BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

“Tsoronsu kake ji da zan yi magana ka amsa ƙasa-ƙasa. A cikinsu ka gaya mini akwai Malam ko kuma akwai ni. Ban da Allah da Manzonsa wa yake ƙaunata, ya hore mini lafiya da abin da lafiya za ta ci?” Yaya Babba ta yi maganar cikin ƙunan rai. Baba Abubakar ya ce, “Ayi haƙuri Inno”

Yaya Babba ta zuba hannuwa biyu tayi tagumi ta ce, “Garba ni wace ce a wurinku?” Baba Abubakar ya bata amsa, “Ke Mahaifiyarmu ce Inno”

“Idan na tsinewa su Munkaila wa billahi sai ta ka kama su ko ba haka ba?”

“Inno abar maganar tsinuwa don Allah.” Baba Abubakar ya faɗa cikin sanyin murya. Yaya babba ta kuma rushewa da kuka sannan ta ci gaba da cewa, “Don Allah mecece tsinuwa da zan tsinewa ƴaƴan cikina. Idan na tsine musu na ɓalɓace duniya da lahira ko ina da wasu ƴaƴan bayan ku?” Baba Abubakar ya yi ƙasa da murya ya ce, “Inna don Allah ki yi haƙuri kin ga duk mutane kallonki ake yi.”

Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, “Ka yi mini iyaka da Munkaila ko a hanya ya ganni kar ya nuna ya sanni, balle a lahira ya yi gabas na yi yamma. Haƙƙi ɗaya na san Munkaila yana bina, lokacin da aka yi masa shayi (kaciya) don Allah Garba ka biya shi cinyar kazar da na ci, ko ba za ka biya shi ba Garba?” Baba Abubakar ya rasa abin faɗa sai kawai ya girgiza mata kai. Yaya Babba ta ci gaba da cewa, “Me marainiyar Allah ta yi masa da zai ƙullace ta har ya sheganta mini ita? Don Allah Garba ka tambayar mini shi ta wurin da Dubu ta zama shegiya? Ka tambayi munkaila Ni Indo Kakarta ce shegiya ko matattun iyayenta?”

Baƙin ciki ne ya cika Baba Munkaila domin jikansa ya ba shi abin da Dubu ta faɗa ba gaskiya bane saboda ya san wacece ita, amma gani yake meye laifinsa don yana son hukunta Dubu domin ta faɗi gaskiyar magana. Gani yake idan ya yi haka shi zai kawo musu ƙarshen duk wannan guje-gujen da ake yi. Tun da tun farar safiya ya ji labarin abin da ya faru yake tantama akan Dubu don kowa ya san irin hatsabibancinta.

Wata uwar harara ya watsawa Dubu sannan ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, “Yanzu Inno saboda na hukunta Dubu shi ne ya ɓata miki rai? Tun da haka ne na zame hannuna daga cikin sabgarta shi kenan?”

Yaya babba ta wara hannuwa alamun abin ya mata daɗi ta ce, “Sadaƙallahul azeem! Kana jin me ya ke faɗa ko Garba, dama me Munkaila yake yi wa Dubu? Ka gaya mini waye yake shiga lamuran Dubu bayan Allah da manzonsa idan ba ni ba?” Baba Abubakar ya sake ƙasa da murya ya ce, “To duk na ji wannan Inno amma don Allah ki taho mu tafi ɗaki.”

Yaya Babba ta yi biris da Baba Abubakar tana cewa, “Don Allah ka yi mini iyaka da Dije saboda tsoro nake ku tafi ku bar ni da ita a ɗaki ɗaya, kar a wayi gari ta maƙure ni na mutu har lahira.” Cewar Yaya Babba tana satar kallon Hadiza.

Rass gaban Hadiza ya faɗi da jin kalmar Mahaifiyarta, da sauri ta ce, “Inno ni kuma? Ni ce zan kashe ki?”

“Duk gidan nan babu wanda ya ƙullace ni yake jin haushi kamar Dije dubi irin kallon da take yi mini, haushina take ji saboda na ce ta buɗe mini ƙofa na je wurin Dubu. Don Allah Garba ka gaya mini me na yi mata ko zargina take akan mutuwar mahaifinku?” Sam wannan maganar bata yiwa duka ƴaƴan Yaya Babba daɗi da cikin yanayin rashin jin daɗin maganarta ya ce, “Haba Inno me kike yi haka ne kowa fa a wurin nan ke yake kallo saboda Allah me mutane za su ɗauka jiya-jiya Mahaifinmu ya rasu amma kina wannan abubuwan.” Ya ƙarasa maganar yana dafa ƙafarta.

