BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Masha Allah sis Hafsat ina tayaki murnar kammala novel d’inki mai suna LAINART gaskiya littafin ya wa’azantar kuma ya nishad’antar da mu na jinjina miki a yarda kika baje mana basirarki a cikinsa lallai kin cancanci yabon girmamawa
Allah yak’ara basira da zak’in hannu, More grace to your golden elbow
So much luv u dear????

Page 2⃣6⃣

Haydar fira sukeyi da ummah ammah baisan ma me take cewaba kawai dai yana binta da uhm sai uhm-uhm ak’arshema tashi yayi yai ma ummah sallama yabar gidan.

Sapna ko da tashiga d’akinta saida tafara wanka sannan tad’auro alwallah tazo tagabatar da sallar magrib, bayan ta gama a nan saman darduma bacci yayi awon gaba da ita, sai wajen k’arfe tara da ummah takek’o d’akin saboda ta jita shuru bata fitoba sai tad’auka ko ciwon kan ne, ganinta tana bacci yasa ummah tace Sapna ko ciwon kan ne, dakyar Sapna tabud’e idonta tace ummah anyi isha’i? Ummah tace tun d’azun yanzu har tara ma tayi, dasauri Sapna tatashi tanufi toilet domin tad’auro alwallah, ummah tace idan kin gama sallar kifito kizuba abinci kici sai kisha magani Sapna tace toh ummah.

Bayan ta gama sallah shiryawa tayi cikin kayan bacci sannan tafito taje kitchen tazubo abinci takoma d’akin ummah taci bayan ta gama magani ummah tabata domin tasha Sapna saida ta6alle tabs d’in kusan guda shidda tashanye batare da ummah ta saniba sannan tatashi tayi ma ummah sallama takoma d’akinta, saman gadonta tahau takwanta duk yadda taso tayi bacci kasawa tayi juyi kawai take tana tuno tsantsan tsanarta da tagani cikin idon haydar duk sai taji babu dad’i chan kuma sai taja tsaki tace shi dai yasani mutum sai girman kan tsiya nima ai na tsanesa duk yadda taso takauda tunaninsa ammah takasa ahaka har bacci yayi awon gaba da ita

Haydar lokacin da yabar gidan direct gidansu yawuce ko wajen mami bai shigaba yawuce part d”insa cike da takaici, wanka yashiga domin ko ya samu sauk’in abinda yakeji a ransa ammah haka yagama wankan yafito Zuciyarsa a cunkushe, bayan ya shirya saman gadonsa yahau yakwanta yanayin yadda yaga sapna ne yadinga masa yawo tabbas ya tabbata sapna ‘yar maye ce, cikin ransa yace wa ma yasani ko har bin maza tana yi, haushinta ne yak’ara kamasa tsaki yaja cike da takaici duk yadda yaso yature tunanin ammah yakasa har wajen k’arfe d’ayan dare idonsa biyu sannan daga baya bacci yayi awon gaba da shi.

Washe gari sapna tun da takoma bacci bata farkaba sai wajen 11am shima ummah ce tazo tatayar da ita, bayan ta yi wanka ta shirya har d’aki ummah takawo mata breakfast tayi, duk yadda taso takama ma su ummah aiki ammah ummah tak’i, sapna saida tanace sannan tasamu ummah tabarta tayi daman tsoronta kar ummah tahanata fita anjima,

Lubna tun wajen k’arfe ukku take kiran sapna domin tazo ammah sapna ba ita tashiryaba sai bayan la’asar sannan tashiga wanka bayan ta fito tashirya cikin wando pencil ya kamata sosai sai tasa riga mai hannun vest ta d’ameta sosai, tufke gashin kanta tayi sannan tad’auko after dress tad’aura saman kayan gudun kar ummah tagani, jakkarta tad’auka tare da zura takalma, kulle d’akinta tayi tafito tanufi d’akin ummah cikin zuciyarta tana addu’an Allah yasa ummah tabarta tafita domin a yarda ummah tad’auka dagaske batada lafiya ba ta tunanin zata barta taje ko nan da zaurene, cikin sa’a ko da tatambayi ummah bata hanataba tace adawo lfy tare da yi mata Allah yakiyaye hanya.

