BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Zabbin da suka tarwatse wasu daga cikin su hanyar waje suka yi, suna kuka a firgice. Dubu tun da ta ga an ɗauke wuta ta haye katanga ta dira ta bayan gidan. Sai ga ta kamar mumina ta wuce shagon Lamarana ta siyo maganin sauro, da sauran wata hamsin ɗinta. Zuwanta ƙofar gidansu ya yi daidai tashin Baba Munkail kenan yana kaɗa Zabbin da ya ga suna tsalle suna fitowa ɗaya bayan ɗaya. Mutanen wurin ne suka fara taya shi, Dubu na zuwa ta zabga uwar sallama, ta yi haka ne saboda Baba Munkaila ya ganta don ta sake cire zarginta da yake daga kanta.

Cikin masifa ya fara yi mata magana, “Dallah sakarai matsa kina gani zabbina na fitowa sai wani ya ɓace a cikin duhu.” Da sauri ta matsa gefe ta ce, “Baba Munkaila don Allah ara min fitila na kaiwa Inna Maganin sauronta tsoron soro nake.” Ci kanki bai ce mata ba har suka samu suka kame zabbin, ban da masifa babu abin da Baba Munkaila yake yi, don a duniya idan kana son ganin ɓacin ransa cikin gaggauwa ka taɓa masa zabbinsa ko kuma wani laulawar keken hawansa. Yana gaba Dubu na biye da shi sai mutum uku da suke riƙe da zabbin nasa. Faɗa yake ta saki yana cin alwashi ga duk wanda ya buɗe masa Zabbi sai ya yi masa rashin mutumci. Suna shiga tsakar gida Baba Munkaila ya hasko gawar wasu zabbi biyu daga bakin ƙofa. Nan take cikinsa ya bada sautin ƙululululu! Jikinsa ne ya ɗau tsuma wani gumi na keto masa ta ko’ina, watsar da na hannunsa ya yi; ya kwasa a guje.

Yadda jaruman Indiya suke kwasar gudu idan sun yi tozali da masoyansu haka Baba Munkaila ya watsar da zabbin hannunsa ya kwasa da gudu har da wata uwar ƙara yana zuwa ya zube a wurin ya suri Gawarwakin zabbin ya rungume yana sauke ajiyar zuciya mai zafi, haɗe da haɗiyar wani irin yawu mai ɗacin gaske.

Kamar mai shirin yin kuka haka Baba Munkaila ya rinƙa shafa matattun zabbin yana cewa, “Don Allah wanene ya yi mini wannan ɗanyen aikin. Wallahi duk wanda na kama yana da hannu a ciki sai na ci ubansa.” A daidai lokacin Dubu da sauran mutum ukun da ke riƙe da zabbinsa suka ƙaraso. Dubu ta yi tsaye tana kallon yanda gumi ke ɗiga daga jikin Baba Munkaila. Yana ɗagowa ya maka mata duka yana cewa, “Don Ubanki za ki kamo mini sauran ko su ma sai an kashe mini su.” Kamar mai jira haka Dubu ta sheƙa da gudu kamar gaske tana dariya ƙasa-ƙasa. Daga can ɗan nesa Baba Munkaila ya fara hango ƙaramin yaro yana tafe yana jan ƙafar wata ƙatuwar zabuwa, wacce da alama ita ce uwar garken ciki. Salihu yana tafe yana murmushi yana zuwa ganin Baba Munkaila na riƙe da sauran zabbin ya sa ya miƙa masa yana sake yaƙe baki yana cewa, “Baba an ci kaza.” Kusan suman zaune Baba Munkaila ya yi, ya ƙurawa Salihu ido ya ganshi tik ko wando babu. Cikinsa ya yi kurcici sai sheƙi yake da maiƙon abinci. Baƙin cikin ne ya kama Baba Munkaila ya dubi Salihu murya a daƙile ya ce, “Kai a ina ka gano wannan?” Salihu ya juya bayansa ya nuna ya sake cewa, “Baba an ci kaza”

A fusace Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, “A gidan uwarka za a ci kaza?” Salihu ba ƙaramin tsorata ya yi ba don haka ya saki zabon hannunsa jikinsa na rawa. Baba Munkaila ya sake ɓata fuska ya ce, “Waye ya kashe mini zabbi ko kaine?” Tsoro da ganin yanda Baba Munkaila ya ɓata fuska ya sa Salihu bai yi wata-wata ba, ya ce, “Ni ne a cen”

Baba Munkaila zuru ya yi yana kallon Salihu kamar wanda ya yi tozali da sabuwar halitta, ya sake haɗiyar yawu mai ɗaci murya a daƙile ya ce, “Wato kai ka buɗe daga keji suka fito ko?” Salihu ya gyaɗa kai wannan karon har da murmushinsa na ƙarfin hali ya ce, “Ni a Umma ne…” Haushi ya sake kama Baba Munkaila ya ji kamar ya shaƙe wuyan Salihu. Kawai sai ya miƙe ya damƙi hannun Salihu ya juya ba walawa ya cewa mutanen da suka rako shi ciki, “Malam Hamza ga kejinsu ku zuba su a ciki.” Mugun kallo ya watsawa Dubu don Allah ne ya taimake ta ba ta yi wani laifin ba da ragowar fushinsa a kanta zai sauke.