“Sakar mini ƙafata Garba.” Yaya Babba ta faɗa a hassale. Ba musu ya sakar mata ƙafa. Sai kawai ta miƙawa Hadiza hannu ta ce, “Allah ya jiƙanki ba don kin mutu ba Dije don Allah taimaka min zan koma ɗaki, ko a baƙar zuciyar Munkaila kina ga zai kaini ɗaki?” Hadiza ta girgiza kai tana murmushi, Yaya babba ta ci gaba da cewa, “Don Allah ki ce Garba ya matsa daga gabana ko na fice na bashi wuri.” Gefe Baba Abubakar ya matsa Dije ta samu ta lallaɓata suka shige da Yaya Babba ɗaki. Suna niyyar tafiya daga wurin suka ji ƙarar abu tim! Daga bayansu. Da sauri suka waiga sai gani suka yi Inna Furai ce da ƙaton buhunta tana ja Auwalu shima yana ja wai dole a barta ta fita ta yafewa zaman cikin gidan. Ita ma sai da suka sha fama da ita sosai sannan suka samu ta koma ɗaki. Baba Abubakar ya dubi Dubu yace,

“Dubu ince idan muka je da ke za ki iya nuna mana ta wurin da kika ga fatalwar?” Dubu ta gyaɗa kai suna haɗa ido da Baba Munkaila ya watsa mata harara. Shi kansa Baba Abubakar zuciyarsa raya masa take tabbas akwai wanda yake son tsoratar da mutanen cikin gidan tun da wanda ya mutu ya mutu kenan har abada baya ƙara tashi. Dubu suka tasa a gaba tana gaba suna biye da ita a baya, sai wani ɗari-ɗari take ita Allah dole tsoro take ji.

Zu-gar mutane ne suka yi dafifi don ganin ta wurin da Dubu ta ga Fatalwa da idonta. Ita kuwa hakimar kanta sai ƙara girma yake musamman yanda ta ga mutane kowa ambatarta yake ana jinjina mata bisa ga ƙoƙarinta na tunkarar wurin. Daga can hanyar banɗaki suka hango wasu fararan kaya, daga nan wasu suka fara cin burki, sai kuma hular Marigayi Mai carbi da iska take kaɗa ta sama-sama. Mamaki da ta’ajibi ne ya kama su hatta Baba Munkaila sai da ya zubawa kayan ido, ɗaya tsagin na zuciyarsa na son aminta da abin da Dubu ta faɗa sakamakon kayan da ya gani. Amma yana tuna wace ce Dubu zai ji ya ƙi aminta da komai.

Baba Abubakar ne ya yi bismillah ya ɗebo kayan yana ƙare musu kallo zuwa can ya kalli Dubu yana shirin yi mata magana, sai kuwa ta zabura tamkar wacce aka ɗanawa wuta. Can bayan Zulfa’u ta maƙale tana cewa, “Baba Habu wallahi tsoro nake ji.” Baba Munkaila ya karɓi kayan yana jujjuyawa sannan ya ce, “Amma gaskiya ana raina wa mutane hankali.” Baba Abubakar ya yi gaba yana cewa, “Dole mu san abin yi amma tabbas akwai wata a ƙasa. Da alama wani ne yake son kawo yamutsi amma kowa ya kwantar da hankalinsa komai ya zo ƙarshe.” Baba Munkaila ya hau muzurai yana zare idanu ya ce, “Koma wane ne ni da hannuna zan ci ubansa don na san na gida ne yake aikata wannan abubuwan. Amma duk wanda yake da hannu cikin wannan tafiyar sai na kusa tsinka shi gida uku.” Ya ƙarasa maganar yana yi wa Dubu kallon idan ma ke ce za mu gauraya da ke.

Kafin wani lokaci tuni maganar fatalwa ta fara zaga cikin garin Ɗangwauro, har da masu isar da labarin abin da bai faru ba. Kasancewar kowa da abin da yake ji shi yake idarwa.

            ************

“Dubu ki kwantar da hankalinki idan ma don wannan ne kamar an yi an gama a wurina. Ba dai ni na haifi Garba ba?” Yaya babba ta ƙarasa maganar tana kallon Dubu cikin sigar lallashi.

Dubu ta tura baki gaba tana cewa, “To ai ke sai an gama magana da ke lafiya ƙalau sai kawai daga baya ki sake shawara, gaskiya ni dai ko ki sa mu koma birni gidansa ko kuma ki ce su dawo garin nan wallahi sai mun fi cin daɗi tun da anan me muke ci kamar ba ke kika haifeshi ba.” Yaya Babba ta yi jim sannan ta ce, “Ba zan koma birni ba domin Malam har wasiyya ya bari akan kar mu kuskura mu bar gidan nan to kin ga saɓawa miji haramin ne amma Garba ko ya ƙi ko ya so dole ya dawo gidan nan da zama.”

Baba Munkaila ne ya kawo kai zai shiga ɗakin Mahaifiyarsu amma ya ga mutane sun yi carko-carko a ƙofar ɗaki ya tambaya ko lafiya.

Hadiza ta taɓe baki ta ce, “Inno ce suke shawara da Dubu shi ne ta koro mu waje.” Haushi ne ya ƙara kamashi don ya san duk iskancin da Dubu take yi Mahaifiyarsu ce take ɗaure mata. Ɗaga labulen ɗakin ya yi suna haɗa ido da Yaya Babba ta ce, “Kai Munkaila ka tara mini ƴan uwanka yanzun nan ina son magana da ku!” Kallon Dubu ya yi ya ga ta yi ɗai-ɗai a cinyar Yaya Babba, gudun neman magana ya sa bai tanka ba ya amsa ya fice. Don baya raba ɗayan biyu Dubu ce ta kitsa mata wata maganar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button