BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haydar tsaye yake ya kafeta da idanuwansa kallonta yake daga sama har k’asa towel ne k’arami take d’aure da shi iyakarsa a cinya yatsaya mata, yanayin yadda tad’aura towel d’in rabin k’irjinta duk a waje yake, Sapna ganin yadda yazuba mata ido yasa takalli jikinta, zaro ido tayi ganinta d’aure da towel dasauri tabud’e wardrobe d’in tajanyo doguwar hijab tasaka,

Haydar cike da jin kunya yafauje yaje yad’auki wayarsa yaficce daga d’akin,

Sapna tana ganin fitarsa tarakasa da harara tace Allah ya isa kallon da kayi min.

Haydar jikinsa ya yi sanyi sosai ahaka yakoma yazauna kasa cigaba da breakfast d’in yayi duk yadda yajuya sapna ce yake gani, k’arshe ma tashi yayi yaje yashiga motarsa yabar gidan.

Sapna ko da tashirya saida tagyara d’akin sannan tafito taje tayi breakfast, har lokacin tana jin takaicin yadda Haydar yashigo yaganta ba kaya jikinta. itama bataci abin kirkiba takwashe tamaida kitchen sannan tadawo tazauna takunna kallo tana yi.

Comment
nd
Share

Sis Nerja’at✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Page 3⃣5⃣

Haydar tunda yaje asibiti a daddafe yake aiki duk yadda yaso yature tunanin sapna a ransa ammah yakasa dan ma Allah ya taimakesa yau baida patients sosai hatta shi kansa Dr Ahmad saida yayi mamakin ganin yadda haydar yacanza yau baida kuzari a tare da shi, ko da yatambayesa ko baida lafiya, haydar cewa yayi lafiyarsa lau kawai yanayin ne nayau yacanza masa,

shidai Ahmad ba dan ya yardaba kawai dan ya san halin abokin nasane da zurfin ciki.

Sapna hankalinta gaba d’aya yana wajen kallo bata ankaraba sai gani tayi k’arfe sha biyun rana tayi, dasauri tatashi tashiga kitchen jalop rice ce tayi musu wacce taji kayan lambu nan da nan gidan yagauraye da k’amshin girkinta, bayan ta gama ta gyara wajen, bedroom tashiga saida tayi wanka tashirya sannan tayi sallar azuhur, bayan ta gama tadawo parlour tazauna tacigaba da kallo sai wajen k’arfe ukku sannan haydar yadawo gidan,

sapna ciki-ciki tace sannu da zuwa batare da ta kallesaba, Haydar shuru yayi kamar ba zai amsaba yatsaya yana kallonta sai kuma chan yace sannu, sannan yashige bedroom.

sapna ta ji haushin yanayin yadda ya amsa mata, tsaki taja tace ka dai ji dashi,

Bayan ya gama kimtsawa yafito yanufi dining, sapna tashi tayi tabi bayansa saida tayi serving d’insa sannan itama tazuba nata tazauna taci, bayan sun gama tattare kayan takai kitchen, lokacin da tadawo haydar har ya canza channel d’in da take kallo, turo baki tayi tace yaya haydar ba fa nan nake kalloba, batare da ya kalletaba yace toh Ai ni nan nake sha’awar kallo,

Sapna cike da jin haushi tawuce tashiga bedroom tazauna, idanuwanta takai bisa bedside da ya aje wayarsa cikin jin dad’i tad’auki wayar talalubo number d’in ummah takira,

