BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Sapna da tunda ummah tafara maganar kuka take dasauri taduk’a tarik’o k’afar ummah cikin kuka tace ummah dan Allah kiyafe min wlh ba laifina bane su lubna ne suka d’aurani kan wannan gur6atacciyar rayuwar dan Allah kiyi hak’uri kiyafen wlh ba zan k’araba, tureta ummah tayi cikin 6acin rai tace na baki nan da minti biyar kitattara kayanki kibarmin gida inba hakaba wlh zan kasheki inhuta da takaicinki, sapna k’ara rik’o k’afar ummah tayi tace dan Allah ummana kiyi hak’uri na yi miki alk’awali ba zan k’araba,

Ummah tureta tayi tace wlh ko kitashi kifita ko inkasheki, daidai lokacin haydar yashigo gidan dasauri sapna tatashi tanufi wajensa tana kuka tarik’o hannunsa tace yaya haydar kataimaka min kaba ummah hak’uri wlh ba laifina bane, ba zan k’araba, dan Allah kace kar takoreni wlh banda kowa sai ita, jawosa tayi tace please muje katayani bata hak’uri, haydar ganin yadda sapna tarikice sai kace mahaukaciya kallon ummah yayi cike da mamaki ganin yadda take kuka, har ya bud’e baki zaiyi magana, d’aga masa hannu ummah tayi tace kar kasaki kabani hak’uri haydar nuna masa kwalaben giyan da suke k’asa tayi tace kaduba kagani haydar wai d’iyatace ta cikina take shaye-shaye, ni wai nahaifi karuwa yanzu ashe mutane zagina suke, cike da takaici ta girgiza kai tace duk tarbiyar da nayi ma yarinyarnan ashe ta banza ce toh wlh sai ta barmin gida takoma chan wajen ‘yan iskar abokanta tacigaba da karuwancinta,

Sapna cikin tashin hankali tace ummah wlh ban ta6a karuwanciba dan Allah kiyafe min, cikin d’aga murya ummah tace kifita kibarmin gida nace tun kan inkasheki, sapna da take kuka dafe kanta tayi da taji yana sara mata saboda ciwo, wata irin k’ara tasaki tayi taga-taga zata fad’i, dasauri haydar yatarota tafad’o jikinsa wata irin k’ara takeyi nan k’afafuwanta suka fara nad’ewa, wani dogon numfashi taja tabank’are, ba haydar ba hatta ita kanta ummah ta tsorata, haydar kallonta yake ganin condition d’in da take ciki yasa tagane aikin ba na asibiti bane, dasauri yakwantar da ita k’asa tare da jawo wayarsa yakira malam yahya ishaq kasancewar wajensa haydar yake d’aukar karatu, cikin sauri yai masa bayanin halin da sapna take ciki, nan malam yace yaimasa kwatancen gidan gashinan zuwa.

Ummah tunda sapna tafad’i tsaye tayi tana kallonta ta kasa zuwa inda take saidai binta take da ido hawaye suna zuba, haydar ganin haka yasa yaje yarik’e ummah yazaunar da ita cike da tausayi, ummah dafe k’irjinta tayi tana nanata innalillahi wa’innah ilaihiraji’un saboda yadda takejinsa.

Ko da malam ya iso anguwar haydar ne yaje yatafo da shi gidan, tunda suka shigo malam kallon sapna yake tsawon minti ukku sannan yace ma haydar yabashi ruwa a cikin cup, dasauri haydar yaje yad’ebo yakawo masa, duk’awa malam yayi kusa da ita yayi addu’o’i cikin ruwan sannan yayi bismillah yad’ebo ruwan yawatsa mata a fuska, wani dogon numfashi sapna taja, malam ruwan yak’ara d’ebowa yawatsa mata, wata irin k’ara tasaki cikin wata irin babbar murya tace kar kakashemu wlh turomu akayi kabarmu da ranmu,
Ummah da haydar mamakine yakamasu
malam yace wa yaturoku?
Girgiza kai sapna take tana shirin tashi tagudu malam yakalli ummah yace tazo tarik’eta,
Dasauri ummah tazo tarik’eta; fizge-fizge sapna tafara yi ganin haka yasa malam yak’ara d’ibar ruwan yawatsa mata a fuska, nan tak’ara sakin wata gigitacciyar k’ara tace kayi hak’uri kar kakashemu mun bika,
Malam yace wa yaturoku?
Cikin kuka sukace turomu akayi,
Yace ba zaku fad’amin Wanda yaturokuba?
Shugabanmu sukasa yaturo mu domin muhau kanta,
Malam yace su wanene sukasa aka turoku?
Cik’in d’aga murya sukace ba zamu fad’aba!!!!
Malam yace toh shikenan nikuma zan k’oneku da ayoyin Allah,
nan malam yafara mata karatu, cikin k’araji sukace kar ka k’onamu kajira zamu fad’a,
Malam dakatawa yayi da karatun yace kufad’a inji kuma kukayi min k’arya sai na k’onaku,
Sukace wannan tantiriyar ‘yar iskar bace taje Wajen oganmu tahad’ashi da sapna tace ayi mata aiki akanta domin tamallaketa, a tsorace duk suka kalli sapna kowa mamaki yabayyana a fuskarsa,
malam yace ina jinku.
Aljanin yana kuka yace shine malam yaturoni nahau kanta saboda ta fi k’arfin mu ba zamu iya shiga jikintaba saida muka samu ranar da batayi azkhbar ba tana period ta wannan damar muka samu muka shigeta shine mukesa ta tana wannan halayyar, hatta ita kanta mahaifiyarta saida akayi aiki a kanta aka rufe mata baki, tunda mun fad’a maka gaskiya toh dan Allah kabarmu mutafi wlh ba zamu k’ara dawowaba, malam yace toh shikenan kufita idan kuma kuka k’ara dawowa toh sai na k’onaku da ayoyin ubangijinmu kun yarda?
Cikin d’aga murya sukace wlh mun yarda daman ta fi k’arfinmu.
Malam yace toh shikenan bismillah,