Yadda Baba Munkaila yake fusgar hannun Salihu ba ƙaramin tausayi da dariya zai baka ba, yana zuwa wurin ɗakunan ya fara kwaɗawa Muhsana kina. Sai dai babu motsin wanda ya ji hasalima ƙofar ɗakunan gabaɓaya a rufe suke. Haushi da ya kama shi ya hau buga ƙofofin ɗakuna yana faɗin,

“Wai lafiya kuwa mutanen gidan nan wannan wanne irin abu kuke yi ne.” Wannan bugun ƙofar ba ƙaramin razana Salihu ya yi ba, don haka ya fara tsanyara kuka yana murza idanu tare da wurga tsilla-tsillan ƙafafuwansa. Cike da takaici Baba Munkaila ya tallaƙe ƙeyarsa yana cewa, “Rufe mini baki don ubanka. Shegen yaro mai siffar ƴan ruwa.”

Dukan da Baba Munkaila ya yi wa Salihu ba ƙaramin ratsa kansa ya yi ba don haka ya kuma fashewa da kuka. Lantan da ke cikin ɗaki ta kuma zabura tana cewa, “Innamal A’amalubinniyati…” Sai kuma ta hau gado ta sauko, sannan ta sake cewa, “Sadaƙallahul azeem. Kuna ji fatalwar nan har rikiɗa take yi za ta yaudare mu, mu buɗe mata ƙofa.” Inna Furai da ta yi ɗai-ɗai a ƙasa ta ɗauko wani rawanin Marigayi Mai carbi, ta ƙadandane shi tana numfarfashi ta ce, “Ni dai na san idan da zazzagar amana to babu makawa fatalwar nan koda ta shigo ba za ta illatani ba. Wannan rawanin tun na ranar aurenmu ne wannan kaɗai ya isa shaidata…” Bata ƙarasa sambatun ba suka ji bam Baba Munkaila ya ɓallo ƙofar, ya koma ta ɗakin Yaya Babba ita ma ya ɓalle ta. Nan fa suka yo carko-carko masu ihu na yi masu gudu suma suna yi. Tsawar da Baba Munkaila ya buga ce ta saita nutsuwarsu, yana huci ya nuna Salihu da ke rarraba idanuwa ya ce, “Ina uwar yaron nan?” Tsit suka yi aka rasa mai magana sai Lantan da ke zare idanu ta ce, “Ai Muhsana kam tuni Fatalwa ta daɗe da gamawa da ita…” Da sauri ya katse ta da cewar, “Don Allah Inna Lantana ki rabani da zancen fatalwar nan. Ku duba irin ɓarnar da aka yi mini.” Ya ƙarasa maganar yana haska musu gawarwakin zabbinsa.

Yaya Babba da fitowarta kenan ta zuba kabbara tana cewa, “Kazalika mun ga tabbaci wallahi ya tabbata fatalwa na bibbiyarmu a gidan nan. Dama fa kafin su aiwatar sai da suka faɗi cewar za su fara ta kan dabbo. Don Allah ku kira mini Garba don idan na ƙara kwana a gidan nan ba Mai Jama’a ne ya haife ni ba.”

Ana cikin haka sauran Mazajen gidan da ke zaune a ƙofar gida suka shigo sakamakon Malam Hamza ya sanar da su abin da suka gani. Ganin su Yaya Babba carko-carko a tsaye ya sa su tambayar ba’asi, nan take aka sanar musu Baba Munkaila ya kora musu jawabin zabbinsa. Cikin Baba Auwalu da na Baba Sule kusan lokaci ɗaya ya kaɗa, tuni gumi ya wanke musu fuskoki. Nan fa aka shiga tausar Baba Munkaila akan ɓarnar da aka yi masa sannan magidantan mazan suka ci alwashin ɗaukan mataki a cikin gidan. Baba Abubakar da kansa ya fita ya sanarwa ƴan bijilanti abin da yake faruwa ya basu umarnin kula da gidan tun daga bayan gidan har zuwa cikinsa.

Lantan duk wannan matakin da aka ce za a ɗauka bai yi mata ba, don ta kasa ta tsare akan dole sai ta tafi a daren sai da Baba Abubakar ya lallaɓata sannan ta amince da sharaɗin gari na waye za ta kama gabanta. Hajiya Nafisa na jin haka ita ma ta yi tsalle ta ce washegarin ranar za ta tafi don ba za ta ƙara kwana ba. Gabaɗaya suka ɗunguma zuwa sashen Auwalu da ƙyar can ma aka samu suka buɗe ƙofofi don Muhsana sai da ta suma ya kai sau Uku, da ta farfaɗo idan ta ce ina Salihu? Suna ce mata baya nan take sake zubewa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button