BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Lubna hankalinta ya tashi sosai rashin samun wayar sapna da batayi gashi yanzu bata ji zata iya zuwa gidansu hakanan domin tana tunani kamar asirin ya kare dan haka tashiga yawo wajen malamai ammah duk inda taje babu sa’a wasu cemata suke ai ba sai ta je gidansu sapna ba idan tabada kud’i za’ayi mata aiki mai kyau sapna dakanta zata waiwayeta ta kashe kud’i sosai ammah har lokacin babu biyan buk’ata gashi malaminta baya nan ya je marad’i kuma tasan shi da ya yi mata aiki kamar yankar wuk’ane dan haka tahak’ura sai ya dawo. Shiryawa tayi tabi lubna Abuja tahad’ata da manyan alhazai nan sukai ta shek’a ayarsu suna samun kud’i hankalinsu kwance.


Tun da aka sa bikkin yau kusan sati biyu kenan ammah sapna ba ta bari suhad’u da haydar da taji shigowarsa zata k’unshe cikin d’aki har sai ya tafi shima ko ya zo saidai yazauna susha hirarsu da ummah ba ya tambayar sapna.

Ahmad matsa masa yake akan yakaisa yaga amarya kan dole haydar ya amince yace gobe sai yashirya suje, cike da jin dad’i Ahmad yace Allah yakaimu, Haidar kiran ummah yayi yafad’a mata zuwan da abokinsa zaiyi domin sugaisa, dan haka tatisa sapna gaba suka fara shirye-shiryen tarbarsa.

Wanshe kare wajen 2pm suka gama komai ummah tasa sapna taje tayo wanka simple makeup tayi shima gudun kar ummah tayi mata fad’a tace batayi kwalliyaba, shiryawa tayi cikin shadda gown ash colour wadda tasha aiki da farin zare tana cikin d’aura kallabi tajiyo shigowarsu haydar tsaki taja tacigaba da shirinta, tana ji ummah tayo musu iso, a d’akin ummah suka zauna cike da fara’a suka gaisa bayan sun gama gaisawa ummah tace bari inkira muku ita,

Lokacin da ummah tashiga d’akin sapna lokacin ta gama shiri tana zaune bakin gado farin veil d’inta yana gefenta, kallonta ummah tayi tana murmushi tace gaskiya kinyi kyau itama sapna murmushin tayi, ummah tace kije gasu chan suna jiranki ni zan fita zamuje kasuwa da karima, sapna tashi tayi tana yafa gyalenta tace toh ummah sai kin dawo,
Tunda ummah tafita daga d’akin Ahmad kallon haydar yayi yace abokina wannan matar kamar itace wadda kakirani mukayi treating d’inta a hospital d’inmu, haydar d’auke kai yayi yace eh itace.

Sapna ahankali tad’aga labulen d’akin tare da yin sallama cikin siririyar muryarta, gaba d’ayansu suka zuba mata ido ahankali tataka kanta yana sadde a k’asa taje tazauna kujerar da take opposite d’insu, cikin jin kunya tagaishesu batare da ta kallesuba, Ahmad ne kawai ya amsa tare da cewa amaryarmu ya muka sameki? Murmushi sapna tayi tace lafiya lou, Ahmad yace lallai ruwa baya tsami banza abokina dole kake 6oye mana amarya ko dan kar akwace maka ita, haydar harara yawurga ma Ahmad, murmushi Ahmad yayi yakauda kansa yakalli sapna da take murmushi tana wasa da yatsun hannunta yace ammah dai amaryar nan tamu akwai kunya kin k’i ma d’ago kai inganki dakyau, ammah kallon sani nake miki ke ce kukazo asibiti lokacin mahaifiyarki batada lafiya ko? Sapna tace eh nice yace ammah ai jikin nata ya yi normal yanzu ko? Sapna tace Alhmdllh ta warke, mik’ewa tayi tace ina zuwa, fita tayi takawo musu abinci da drinks sannan tafita tabasu wuri domin suci, ko da tafita Ahmad ne yayi serving d’insu suna ci yana santi shidai haydar ci kawai yake bai ce ufan ba,