Sapna atishawa tayi sau ukku sannan tabud’e idonta dakyar, dasauri Malam yad’auki kofin yabata ruwan addu’an tashanye, dasauri tarungume ummah cikin kuka tace ummah me yake faruwane? Dan Allah kiyafemin wlh su Aunty lubna ne sukeso su gur6atar min da tarbiyar da kika bani, k’ara shigewa tayi jikin ummah tace ummah deejah ce silar fad’awata Wannan mummunar rayuwar dan Allah kiyafemin wlh ba zan k’araba nasan ban kyautaba a lokacin da kikaso inrabu da deejah sai nayi miki k’arya nace miki mutuniyar kirkice, d’ago kai sapna tayi takalli ummah da idanuwanta suka rine saboda kuka tace ummah wlh a lokacin inaso ingyara rayuwar deejah ne sbd ina jinta kamar ‘yar uwata saisa nayi miki k’arya ashe ita kuma tana chan tana neman hanyar da zata gur6atamin rayuwata itace silar fara shaye-shaye na, ummana dan Allah kar kirabu da ni idan kika koreni bansan inda zanjeba.

Ummah har lokacin kuka take rungume d’iyartata tayi tace wlh sapna na yafe miki duniya da lahira kuma nima nasan ina da laifi acikin faruwan haka banta6a bincikan inda kike zuwaba, ban ta6a zuwa d’akinki nabincika naga kalar rayuwar da kikeyi, a lokacin da kike dawowa a cikin maye ban ta6a tsayawa na bincikaba saboda na yarda da ke gani nake babu Wanda zai iya rushemin tarbiyan da nabaki ummah girgiza kai tayi cikin kuka tace ashe na yi kuskure abinda nake tunani ba haka bane, cikin kuka sapna tak’ara ruk’unk’ume ummah nan suka cigaba da ita.

Haydar da malam shuru sukayi suna kallonsu cike da tausayi, saida su ummah suka lafa da kukan sannan malam yayi gyaran murya yace Alhmdllh munji dad’i da gaskiya tabayyana a lokacin da ake buk’atarta kuma kuka fahimci juna, saidai inaso infad’a ma kowa kuskurensa zan fara da ke sapna da farko dai kinyi babban kuskure da kikayi abota da k’awa ‘yar iska alokacin da mahaifiyarki tanuna miki illar abota da k’awar banza ammah ke saboda wata manufarki sai kikayi mata k’arya kika nuna mata ai ‘yar mutunci ce kike tare da ita ke a tunanunki zaki iya shiryar da ita saidai kinyi babban kuskure kar kimance da fad’ar Allah mad’aukakin sarki da yace ma manzonsa INNAKA LA TAHADI MAN AHABABTA WALAKINNALLAHA YAHADI MAN YASHA (Lallai kai ba zaka iya shiryar da Wanda kasoba saidai Allah yake shiryar da wanda yaso) Dan haka kinga bai daceba kice kinaso kishiryar da k’awarki saidai ki mata fatan shiryuwa kidinga mata nasiha kinga ke a lokacin da kikaso kigyara mata rayuwarta itakuma a lokacin take nema ta6ata miki taki rayuwar, sai kuma maganar azkhar bai daceba ace dan kina period ba zaki nemi tsarin jikinki ba a lokacin da mace take haila duk wasu k’ofofin jikinta suke bud’ewa kuma aljannu duk inda k’azanta take sunfi kusantar wajen saisa akeson mace idan tana haila tadinga yawan tsarkake jikinta tana yawan azkhar da zama da alwallah hakan shi zai taimaka miki wajen nisantar mugayen halitta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button