BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Takaici ne yakamata sapna tashiga goge bakinta harda ‘yar k’wallarta, wajen su lubna taje tarik’o lubna lubna tallabo fuskarta tayi tace baby kukanme kike? Sapna share hawayen fuskarta tayi tace mummy kuzo mutafi gida dare ya yi, teema da takechan tare da wani jin da tayi Sapna ta ce atafi gida yasa tad’aure fuska tace nifa lubna saisa banson tafiya da Sapna sai tadinga cewa atafi gida toh mu ba yanzu zamu tafiba sai mungama holewarmu kuma ma sumy tana chan ciki tare da wani Alhaji kinga ko dole sai ta dawo sannan zamu tafi, lubna rik’o sapna tayi tazaunar da ita saman wata chair tace baby kid’an jira bari muzo mutafi, lubna kife kanta tayi a saman table d’in da yake gaban chair d’in da take,

Haydar tunda yashige d’akinsa bai fitoba sai da aka fara kiran sallar magrib sannan yafito zai tafi masallaci nan suka had’e da mami ta dawo anguwa shi baima san bata gidanba, mami tace my son ashe ka dawo? Murmurshi yayi yace eh mami ashe baki ciki, mami tace eh na d’an fitane, masallaci zakaje ko? Haydar yace eh mami, mami tace adawo lafiya,

Haydar ko da yagama sallah ji yayi yana son zuwa wajen umman sapna dan haka bai koma gidaba yashiga motarsa yabar gidan, ko da ya isa bayan sun gaisa da ummah, ummah taje tazubo masa dambun shinkafa da kunun aya, sai lokaci yatuna rabonsa da abinci tun safe dan haka yazauna yanad’i dambunsa yana ci suna hira da ummah har yak’oshi, har lokacin baiji motsin sapna ba nan yak’ara tabbatar ma kansa da bata dawoba ahaka har aka kira sallar isha’i yatashi yaje masallaci,

Sai wajen 7:30pm sannan lubna tatada sapna da take ta faman bacci domin sutafi gida, ko da suka kama hanya sapna cewa tayi asafketa gidansu dan haka har k’ofar gidansu suka safketa, suna safketa daidai lokacin haydar yadawo daga masallaci yana kallon motar tabar gidan, sapna tanufi cikin gida da shigar da take jikinta saboda after dress d’inta tana chan gidan lubna ta baro, ko da ta shiga zaure lek’awa tafara yi taga idan ummah bata tsakar gida sai tasamu talalla6a tashiga, tana cikin lek’awa kawai sai ji tayi an fizgota ta baya, a tsorace takalli haydar da yahad’e rai cikin 6acin rai yace daga ina kike? sapna tsorone yakamata domin ta san kashinta ya bushe idan ummah taji ko tafito taganta, shuru tayi batace ma haydar komaiba, haydar yace kinban mamaki kiduba kiga mahaifiyarki mutuniyar kirki kekuma abinda zaki saka mata da shi kenan kiduba shigar da take a jikinki ahaka wai matsayin d’iyar musulmai ce, tsuru-tsuru sapna tayi, haydar yace ashe ke dama ‘yar shaye-shaye ce? Dasauri sapna tad’ago kai takallesa, tsanartace k’arara tagani a idonsa ta bud’e baki zatayi magana yayi saurin katseta yace babu abinda zakice inyarda, ashe ke karuwace wai har club kika iya zuwa by ur age ke idanuwanki sun bud”e kinsan maza, sapna cikin d’aga murya tace haydar ya isheka kar k’ara jifana da kalmar karuwa tunda baka kamani ina karuwancin ba, haydar azuciye yace karuwace mana tunda har kinsan kije taron da karuwai ‘yan iska suke zuwa, tsanar haydarce taji cikin 6acin rai tace na ji ni karuwarce miye naka a ciki sarkin ‘yan sa ido? Haydar azuciye yad’aga hannu yad’auketa da mari, sapna dasauri tadafe k’uncinta tace ni kamara? Harara yawurga mata yace anmareki ko zaki rama ne? Kwallace tacika ma sapna ido dan haka tace wah sai ka san ka mareni dagudu taruga tashige gida tana shiga d’akinta tamaida tarufe

Haydar saida yasamu yasaita nutsuwarsa sannan yashiga d’akin ummah lokacin tana saman darduma batasan dramar da akayiba, dan haka yana zama saman kujera yajingine kansa akan kujerar tare da lumshe idonsa,

