BABU SO HAUSA NOVEL

DUBU JIKAR MAI CARBI HAUSA NOVEL

Duk plan ɗin da ake shiryawa Dubu ta yi fakare tana sauraronsu, kuma zuciyarta ƙal da ta ji kowa ya ce zai koma inda ya fito.

Sai dai suna haɗa ido da Nabila sai ta bushe da dariyar mugunta tun Nabila bata lura ba har ta fara fahimta. Faɗa suka yi kace-kace har Nabila ta cewa Dubu, “Ballagaza ƴar ƙauye.” Buɗar bakin Dubu kuwa ta ce mata, “Ubanki ma ɗan ƙauyen ne kuma kema kin dawo nan har abada.” Tsautsayi ya ja Nabila ta kifawa Dubu mari nan take kuwa Yaya babba ta yi tsalle ta dire ta fara faɗa daga ƙarshe har ta ce a kira mata Baba Abubakar.

Ran Mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, don a ganinta hukuncin da Nabila ta ɗauka shi me daidai.

Baba Abubakar cikin ladabi ya je gaban Yaya Babba ya ce, “Inno an aiko kina kirana.”

Nuna masa Nabila ta yi tana ɓata fuska ta ce, “Garba don Allah ka gaya mini kana da wani ƙauyen da ya wuce wannan?” Baba Abubakar ya girgiza kai ya ce, “Babu Inno.”

“Ka gaya mini ni da Marigayi mahaifinka muna da garin da ya wuce nan?” Yaya babba ta faɗa fuska a gaɗe.

“Babu Inno mai yake faruwa ne?”

“Ƴarka za ta makanta Dubu akan ta ce mata Ubanta ma ɗan ƙauye ne, don Allah meye aibu a nan? To tun wuri ka yi musu tsakani don ba za ta nakasa mini jika ba. Tun zama bai kankama ba har anfara kai ga haka, ina ga in sun kwaso kayansu sun dawo nan gabaɗaya.” Nabila ta kalli Yaya Babba a fusace ta ce, “Allah ya sawaƙe wa zai dawo nan da zama…” Tun bata rufe baki ba Mahaifinta ya ɗauke ta da mari don tun kafin su zo yake gargaɗinsu akan taɓa Dubu don ba abu ne mai wuya da zai ɓata ran mahaifiyarsu ba. Marin ba ƙaramin shigar Nabila ya yi ba don haka ta fashe da matsanancin kuka, ita kanta Mommy sai da marin ya taɓa ta dukda ba ita aka yi wa ba.

Yaya Babba ta ɗebi sallati tana tafa hannuwa rai a matuƙar ɓace, ta nuna Baba Abubakar ta ce, “Garba a gabana za ka illata mini jika ina ji ina gani. An ya kana ƙaunar Nabila kuwa? Daga na ce ka yi wa yarinya faɗa shi kenan sai ka kashe ta da mari. Don Allah meye mari ana zaune ƙalau? Wallahi idan ka sake shigowa ɗakin nan Garba sai na watsa maka falsafar rashin mutumci. Don Allah Dije ki fice mini da Garba daga ɗaki tun ban fice na bar masa ba.” Yaya Babba ta share ƙwallar idonta ta dubi Baba Abubakar da ke niyyar miƙewa ta ce, “Garba ka fita daga sabgar jikata Nabila wallahi idan ba haka ba sai na saɓa maka.” Ya russuna cikin girmamawa ya ce, “A yi haƙuri dai Inno.” Biris ta yi ta rabu da shi, ita kuwa Mommy ta cika fam kamar za ta fashe sai harare-harare take, don ma Yaya babba bata lura da ita. Dubu ta raɓe ta gefe tana yi wa Nabila gwalo, ai kuwa karaf akan idanun Yaya Babba.

Da sauri ta riƙe haɓa da hannu bibbiyu cikin mamaki ta ce, “Ke dai an yi makirar yarinya. An ya Dubu halin Ahmad kika yi kuwa wallahi wannan baƙin halin sai dai idan na Kulu ne…” Tun bata rufe baki ba Dubu ta ce, “Ni dai ki daina zagar mini iyaye tun da ba su yi miki komai eheee.” Yaya Babba na jin haka ta rushe da kuka tana ƙwalawa Baba Munkaila kira.

Ummou Aslam Bint Adam????
DUBU JIKAR MAI CARBI

        ©AMEERA ADAM

FIRST CLASS WRITER’S ASSO…

Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.

FREE PAGE 5

  Da sauri Baba Munkaila ya juyo yana muzurai don har lokacin banda huci babu abin da yake yi. Tun kafin ya ƙaraso Dubu ta riƙe hannun Yaya babba tana bata haƙuri, don duk cikin gidan babu wanda Dubu take tsoro kamarsa. Zuciyar Hajiya Nafisa fes don ko ba komai ta san zai gyarawa Dubu zama, yana ƙarasowa ya ce, "Inno ga ni." Yaya babba ta kalli Dubu da ta yi wuri-wuri sai zare ido take yi saboda gari banza ma Baba Munkaila ba ya raga mata ina ga yau da yake cike da haushin kashe masa zabbinsa. 