Lokacin da ta isa gidan lubna duk ashirye suke ita kad’ai suke jira babu wanda zaka fidda da suturar kirki acikinsu, binta sukayi da kallo ganin yanayin shigar da take a jikinta, teema ce tace ammah dai sapna ba da wannan shigar zakije ba ko? Shuru sapna tayi batace komaiba ganin haka yasa sumy tace ke fa sapna yar wulak’anci ce sai ana miki magana kiyi banza da mutane, shuru sapna tayi, teema tace daman wani lokacin idan ‘yan wulak’ancin na saman kanta idan ta tanka ma mutum toh wannan bangon ma zai tanka, daidai lokacin lubna tafito daga d’akinta sanye take itama da wando pencil da ‘yar riga duk rabin k’irjinta a waje ga uban attach ta zubo a gadon bayanta, kallon sapna tayi tace ammah dota canza kaya zakiyi ko? Saboda kinsan wannan club d’in duk manyan mutane aka gayyata, sapna batare da ta ce komai ba tacire after dress d’in da tad”aura saman kayanta, gaba d’ansu sukace wow gaskiya sapna kinyi kyau, lubna tace ammah dai kyau kicire gyalen sai ki ida had’ewa, shuru sapna tayi tare da bud’e jakkarta tajawo bak’in space d’inta tadad’e sannan tawuce saida takai bakin k’ofar fita sannan tatsaya batare da ta juyoba tace zamu iya tafiya idan kun gama, babu wanda yayi magana nan suka fito suka nufi motar lubna suka shiga, tafiya suke suna hira ammah banda sapna da take zaune gaba tana kallon waje, suna cikin tafiya teema tace lubna dan Allah kid’an tsaya insayi recharge card, lubna tace ohk bari muje wancan junction d’in nagaba sai intsaya, daidai lokacin da take parking shikuma haydar yafito daga cikin wani babban chemist, motar da tayi parking gaban tasa yakalla, kallon yanayin parking d’in yayi yai tsaki yace yanzu haka macece tayi sa sai ta je ta yi causing d’in accident, da mamakinsa kuma sai yaga macence tafito a ciki yanayin shigarta yagani yagirgiza kai yace Allah yakyauta, ahankali yatako domin yayi mata magana tagyara parking d’inta, wata yahango zaune gaba fuskarta adad’e da glass sai dannar waya take saida gabansa yafad’i tabbas ya san wannan sapna ce, dasauri yakoma yashiga motarsa domin kar tagansa, har saida suka gama abinda zasuyi suka tada motar sannan shima yabi bayansu cikin dabara, da mamakinsa sai yaga sun shiga wani hotel shima sai yacinna motarsa a ciki yasamu gefe d’aya yayi parking, hotel ne babba cike yake da mata da maza saikace dukkan karuwan garin ne aka tara a wajen kowa harkarsa yake babu wata kunya atare da su, yana kallonsu suka bud’e motar suka fito, tun daga yanayin shigar sapna da yagani saida numfashinsa yakusan d’aukewa kishine yatokare masa mak’oshi takaici yakamasa, yana kallonsu suka nufi wajen taron da mutanen suke, Haydar cikin sauri yakunna motarsa yafice daga hotel d’in cike da takaici gudu kawai yake inkaga yadda yake gudun sai kace wanda yake cikin motar baya son ransa, da taimakon Allah Haydar ya isa gida, ko da yayi parking d’in motarsa bai fitoba kife kansa yayi saman steering d’in motar tsanar sapna da haushinta suka kamasa saida yayi kusan minti goma a haka sannan yafito yanufi part d’insa yana shiga ya maida yarufe saboda ba ya son wanima yashigo yatakura masa.

tunda suka shigo ‘yan maza sukayo musu caaa kowa burinsa yasamu shiga wajensu ganin haka yasa sapna tasalu6e takoma can gefe d’aya bisa plastic chair tazauna, lubna tunda tawaiga bataga sapna ba saida abin yabata mamaki, chan tahangota zaune ita kad’ai ta had’e fuska dan gudun raini, dariya tayi domin ta san daman sapna ba zata ta6a bari amoretaba, kallon masu yawo da kayan maye tayi tanuna musu sapna tace sukai mata, ko da sukaje sapna batayi musuba takar6i kwalbar giya da shisha tafara zuk’a saboda sapna ba ta shan taba,

Haka tazauna tana kallonsu har magrib tayi itadai giya kawai take sha saida tayi tatul sannan tamik’e tsaye dakyar tana rik’e da kwalbar tad’auki jakkarta tanufi inda su lubna suke, tafiya take tana tangyad’i kamar zata fad’i saidai jinta tayi jikin wani saurayi ya rungumeta, dakyar tad’ago kai takallesa so tayi taturesa ammah takasa, cikin muryar maye tace kasakeni, saurayin daman tunda yaga shigowarsu yad’aura idonsa akan sapna har taje tazauna, murmushi yayi yace baby kikwantar da hankalinki kawai so nake muje gidana kitayani hira, sapna tana lumshe idonta dakyar tana bud’ewa tace ni ba zanje gidankaba kabarni kawai inyi rayuwata a haka, saurayin yana rungume da ita yace kikwantar da hankalinki indai zaki bani had’in kai toh kema zaki samu kud’i sosai a wajena, sapna duka k’arfinta tasa taturesa tace ni ba ‘yar iska bace irinka, k’ara rungumota yayi yace itace mana kibani dama kawai indai kika fara harka da irina ba zaki iya dainawaba, turesa sapna tashiga yi ammah ya rik’eta sosai, gani tayi yana neman tura hannunsa cikin rigarta, wani sabon k’arfi yazo mata taturesa tare da d’aga hannu tawankesa da mari cikin 6acin rai tace kar kasaki kayi gigin ta6a min jiki inkuma ba hakaba wlh.. cikin zafin nama saurayin yak’ara jawota tare da yin kissing d’in bakinta, sannan yace in nata6a me zaki iya, sapna turesa tashiga yi ammah takasa dan haka tad’ago kwalbar giyar da take hannunta tak’wad’a masa a kai, cikin sauri yasaketa tare da dafe kansa saboda wani irin zafi da yaji dubawar da zaiyi har ta fasa masa goshi, saida yakalla yaga ba mai kallonsa sannan dasauri yawuce yashiga motarsa yabar wajen,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button