BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Murmushi mami tayi tace Allah sarki Allah dai yabada ladar, my son idan karik’e gaskiyarka kataimaka ma wanda yake buk’atar taimako toh Allah zaici gaba da bud’e maka ta inda baka tsammani.
Cikin jin dad’i Haydar yace insha Allahu mami.
Mami tace ka ci dinner d’inka?
Yace eh yanzu naci
Tace toh my son kaje kahuta nasan agajiye kake.
Yace toh mami sai dasafe.
Murmushi mami tayi tace Allah yakaimu my son.
Haydar ko da yakoma d’akinsa kayan jikinsa yacanza sannan yabi lafiyayyen gadonsa yahau fuskar sapna ce take ta yimasa gizo da yanayin shigar da take jikinta, tsaki Haydar yaja yace duk matan yanzu abun tsorone ita da nake ma kallon mutuniyar kirki ammah ba haka bane toh aiko babu macen da zan iya aure a yanzu saidai nan gaba idan nasamu wacce tayi min, yana ta raya zancen a ransa ahaka bacci yayi awon gaba da shi.

Bayan nurses d’in sun fita sapna dawowa tayi kusa da ummanta tazauna cike da tausayi tace sannu ummana ya jikin naki? Murmushi ummah tayi tare da shafa kan d’iyartata tace jiki Alhmdllh ya yi sauk’i mamana dafatan dai baki fad’a ma babanki saniba, ita sapna shaf ta ma mance da su baba sani sai yanzu da ummah tayi mata maganar, tace eh ummah basu saniba, ummah tace aik’ara da baki fad’a musuba saboda bana son hankalinsu yatashi, murmushi kawai sapna tayi batace komai ba,
Ummah tace ina wanda yakawo mu ko har ya tafi?
Sapna tace eh ummah ya tafi.
Ummah tace ayyah naso ingansa inyi masa godia Allah dai yasaka masa da alkhairi,
Sapna tace Ameen y rabb.
ummah tashi tayi sapna tataimaka mata tayo alwallah sannan tazo tarama sallolin da ake binta bayan ta gama takoma ta kwanta sapna talullu6eta da blanket sannan takoma d’ayan sickbed d’in itama takwanta.

Tun da asuba da suka tashi ummah ta ji k’arfin jikinta sosai dakanta tashiga toilet tad’auro alwallah bayan sunyi sallah bacci suka koma.

Wajen k’arfe takwas haydar yagama shirinsa d’akin mami yalek’a ganin tana bacci yasa yafito yanufi kitchen lokacin Lami tana ta soya doya Cikin fara’a suka gaisa sannan yace tazuba masa Cikin foodflask sai ruwan zafi, haka tahad’a masa cikin basket yasaka plate da cups sannan yad’auka yaje yasa cikin motarsa yashiga yatada yakama hanyar AKTH,
Lokacin da ya isa d’aukar basket d’in yayi direct room d’in da su sapna suke yanufa, knocking d’in k’ofar yayi nan aka bashi izini yashigo lokacin sapna na zaune gefen ummah suna ta fira, cikin tafiyarsa ta k’asaita yashigo kallo d’aya yayi ma sapna yad’auke kai yamaida kallonsa ga ummah fuskarsa d’auke da murmushi ya aje basket d’in yace masha Allah ummah jiki ya yi kyau, murmushi ummah tayi aikam dae na samu sauk’i, plastic chair tajawo yazauna sannan yagaishe da ummah cikin girmamawa, ummah fuskarta d’auke da fara’a ta amsa, nan yatambayeta jikin nata, tace Alhmdllh ya warware, nan ummah tayi masa godia,
sapna da take gefen ummah tagaishesa, batare da ya kalleta ba ya amsa sannan yace tatashi tazuba ma ummah breakfast

Batayi musuba tatashi tazuba mata tamik’a mata sannan takoma tazauna ita bata zuboba, shareta haydar yayi nan suka cigaba da hira da ummah kamar daman sunsan juna saida tagama breakfast sannan yayi mata allura tasha magani yace da anjima za ayi discharging d’inta bayan anmata allurarar k’arfe sha biyu, nan ummah tayi masa godia yayi musu sallama yatafi bakin aikinsa.

Sapna saida taga fitarsa sannan tatashi tahad’a nata breakfast d’in tazauna tayi tana mamakin halin haydar, d’an guntun tsaki taja ahankali tace basai na damu dashiba sannan zai min wulak’anci.

Bayan ta gama tatattara kayan da suka 6ata tawanke sannan tadawo kusa da ummah tazauna, kallonta ummah tayi tana murmushi tace wlh yaron nan yana da kirki sosai kalli yadda bai sanmuba ammah sai d’awainiya yake da mu Allah dai yabiyasa, sapna tace Ameen y rabb.

