BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

dariya lubna tayi tace shegiyar gora ni ai gashinan k’awarta ta gasani dayawa, rurin da wayarta tashiga yi ne yasa takalli amfah tace k’awata bari inje indawo wani sabon kamune nayi yanzu haka yana hotel yana jirana, dariya amfah tayi tace to k’awata sai kin dawo ammah kitatso mana dayawa, dariya sukasa gaba d’ayansu sannan lubna tad’auki jakkarta taficce……..

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Nagode sosai my fan’s, gaskiya naji dad’in yadda kuke nuna damuwarku akaina, ina jin dad’in addu’o’in da kukemin, masu bina a pc wad’anda ban samu namaida musu reply ba kuyi hak’uri nima ba a son raina hakan take faruwaba ammah duk da haka ana tare nagode sosai da addu’anku

wannan page d’in nakune my fan’s nabakushi a kyauta????

Page 3⃣8⃣

Sapna kuka takeyi babu k’ak’autawa saida taji kanta ya fara ciwo sannan tayi shuru dakyar tatashi tasha magani sannan takoma takwanta nan da nan zazza6i yafara rufeta dakyar take tashi tana sallah,

har akayi sallar isha’i batasa haydar a idontaba dakyar tatashi tayi wanka tasaka rigar baccinta kwanciya tayi ammah takasa baccin ga yunwa ga zazza6i, ganin har k’arfe tara batasa haydar a idontaba yasa tafara kwallah tace shikenan shi yana can wajen ‘yan matansa nikuma ya barni nan ni da baya k’auna, tsayuwar motarsa ce taji sai jin wani sanyi taji a ranta, haydar ko da yashigo bata kalli inda yakeba murmushi yayi yace baby ba dai har yanzun fushin ake da niba?

haushinsane taji ya k’ara kamata cikin ranta tace tunda ka je kagama soyayyarka, bata tankasaba tajanyo wayanta tafara game, ammah babu alamun fara’a atare da ita.

murmushi haydar yayi yace bari dai inje inyi wanka inyaso idan nafito sai mushirya, haydar wanka yashiga da harara tarakasa cike da jin haushinsa sannan tacigaba da game d’inta.

bayan ya fito saida yashirya sannan yad’auko ledar da yashigo da ita yadawo gefen gadon ya aje sannan yatashi yaje kitchen yad’auko plate da cups sannan yadawo gefenta yazauna yace baby kitaso muci naman nan ni yunwa nakeji kuma nasan yau yadda ake fushin nan ba abinda zaki girka min saisa nasiyo.

turo baki sapna tayi tace kaje kaci ni bana ci.
murmushi haydar yayi tare da shafa cikinta yace ammah ai kema kina jin yunwa, ture hannunsa tayi daga saman cikinta.

haydar bai damuba yatallabo fuskarta yace subhanallah baby halan kuka kikayi naga fuskarki duk ta kumbura, sapna kamar jira take sai hawaye suka fara tsiyaya, haydar a rikice yace sapna meyake faruwane? kallonta yake cikin ido kishinsa yagani k’arara acikin idonta

janye fuskarta tayi daga rik’on da yayi mata, murmushi haydar yayi yace sapna ba dai akan fitar da nayi bane? harararsa tayi tace ni ina ruwana da fitar da akayi dan ka je wajen wacce kakeso ai ba laifi bane,

tunda tafara maganar haydar yakafeta da ido yace baby nifa d’azun hospital naje wata theater mukayi babu wajen wacce naje ni wace mace zata soni ahaka.

sapna kamar zatayi kuka tace kai d’inne mace ba zata so ba bayan kana da kyau da kud’i?
murmushi haydar yayi yace toh ya za’ayi tasoni bayan ke kanki baki sona ai bana tunanin akwai wadda zata soni ahaka.

sapna tana hawaye tace ammah ai ahaka kake zuwa wajen wadda kakeso kuma itama tana sonka,
Haydar da mamaki yake kallonta yace sapna ko dai kema kinfara sona ne?
harara tawurga masa tace Allah yasauk’e ni bana sonka.

