BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Shuru sapna tayi batace komaiba lemunta kawai takesha kamar batasan abunda take fad’aba, ganin haka yasa Amfah tayi murmushi tare da rik’o hannunta tace haba sapna na San kina jina kiyi magana mana.

K’wace hannunta sapna tayi tare da lumshe idonta tace amfah Ahmad ko?

Cikin mamaki amfah tabita da kallo tace ya akayi kika sanni alhali yau kika fara ganina a gidan nan sapna ko wajen lubna kikaji lbrna?

Murmushi sapna tayi wanda yafi kuka ciwo tace na sanki mana daman kece amfah ta deejah……..

More comments more typing

Muje zuwa
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Na ji k’orafinku kuyi hak’uri masu cewa ina sonkai ba na typing d’in Duk tsuntsun da yaja ruwa….. yanzu saidai K’addarace kawai nake toh kuyi hak’uri yau ranar takuce gashinan na yi muku na baku page d’innan a kyauta????

Gobe Ranarki ce mummy (Sainah ummun meenal) Allah yak’ara shekaru masu albarka da nisan kwana, lafiya da dukiya mai Albarka wadda zamuzo muci muma???? up up up Happy birthday in advance mummy

1⃣1⃣➖1⃣2⃣

Murmushi sapna tayi wanda yafi kuka ciwo tace na sanki mana daman kece amfah ta deejah, kece kike tare da k’awata deejah awajenta nasanki.

Murmushi amfah tayi tace Sapna kenan nima daman ina jin labarinki wajenta banyi tunanin kece sapnar ba, numfashi taja tace yauwa yanzu kinga sai muk’ullah dake kema wlh ina sonki sosai.

Murmushin takaici tayi tace Aunty amfah kiyi hak’uri gaskiya ba zan iyaba kije kicigaba da tarayya da deejah itace daidai dake ba ni ba

Ammah sapna kin….

‘Daga mata hannu tayi tace please Aunty Amfah ix ohk! Ina buk’atar inhuta yanzu idan kikacigaba da bijiromin da haka zan iya tsanarki.
Bata jira jin me zataceba tatashi idanuwanta sun ciko da k’wallah domin anta6o mata inda yake mata k’aik’ayi toilet tanufa ttamaida k’ofa tarufe saida taci kuka mai isarta sannan tayo wanka tafito lokacin amfah ta bar d’akin,

shiryawa tayi cikin kayan bacci takoma saman gadon tazauna zuciyarta a tunkushe take, dafe kanta tayi jin yana mata ciwo.

Daidai lokacin Lubna tashigo d’akin ganin sapna a wannan halin yasa tayi murmushi domin amfah ta fad’a masu duk yadda sukayi da sapna,

wajen fridge tanufa tad’auki cup tabud’e tatsiyayi giya bakin gadon tanufa tazauna kusa da sapna tace amsa kisha ko kin samu sauk’in abinda yake damunki,

Kallonta sapna tayi da idanuwanta da sukayi ja sbd kukan da tasha, kwallah ce cike da idonta tace a’a mummy lubna ba zan sha ba kaina ne yakemin ciwo.

Lubna tace amsa bakomai kisha zakiji relief,
ammah mummy……
Please sapna kin san banison gardama kikar6a.
Kar6a sapna tayi tunda tad’aga cup d’in bata safkeba saida tashanye tass,

Murmushi lubna tayi takar6i cup d’in, kwanciya sapna tayi nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

Gefenta lubna takwanta tajawo wayarta tafara waya da tagama da wanchan Alhajin sai tayi da wanchan da tagama sai tayi da wacchan hajiyar ahaka har dare yayi nisa ganin haka kuma ga bacci tana ji yasa takashe wayar tare da komawa takwanta gefen sapna.