Yaya babba ta ɗauke kanta daga wurin Dubu tana cewa, “Munkaila don Allah ka raba ni da yarinyar nan Dubu, ni take son yi wa ɗiban albarka. Wai don Allah meye dalilin da ya sa ba za ka tafi da ita sashenka ba…” Tun bata gama magana ba Baba Munkaila ya zuba mata ranƙwashi a ka. Ai kuwa ta daka uban tsalle ta faɗa uwar ɗaki. Ganin haka ya sa Yaya babba ta sallame shi amma sam ba haka Hajiya Nafisa ta so ba.

Cikin Dare.

Tun dare bai gama tsalawa ba ƴan bijilanti suka yi wa gidan Marigayi mai carbi dirar mikiya, hannuwansu ɗauke da gorori sai fitilun da suke haskawa masu ɗan karen haske. Ban da haske-haske babu abin da suke yi, da sun ji motso ko na dabbobin gidan ne za ka ga sun haske sun nufi wurin da gudu. A wannan ranar ma Dubu da wuri ta yi kwanciyarta don ta samu damar gabatar da aikinta idan ta farka ciki dare. Sai dai wannan karon tsoro ne mamaye a zuciyarta saboda irin gororin da ta gani a hannuwa su Duna da Kuraye. Tana son suma ta nuna musu iyakarsu amma tana shakkar ta inda za ta ɓullowa lamarin saboda sun zagaye ko’ina ga fitilun da suke haske-haseke da su.

Dabara ce ta faɗo mata don har sai da ta murmusa a fili saboda mugunta. Ta shi ta yi a hankali cikin sanɗa ta ɗauko butar Yaya babba sai da ta zo daidai kan Barira wacce take kwance da Ƴarta ta tsiyayawa yarinyar a jikinta , idan ka ga yanda ta yi sharkaf sai ka rantse da Allah fitsari ta yi. Ɗaga rigarta ta yi ta zaro guntun likkafanin da ta ɓoye sai ta ɗaura a ƙafar Baraka ƴar wurin barira. A hankali ta fara jan ƙafar yarinyar har sai da ta kaita ƙofar ɗaki, ta koma ta riƙa jan ƴaƴan mutane tana kaisu bakin ƙofa sai da ta gama sai kawai ta haɗa ƙafafuwa su ɗai-ɗai ta riƙa ɗaurewa da likkafani. Sai da ta kai kusan yara biyar bakin ƙofa sannan ta janyo tsintsiyar kwakwa ta tsinka ta riƙa bi tana kartawa iyayen da yaran, da sauri ta bi gefe ta wurin da yaran suke kwance a bakin ƙofa ita ma ta yi luff ta tura ƙafarta ciki tasu. A hargitse mutanen ɗakin suka tashi carko-carko suka fara wawurar fitila, Barira na haska fitilarta a ka hango yaran suna firƙai-firƙai suna koke-koke. Kowacce da sauri ta je ta rarumi Ɗanta ai suna ganin Likkafani a ƙafar ƴaƴan kowa ya fara shan jinin jikinsa.

Maraƙisiyya ta dubi Barira ta ce, “Don Allah Barira me idona yake gane mini kamar likkafani.” Barira dama bakinta ƙunshe yake da magana don dai tana tsoron furtawa a samu matsala, ai kuwa tana jin haka ta yi farat ta ce, “Lashakka fihi wallahi likkafani ne don Allah ku taimaka mana fatalwar nan za ta ja mana yara.” Jin wannan maganar ta Barira da sauran hayaniyar mutanen ɗakin ya sa Ƴan bijilantin suka tattaru a ƙofar ɗakin Yaya babba suna tambayar ba’asi. Dubu na ganin haka ta zari buta tana matse-matsen ƙarya wai fitsari take ji, da sauri Yaya Babba ta yi farat ta ce, “Dubu ki raba ni da wannan ƙaddararran fitsarin da za ki yi yanzu, so kike ki fita fatalwar nan ta yi gaba da ke?” Dubu ya sake zabura tana buga ƙafa ta ce, “Wallahi fitsarin ya matse ni.”

Barira ta wurga mata fo ɗin Sa’ima ɗayar ƴar tata ta ce, “Maza hau fo ki yi amma babu in da za ki.” Wata uwar harara Dubu ta watsa mata ta ce, “Allah ya sawaƙe a gabanku da su Duna zan yi fitsarin ni dai wani daga cikinku ya raka ni.” Haushi ya ƙule Yaya babba ta zabga mata carbinta da bacci ya kwashe ta yana hannunta ta ce, “Wallahi idan kin ga fita ta ko ƙofar ɗakine ba Mai jama’a ya haife ni ba.” Dubu ta dubi Kuraye ta ga yanda yake ta Muzurai yana hange-hange shi a dole ga wanda yake fagen fama. A zuciyarta ta ce, “Wallahi kuma sai kun kwashi rabonku dan ubanku.” Ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka ta ce, “Inna don Allah ki ce Duna ya sa ɗaya daga cikin yaransa ya raka ni.” Duna na jin haka kansa ya ƙara fasuwa don a duniya babu abin da Duna yake so yake ƙauna sama da a fasa masa kai yana fagen aiki. Don idan ya saka uniform ɗin su na Ƴan bijilanti har ji yake ya fi wani Major general ɗin na Sojoji. Don haka cike da izza ya fara buɗa kafaɗa ya ce, “Babu damuwa muje zan raka ki. Ba fatalwa ba ko Aljan ne idona idonsa sai na ɗaye masa fata daga ƙafa har ƙeya.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button