Wajen k’arfe sha biyu yaturo wata nurse tayi ma ummah allura, saida sukayi sallar azuhur sannan haydar yashigo d’akin nan suka gaisa da ummah, yanzuma ko da sapna tagaishesa ciki-ciki ya amsa sannan yace sutaso yamaidasu gida, ko da suka fito ummah bayan mota tazauna sapna kuma tana gaba, haydar da ummah hirarsu kawai suke, saida yabiya chemist yasiya mata magunguna sannan suka je resturent yayo musu takeaway daganan yawuce dasu gida ko da suka fita godia sukayi masa ummah tace ba zaka shigoba? Yace eh ummah zan koma wajen aiki ammah da anjima zan biyo tace toh Allah yakaimu mungode sosai, bayan ummah ta shiga gida sapna da take tsaye kamar gunki ahankali tabud’e baki tace dr mungode sosai Allah yasaka da alkhairi, Haydar kallonta yayi yaga kanta asunkuye yake cikin ransa yace ahaka sai kace mutuniyar kirki dakyar yabud’e baki yace Ameen sannan yaja motarsa yatafi, yanayin yadda ya amsa ma sapna ta ji haushi tsaki taja sannan tashige gida.

Sapna kashe wayarta tayi gudun kar lubna tanemeta saida sukayi wanka sannan sukaci abinci ummah da ta motsa batada labari sai na haidar itadai sapna shuru tayi ak’arshema sai tashi tayi tagyara masu gidansu tas, ko da tashiga d’akinta domin tayi sallah saida tasha tabs d’inta saboda tun d’azun takejinta wata iri daurewa kawai take, bayan ta yi sallar la’asar kitchen tashiga domin tad’aura musu girkin dare.

Haydar ko da ya ajesu asibiti yakoma yacigaba da aikinsa sai bayan sallar la’asar sannan yakoma gida, bayan yaci abinci suka zauna hira da mami sai da aka kira magrib sannan yatashi yaje masallaci bayan ya dawo motarsa yashiga yabar gidan.

Sapna tana zaune d’akin ummah suna fira kawai sai jiyo sallama sukayi, kallonta ummah tayi tace jeki kigano wanene yake sallama, Sapna hijab d’inta tasaka sannan tafito da mamakinta sai ganin haydar tayi tsaye a k’ofar gida hannunsa rik’e da waya, d’ago kai yayi suka had’a ido sapna janye idonta tayi daga kallonsa tagaishesa, ya amsa mata tare da tambayarta jikin ummah tace Alhmdllh ya yi sauk’i kashigo, haydar baiyi musuba yabi bayanta suka shiga har d’akin ummah, cike da fara’a ummah tayi masa sannu da zuwa sannan yazauna suka gaisa tare da yi ma ummah ya jiki, sapna ruwa taje takawo masa nan suka cigaba da hira da ummah kamar daman sun saba da juna ganin haka yasa sapna takunna kallo tana yi.

Haydar a masallacin anguwar yayi sallar isha’i bayan ya dawo nan sapna tazubo masa d’an wake da miyar gyad’a daman Haydar yanason d’anwake dan haka yazauna yaci abinsa, sai wajen k’arfe tara sannan yayi musu sallama yabar gidan.

Sapna taje tarufe musu gidan saida tatabbatar ummah bata buk’atar komai sannan tayi mata sallama takoma d’akinta cikin sauri tamurza ma k’ofar key tanufi wajen wardrobe d’inta tanud’e tad’auko k’waya tasha nan hankalinta yarabu da jikinta dakyar tararrafa tahau gadonta cike da nishad’i.

Bayan kwana biyu ummah ta warware sosai haydar kusan kullum sai ya zo gidan sunsha hira da ummah har lokacin ba sa magana sosai da sapna indai ba maganar ta zama doleba,

Yau kasancewar lahadi ce sapna kunna wayarta tayi ko minti biyar batayiba da kunnawa sai ga kiran lubna ya shigo, tsaye tayi tana kallon wayar har ta tsinke, wani kiran ne yasake shigowa, picking d’in wayar tayi kafin tayi sallama lubna cikin fad’a tace sapna dan kin rainani har kin kai matsayin da zaki kashe min waya ko? Sapna kwantar da muryarta tayi tace ba haka bane mummy kiyi hak’uri, cikin fad’a lubna tace to in ba haka bane to yayane? Sapna shuru tayi sai can tace wlh ummanace batada lafiya har hospital akayi admitting d’inta tun ranar da mukaje partyn nan, a chan 6angaren lubna ta6e baki tayi cikin ranta tace dama ta mutu kowa yahuta, sai chan tace Allah sarki toh ai baki fad’amin ba ai da munzo munganta, yanzu kuna ina?
Sapna tace muna gida ai ta ma ji sauk’i, lubna tace toh Allah yak’ara sauk’i yanzu to yaushe zaki shigo? Shuru sapnana tayi saida lubna tak’ara maimaita mata sannan sapna tace saidai ko gobe mummy,
Lubna tace haba sapna tunda ta ji sauk’i kid’an shigo yau inganki baby sai kidawo gida ba kwana zakiyi ba.
Shuru sapna tayi kamar tace a’a sai kuma taji ba zata iya yi ma lubna gardama ba danhaka tace toh mummy ganinan zuwa, cikin jin dad’i lubna tace yauwa baby sai kin shigo, kice ma ummah ina mata ya jiki, sapna tace toh sannan sukayi sallama takashe wayarta,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button