Kallon sapna tayi da taketa baccinta hankalinta a kwance murmushi tayi tare da shafa gefen fuskar sapna tace sapna ban san dalilin k’in yarda da ni da kikeyiba ammah ahankali zakizo hannu, hannu takai cikin rigar sapna tanafa shafata, cikin bacci sapna taji ana ta6ata dakyar ta iya bud’e idonta tasafkesu akan lubna da take k’ok’arin rabata da rigarta rik’e hannunta tayi cikin muryar da anji ansan a bige take tace mummy lubna kar kiyi min haka please kidaina bana so,

Muryar lubna tana rawa tace haba sapna wai miyasa kike guduna? Please ki amince da ni ba zan cutar da keba ke sheda ce kinsan ina sonki sosai zan baki duk abinda kike buk’ata, wlh sapna akanki zan iya rabuwa da kowa indai kika nuna bakison tarayyata da kowa kuma kika amince min.

Dakyar sapna ta iya janje jikinta chan gefen gadon takoma kwallah tana zubowa Daga idonta tace kiyi hak’uri mummy wlh ba zan iyaba kurabu dani kukyaleni inyi rayuwata hakanan banaso ina kyamar aikata wannan abun dan Allah kar kusani in aikata abunda natsana, meyasa kowa jikina yake so ba zan iyaba kurabu dani tun kafin intsaneku fashewa tayi da kuka tare da mik’ewa tsaye dakyar tana tafiya tana tangyad’i kamar zata fad’i tana yi tana sakin hanya har ta isa wajen kujera 3 seater takwanta tare da takure jikinta kamar wani ya ce zai saceta ammah har lokacin hawaye suna zuba daga idonta duk yadda taso taji tsanar lubna a ranta ammah ta kasa.

Tasowa lubna tayi tanufo inda sapna take kwance idanuwanta sunyi jawur kusa da sapna tatsugunnah muryarta tana rawa tace sapna kiyi.. sai kuma tayi shuru tare da jan numfashi sannan tak’ara cewa sapna kiyi hak’uri hakan ba zata k’ara faruwaba na yi miki alk’awali ba zan miki abinda baki so ba sai da yardarki.

Kwallah tana zuba daga idon sapna tad’aga ma lubna kai kamar zatayi magana kuma tafasa, lubna tace talk mana,
Dakyar tabud’e baki cikin muryar kuka tace toh Aunty lubna bakomai na hak’ura,

Murmurshi lubna tayi tace yauwa my sapna nagode cikin ranta tace sapna kenan ahankali zakizo hannu na lalla6akine a yanzu……. firgit tayi jin muryar sapna tana cewa Aunty lubna kije ki kwanta.

Tashi lubna tayi tana murmushi tanufi hanyar fita daga d’akin.

Kallonta sapna take har takai bakin k’ofa tace mummy lubna ina zakije? Juyowa tayi takalleta da idanuwanta da suka canza kala tace d’akin teemah zan je, tsareta da ido sapna tayi da alamun tambaya , ganin yadda take Kallonta yasa lubna yin murmushi tace tunda ke baki amince min kin nuna baki sona shine zan je inda akeyi da ni kar kidamu kiyi baccinki kawai sai dasafe bata jira jin amsartaba tabud’e kofar taficce. Ta6e baki sapna tayi cikin takaici sannan tajuya tacigaba da baccinta………..

More Comments More typing✍????

Muje Zuwa
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Wannan page d’in na sadaukar da shi ga intelligent writer’s Allah yabar k’auna, Allah yak’ara had’a kawunan mu????

Page 1⃣3⃣➖1⃣4⃣

Wajen k’arfe shidda tafarka dakyar ta bud’e idonta tajawo waya taduba ganin shidda ta yi yasa dasauri tayi wuf tatashi su mummy lubna ne da Am fag kwance saman gadon rungume da juna takaicine yakamata ganin yadda suke abubuwansu a gabanta basu ko jin kunya cikin ranta tace da alama ko sallah basuyi ba,

Dasauri tafad’a toilet tad’auro Alwallah , ko inda suke bata k’ara kalloba tad’auko hijab tazo tagabatar da sallah, bayan ta idar ta gabatar da addu’o’inta tatashi batare da takallesu ba tace mummy lubna ina kwananku? Cikin dashewar murya tace baby kin tashi lafiya? Ai nad’auka yau ba zan samu gaisuwar ba fushi ake dani, sapna bata tanka mataba tawuce takoma saman 3 seater tayi kwanciyarta talumshe ido domin ba ta buk’atar k’ara kallonsu nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button