban taɓa sanin haka zuciyarki ta ƙeƙashe ba Dije, wannan wacce irin falsafar rashin imani ce? Kowaccenku na riƙe da Ɗanta amma ni kun hanani nemo Marainiyar Allah. An ya kuwa Dije?” Hadiza babu yanda ba ta yi ba amma fir Yaya Babba ta kafe, don ban da ruwan hawaye babu abin da take yi. Hadiza na buɗe ƙofar Yaya babba ta fice da sauri tana ƙwalawa Dubu kira. Da sauri Dubu ta taho aikuwa caraf Baba Munkaila ya damƙi hannunta bayan ya gama jin labarin abin da aka bashi dangane da fatalwa. Yana fisgota ya zuba mata ranƙwashi a ka yana cewa, “Wallahi sam ban yarda da abin da wannan shaiɗaniyar yarinyar nan ta faɗa, ke a gidan uban wa kika ga fatalwa har ta baki saƙo?” Yaya babba na ganin haka ta ƙarasa wurin ƙafar Baba Munkaila ta yi zaman dirshen sai kawai ta fashe da kuka. Gabaɗaya ido ya dawo kanta, Baba Munkaila ya sassauta murya ya ce, “Inno lafiya kuwa?” Yaya Babba ta ɗago ya dubi Mukaila ta janyo hannunsa ta ce, “Ka dake ni kawai Munkaila na ce ka dakeni ka huce takaici. Kaga sai na tabbatar da falsafar rashin mutumcinka yanda ya kamata.”

Baba Abubakar da shigowarsa kenan ya hango taron jama’a yana zuwa ya ga Mahaifiyarsa ce mutane ke zagaye da su. Har ƙasa ya russuna yana tambayar Mahaifiyarsa. Yaya Babba ta share hawaye ta ce, “Allah ya yi maka albarka Garba! Don Allah ka ga ya mini me na tsare wa Munkaila da Dije? Munkaila dai ya fi jin haushina. Garba ka gaya mini wacce tsiya suke tsinana mini, bayan Allah da ma’aiki waye gatana wa zai tsunduma ni a aljannah?” Baba Garba ya jinjina kai ya ce, “Inna wai me yake faruwa ne? Me suka yi miki?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button