bugu biyu ummah tad’auka jin muryar ummah da tayine yasa taji sanyi a ranta ahankali tace ummana ina wuni?
Umma ma cike da jin dad’i tace lafiya lou mamana ya kuke?
Sapna tace lafiya lou ummah nayi missing d’inki.
ummah tace ban yardaba keda kikaje kika kashe waya dan ma kar mu dameki, ai shi haydar yana kira kullum muna gaisawa.
Sapna marairaicewa tayi tace ummah wlh ba haka bane, ummah tace toh yayane idan ba haka bane?
Sapna kamar tafad’a ma ummah kwacemata waya da haydar yayi sai kuma taji ba zata iyaba gudun kar Hankalin ummah yatashi tad’auka basu zaman lafiya,
muryar ummah taji tana cewa kinyi shuru.
Murmushi Sapna tayi tace Ummah wayanace tafad’i ta lalace saisa kikaji ni shuru.
Ummah tace ayya Allah sarki toh maimakon kibada agyara miki?
Murmushi Sapna tayi tace ai ya ce zai kai min wajen gyara.
Ummah tace toh shikenan dafatan dai kuna zaune lafiya babu wata matsala?
Sapna tace lafiya lou muke ummah,
Ummah tace Masha Allah haka akeso kidaita hak’uri domin shi zaman aure sai da hak’uri, kizauna da danginsa tsakani ga Allah banda yawo.
Sapna tace toh shikenan ummah insha Allahu zan kiyaye, ya wajensu baba sani? Ummah tace suna nan lafiya lau, Sapna tace Allah sarki Ummah yanzu ke kad’ai ce gidan, dariya ummah tayi tace injiwa yafad’a miki ai nayi wata sabuwar ‘yar aiki dattijuya yanzu haka na bata d’akinki ta zauna kinsan zama mutum d’aya babu dad’i.
Cikin jin dad’i Sapna tace aikam dai ummah hakan da kikayi shine daidai ammah kamar kina jira intafi daga tafiyata har anbada gadon d’akina,
dariya ummah tayi tace toh ya za’ayi daman ai ita mace zamanta a gidansu na d’an lokacine gidan mijinta shine ake fatan yakasance dauwamamme,
Numfashi Sapna taja tace haka ne ummah,
Ummah tace toh sai anjima kigaishe min da haydar d’in,
Sapna tace insha Allahu za ya…. jin za a bud’e dakin yasa tayi saurin kashe wayar batare da ta gama wayar ba.

Yana shigowa dasauri tamaida hannunta baya ta6oye wayar,

haydar tsaye yayi yana kallonta domin daga ganin yanayinta ka san batada gaskiya, kallon hannunta yayi da ta6oye a baya yace me kike 6oyewa? Sapna daburcewa tayi tace um-um bakomai,
harararta haydar yayi yace ban yarda da ke ba, Sapna tana ganin ya nufo inda take dasauri tace Allah yaya haydar babu komai,
Haydar bai tanka mataba saida ya iso inda take sannan yace muga abinda kike 6oyewa,
Sapna tace na fa ce maka babu komai
Hannu yakai zai janyo hannunta dasauri tatura wayar k’ark’ashin pillow sannan tafiddo hannunta tace kagani babu komai?
Harararta haydar yayi yace tashi daga nan, turo baki tayi tace ina zanje,
tureta haydar yayi daga wajen yana d’aga pillow saiga wayarsa, d’aukowa yayi damamaki yake kallon Sapna yace wa yace kita6a min waya?
Sapna tsaye tayi tayi tsuru-tsuru cikin tsawa yace nace ubanwa yace kid’aukar min waya, wa ma kika kira?

Sapna tace kayi hak’uri ummah ce nakira, baice mata komaiba yashiga duba call history sannan yad’ago yakalleta yace da izinin wa kika d’aukar min waya kika kirata,

idanuwan Sapna sukayi rau-rau da k’wallah tace kayi hak’uri, banza haydar yayi mata yawuce yafi,
Hamdala Sapna tayi dataga bai mata komai ba dan ta ma d’auka zai doketa ne.

har tayi sallar la’asar ammah bataji motsinsa ba hakan yatabbatar mata da ya fita dan haka tataso tadawo parlour tana fitowa taci karo da hularsa a saman 1 seater tace ikon Allah shikuma wannan mugun nan yamance hularsa? d’aukar hular tayi tasa a kanta tace bari ingwada yadda yakeyi, juyawa tayi tafara tafiya tana kwaikwayon yadda haydar yake tafiya tace a’a ba haka yakeyi ba gyara tafiyar tayi tace yauwa haka yakeyinta cikin k’asaita, saida taje kamar zata shiga bedroom batare da ta juyoba tatsaya tace bari inga ko zan iya irin muryarsa,

gyaran murya tayi tace ke naga kina shishige ma hafsat toh inaso kisani ko da dawasa kar kikuskura inga wani abu daga cikin tarbiyar da muka bata ta canza,

dariya sapna tayi tace yauwa ashe na iya kalan maganarsa, toh bari inyi yadda yake d’aure fuska kamar dunkum, d’aure fuska tayi tare da juyowa tace ke me kika….. k’ara tasaki lokacin da sukayi ido hud’u da haydar da yake kwance saman 3 seater yana kallonta, tsorone yakamata muryarta tana kyarma tace yaya haydar! dagudu taje tashige bedroom bata tsaya ko’ina ba sai saman gado tazauna tazuba ma k’ofa ido tana jiran shigowar haydar domin ta san yau sai ya 6ata mata rai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button