Saida sapna ta daidaici lokacin da suka gama Sannan takoma d’akin, Ahmad yace kai amarya wannan kalar delicious haka? Kar fa kija bayan aure inbaro girkin matata inzo intare ma naki, sapna dariya tayi tace ai bakomai duk d’ayane ai, Ahmad ma dariya yayi yace yau dai laifin nakine kinga kinja na cika cikina nan na baro na matata, murmurshi sapna tayi tace aba Auntyna hak’uri ai yaune kawai aka samu akasi,
ahmad yace ashe akwai rigima tunda nacika cikina nan, sapna kallon haydar tayi da yahad’e fuska yana dannar wayarsa kamar bai san abinda suke cewaba murmurshi tayi tace ai ga abokinka nan sai katisa shi gaba kuje kucinye abincin tare, dariya Ahmad yayi yace wannan uban d’an Jin kan, nan sukayita firarsu kamar daman sun san juna sai daga baya haydar yace ma Ahmad yatashi sutafi,

Nan sukayi ban kwana ahmad ya aje mata 20k tare da yi mata godia, sapna har wajen motarsu tarakasu takalli haydar da har lokacin fuskarsa a d’aure take tace yaya haydar Allah yakiyaye agaishe da su mami, kallonta haydar yayi dakyar yabud’e baki yace zasuji sannan yaja motar yabar gidan,

Ko da suka kama hanya Ahmad hirar sapna da kirkinta yake ma haydar shidai haydar yayi banza da shi, Ahmad bai damuba yace ammah abokina ya kamata kacanza hali wlh kwata-kwata bai daceba ace kana sha ma matar da zaka aura k’amshi saikace wani yaza6a maka ita ba kai kaza6i abinka ba, haydar ko inda yake bai kallaba yacigaba da tuk’insa, tsaki Ahmad yayi yace daman ai nasan za a rina mutum sai miskilancin tsiya,

Ko da suka isa gidansu haydar nan Ahmad yazauna yana ba su mami labarin kirkin su sapna da mahaifiyarta murmushi mami tayi tace Allah sarki wlh naso ingan d’iyarnan tawa kafin bikki ammah bakomai ai dayake bikkin kamar gobe ne,

BAYAN WATA ‘DAYA
Gidajen guda biyu hidimar bikki kawai ake domin bikkin a yanzu baifi saura sati biyu ba, ummah da Aunty karima sai banka ma Sapna magunguna da had’in kaza suke, Sapna saidai ta6oye a toilet taci kukanta ita kad’ai cike da takaicin auren da za’ayi mata da haydar, ga maganin da su ummah suke d’ura mata suna k’ara taso mata da sha’awarta dan ma Allah ya taimaketa tana shan tabs d’inta, ‘yar borno ce aka kira tana mata dilka nan da nan sapna tayi jawur,

Dangin Haydar akwati set shidda suka kawo ma Sapna na lefenta komai na ciki masu tsadane su ummah sun jinjina ma k’ok’arin da sukayi, hafsat ko da sukazo kawo lefe taso taga Sapna ammah cikin rashin sa’a basu samu had’uwaba kasancewar sapna ba ta gida.

Su hafsat sunso ayi party a bikkin ammah haydar yace babu abinda za a yi a bikkinsa kan dole suka hak’ura domin ta san halin yayannata kaifi d’ayane,

Sapna ma cewa tayi babu abinda zatayi ba ma zata gayyaci kowaba sai k’awarta d’aya Amina ‘yar islamiyarsu tagayyata.

Haydar 50k ya aiko mata dasu yace gashinan idan akwai abinda take buk’ata sai tasiya, sapna abun ya bata haushi ganin yadda bai zo ba saidai ya aiko a bata sai tausayin kanta yakamata domin ta san zaman hak’uri kawai zatayi da haydar.

ummah ta kashe kud’i sosai wajen ganin ta yi ma d’iyarta kayan d’aki na gani na fad’a gado set biyu tayi mata sai kayan parlour set d’aya dukkansu ‘yan Italian ne kowa ya jinjina ma namijin k’ok’arin da tayi wajen ganin ta fitar da d’iyarta tilo kunya,

Baba sani ma ba a barsa a bayaba duk kayan kitchen da kayan gara shi yad’auki nauyinsu.

Akwana atashi babu wuya wajen Allah yau jumma’a tun da safe ummah tasa sapna da k’awarta Amina sukaje wajen saloon da k’unshi, sapna batayi niyar yi ba ammah gudun 6acin ran ummah yasa taje,

Su Aunty karima suka shirya sukaje jere gidansu haydar part d’aya aka fitar ma sapna da shi a cikin gidan room nd bed room ne sai akayi mata kitchen d’inta, gado set d’aya aka saka mata komai nata ash nd black colour ne, aka tsara mata parlourn ta shima yayi gwanin kyau, jere akayi mata a kitchen d’inta kowa ya yaba tsaruwar d’akin nata ko da zamansu na d’an lokacine kafin agama gyaran gidan haydar sukoma,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button