Sapna ko da tashiga d’akinta saman gado tafad’a tafara kuka saidai babu abinda yafi 6ata mata rai sai kiranta da haydar yayi da sunan karuwa saida tayi kukan mai isarta tafara tunanin ya akayi haydar yasan tana zuwa club? Ya akayi yasan tana shaye-shaye? duk yadda taso tasami amsar tambayar ammah takasa, k’wallace tacika mata Ido tunowa tayi da marin da haydar yayi mata ammah takasa ramawa, cikin takaici tatashi zaune tare da dafe kanta tace ya akayi ban ramaba? Tsaki taja tace sai na rama domin bashi kad’auki marin da kayi min, sannan tatashi tanufi toilet saida tayi wanka sannan tad”auro alwallah tazo tashirya saida tafara sallar magrib sannan tayi isha’i, bayan ta gama cire hijab d’in tayi tafito tanufi d’akin ummah, ko da tashiga da mamakinta tatarar da haydar a zaune bai tafi gidaba ko kallon inda yake batayi ta isa inda ummah take tazauna, ummah cikin fara’a tace mamana har kin dawo, murmurshi sapna tayi tace ummah tun d”azun nadawo ina d’akina, kallon haydar tayi daidai lokacin shima ya kallota yawurga mata harara itama harararsa tayi sannan tad’auke idonta daga kallonsa saboda k’warjinin da yakeyi mata, tace ummah bari inje inci abinci, ummah tace toh shikenan daman abinda kikesone aka dafa dambu, cikin jin dad’i sapna tace yauwa ummana wlh naji dad’i bari inje inci daman yunwa nakeji, dariya ummah tayi, bayan ta fita haydar kallon ummah yayi cike da tausayinta domin yana jin matar har cikin ransa yace ummah bari intafi gida naga dare ya yi, ummah tace toh shikenan haydar Allah yakiyaye hanya kagaishe min da maminka, ban dai da kirki har yau banje muka gaisaba, murmushi haydar yayi yace toh ya za’ayi ummah hidimarce sai ahankali ai akwai lokaci wata rana kun gaisa, ummah tace hakane kuma, sai dasafe Allah yakiyaye hanya nagode sosai Allah yabada ladar zumunci, haydar yace Amin ummah,
Sapna saida taga tafiyarsa sannan tad’au plate d’in abincinta takoma d’akin ummah tana ci suna hira.

Tun daga ranar Sapna da haydar harara kawai take had’asu kowa haushin d’an uwansa yakeji kuma ko a haka Sapna bata daina yawontaba, haydar abin yana d’aure masa kai ganin yadda ummah ba ta hanata fita.

Bayan sati d’aya daddyn su haydar yadawo daga tafiyar da yayi ta tsawon 2 months sunyi farin ciki sosai da dawowarsa dan haka yasa haydar yarage fita daga inda yadawo wajen aiki to yana manne da daddynsu yanzu ko gidansu sapna rabonsa da yaje kusan kwana bakwai da suka wuce, ummah ta damu sosai da rashin ganin haydar hatta ita kanta sapna da basu shiri saida taji ba dad’i, ammah ta samu sauk’in sa mata ido da yake, yanzu yawonta take hankalinta a kwance.

Lubna ce zaune tare da k’awarta amfah suna fira tace k’awata kinga yadda kika k’ara kyau kuwa? Miye sirrin? Dariya amfah tayi tace ance miki zaman abuja wasane? Wani Alhajine nasamu yake sakar min kud’i sosai banma yi niyar dawowa yanzu ba dandai tafiyace takamasa nan da 2 weeks zai dawo sai inkoma wlh k’awata kizo muje inhad’aki da abokinsa kema kiyagi rabonki dan ni nan jakkata cike take, hannu lubna tabata suka ta6a tace kai k’awata gaskiya kinja kaya dayawa dole inbiki ammah fa sai na samu sapna ko da tatsiyane domin har zuwa wannan lokacin banga alamun zata amince da ni ba, Amfah Dariya tayi tace toh kin mance da maganar malaminki da yace kar kiyi mata dole? Ta6e baki lubna tayi tace toh ai banga alamu zata amince min cikin ruwan sanyiba, gyara zama amfah tayi tace toh k’awata yanzu dai asamo mafita domin nima ina buk’atar ind’an huta da ita, dariya lubna tayi tace ai dolene asamo mafitar kinga idan aka gama shan mangwaro sai ayada k’wallon ahuta da k’uda, amfah murmushi tayi tace hakane k’awata ammah sai inga kamar ba zaki iya rabuwa da yarinyar nan ba, dogon numfashi lubna taja tace wlh ina sonta dayawa kawai naga bata moruwane ga customers suna ta bibiyata inhad’asu da ita ammah girman kanta ya hana kinsan kud’i sune abokan rayuwa ni ban had’asu da komaiba dan haka saboda kud’i zan iya barinta bari dai musamo mafita, dariyar jin dad’i amfah tayi tace saisa nakesonki k’awata wlh ki murji kud’inki, lubna murmushi tayi tace anfad’a miki ni ta wasa ce? Ai indai inaso toh babu wanda ya isa yahanani ina alfahari da hakan kidai saurareni kiga zuwa gobe sai sapna ta zo hannuna, lubna jinjina kai tayi tace k’awata ke ta dabance kuma kowa ma ya biki, cikin jin dad’i lubna tamik’e tsaye tace ai dolene kowa ma yabi, yanzu dai bari inje otel Alh naira yana can yana jirana koma dai minene bari inje indawo ba dad’ewa zanyiba ai nasan dai nan zaki kwana, amfah kwanciya tayi tace bari ind’anyi bacci kafin kidawo ai yau muna tare ammah fa kar kidad’e please, lubna lokacin takai bakin k’ofa tace ba zan dad’eba dear kar dai kije ko’ina dan nasan halinki, dariya amfah tayi tace ba inda zanje har sai kindawo saboda inaso inga gobe yadda zamu samu yarinyarnan sarkin girman kai da ji da kai, lubna dariya tayi tace zanko baki mamaki saidai na dawo………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button