haydar lakuce hancinta yayi yace toh naji ba’a sona shikenan ko? nima Allah zai bani wadda zata soni

sapna d’auke kai tayi daga kallonsa tace bayan wadda kuke soyayya,
murmushi haydar yayi yace ai mata hud’u nake da burin yi,

sapna a tsorace tazaro ido tace mata hud’u kuma? duk ina zaka ajesu?
haydar yadda tayi tambayar ta so tabashi dariya, kwantar da kansa yayi a k’irjinta yace baby cikin hud’un nasan akwai wadda zata soni.

sapna gabantane taji yana dukan ukku-ukku hatta shi kansa haydar yana ji, murmushi yayi tare da shafa fuskarta,
k’ara turo d’an k’aramin bakinta tayi, haydar jan bakin yayi yace me kuma nayi?

sapna cikin fushi tace ni kad’agani, haydar murmushi yayi yace baby ai banida nauyi,

ta bud’e baki tana shirin yin magana haydar yahad’e bakinsu yafara kissing d’inta, sapna kamar jira take nan tabiyemasa.

haydar tabasa mamaki sosai ganin yau ko kad’an bata hanasa ta6ataba, ahaka yasamu yarabata da ‘yar 6ingilar rigarta, romance d’inta yake son ransa saida yaga ya rikitata sosai sannan yatashi daga jikinta, dasauri sapna tarik’o hannunsa.

haydar kallonta yayi da idanuwansa da suka canza kala yace baby ya dai? dasauri sapna tasakesa jikinta duk ya canza,

murmushi haydar yayi yazauna k’asa yana juye kazar a cikin plate, kallonta yayi yaga bata da shirin tashi yace baby kitashi kisa rigarki kizo muci nasan kema yunwa kikeji,

sapna kamar tad’aura hannu saman kai takwala k’ara, dakyar tajawo rigarta tasaka tana turo baki tasafko, dan dai yunwar da takeji da ba zata ciba.

haydar ganin yadda take kumbure-kumbure kamar yayi dariya ammah yadanne dariyar yace muci ko ni zan baki dakaina?

harara tawurga masa sannan tad’auka tafara ci, murmushi haydar yayi sannan shima yafara ci daga nan ba wanda yak’ara magana har suka gama.

Sapna ce tafara janye hannunta tatashi taje toilet tawanke hannunta da bakinta sannan tadawo takwanta,

haydar shi yakwashe kayan yakai kitchen, sannan yadawo saida yak’ara yin wanka sannan yadawo yakwanta shima,

tunda suka kwanta yana jin sapna tana ta juyi yashareta yajuya mata baya,

sapna haushine yakamata ganin yadda yajuya mata baya, tun tana tunanin zai juyo gareta saboda wani irin feelings da takeji ammah ko waiwayarta baiyiba, nan fara tsaki.

haydar dariya yake ahankali saboda shima yasan shi yafara tak’ulota, cikin ransa yace zan gani idan zaki aje wannan girman kan naki kibada kai.

chan sai ya tsagaita da dariyar da yake batare da ya juwoba yace baby lafiya kike ta tsaki? sapna cike da k”ulewa tace ina ruwanka.

haydar dariyarsa yake yace sorry babu fa ruwana ammah dan Allah kirage motsi saboda bacci zanyi.

sapna harara tawurga ma k’eyarsa sannan tajuya itama,

dakyar tasamu bacci yayi awon gaba da ita,

da asuba ita tafara tashi saida tayi wanka sannan tad’auro alwallah, haydar yana ganin ta fito yatashi yashiga domin yad’auro alwallah, lokacin da ya fito ana shirin tada sallah dasauri yaficce yatafi masallaci.

wajen k’arfe goma tafarka a daddafe tatashi tashiga kitchen tahad’a musu breakfast, bayan ta gama tana shiga bedroom lokacin haydar yafito daga wanka,

kallonta yayi tana ta kumbure-kumbure har lokacin murmushi yayi batare da ya ce komaiba yacigaba da goge ruwan jikinsa da d’an k’aramin towel, sapna kallo d’aya tayi masa tawuce tashige toilet

lokacin da tafito d’aure take da d’an k’aramin towel haydar binta yayi da kallo, sapna bata damu da kallon da yake mataba tazo gaban dressing mirror tafara shafa, ta cikin mirror tahangosa har lokacin ya kafeta da ido harara tawurga masa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button