BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Haydar saboda farin ciki kasa komawa bacci ahaka har aka kira sallar asuba,

janye sapna yayi daga jikinsa tare da gyara mata kwanciya sannan yatashi yanufi toilet, bayan ya d’auro alwallah dawowa yayi yazauna gaban sapna ahankali yakai hannu yashafi fuskarta, ganin ta motsa yasa Haydar yace baby kitashi kiyi sallah lokaci yayi,

dakyar sapna tabud’e idanuwanta da suka kumbura tasafkesu akan fuskar Haydar, dasauri tamaida idonta tarufe cike da tsanarsa domin bata ma son ganinsa,

murmushi haydar yayi yace please baby kitashi ko baki iyawa intaimaka miki? Bud’e idanuwanta tayi tare da wurga masa harara, haydar tsanarsa yagani tsantsa a cikin idanun sapna, bai damuba yace kitashi kinga ana shirin tayar da sallah masallaci, Sapna saida tagyara d’aurin towel d’inta sannan ta janye blanket d’in tana shirin mik’e,

hannu haydar yakai zai taimaka mata tamik’e, dasauri sapna tad’aga masa hannu cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace kar kasaki kata6ani, dakyar tamik’e tana fara takawa kamar zata fad’i saboda wani irin zafi da takeji, nan ma haydar yace baby ba zaki iyaba bari intaimaka miki hannu yakai yana shirin rik’eta,

k’wallah tana fita daga idanun sapna tace na ce maka kar kasaki kata6ani, harara tak’ara wurga masa cike da takaici tace ashe ka san taimako ban saniba, ko ka mance da karuwa ‘yar iska kake tare?

Haydar lumshe idonsa yayi yana Jin yadda maganar sapna tak’arshe tadaki dodon kunnensa, ahankali yabud’e idonsa yasafkesu akan sapna da take taku dakyar ahaka har takai toilet,

ganin haka yasa haydar yaficce yanufi masallaci cike da tausayin sapna domin shima kansa ya san ya wahalar da ita.

Sapna ko da tashiga toilet maida k’ofar tayi tarufe tajingine kanta jikin k’ofar tacigaba da rusa kuka cike da takaicin abinda haydar yayi mata koda ta san taimakonta yayi ammah ta gwammace tamutu da ciwon akan abinda yayi mata. , saida tayi mai isarta sannan tahad’a wasu ruwan masu d’umi tashiga tak’ara gasa kanta sosai sannan tayi wanka tare da d’auro alwallah.

Bayan ta fito wardrobe tabud’e tad’auko doguwar riga tazura tazo tagabatar da sallah, tana zaune saman darduma har haydar yadawo yakoma yakwanta.

saman dardumar takwanta nan bacci yayi awon gaba da ita, ganin ta yi bacci yasa haydar yazo yasureta yanufi gado da ita, yakwanta tare da rungumeta a jikinsa ahaka shima bacci yayi awon gaba da shi.

around 11 haydar ne yafara farkawa janyeta yayi daga jikinsa yatashi, fita yayi yanufi chan part d’in su mami yayi sa’a ba kowa wajen dan haka yanufi kitchen da yaji motsi yana shiga yatadda mai aikin mami ce bayan sun gaisa nan yasa tazuba masu yamball d’in da tayi tare da kar6ar flask d’in ruwan zafi.

ko da yadawo a dining ya aje sannan yakoma bedroom har lokacin sapna bacci take dan haka toilet yawuce yayo wanka, yana cikin shiri sapna tafarka, Suna had’a ido tamaida idonta tarufe tare da juya masa baya.

Murmushi haydar yayi yace baby kidaure kitashi kije kiyi wanka kiyi breakfast dan nasan yanzu dai yunwa kikeji.

Sapna shuru tayi takyalesa kamar ba da ita yakeba, ganin haka yasa shima haydar yashareta yacigaba da shirinsa saida yagama sannan yace kitashi kije kiyi wanka bari inje parlour injiraki idan kuma har nashigo bakiyiba toh ni zan yi miki da kaina, yana gama fad’in hakan yaficce daga d’akin tare da maida k’ofar yarufe,

Sapna tana jin fitarsa tamik’e dakyar tare da wurga ma k’ofa harara tace mugu kawai sai Allah ya saka min kuma yau sai ka sakeni, wajen wardrobe tanufa tafiddo kayan da zata saka sannan tad’auko wani bedsheet d’in taje tashimfid’a a gadon saida tagyara d’akin fes yad’au k’amshi sannan tashiga toilet tayi wanka,

Bayan ta fito mai da powder kawai tashafa batayi wata kwalliyaba tad’auko rigarta gown tasaka ta atamfa sannan tad’aura kallabi,

komawa tayi bakin gado tazauna tare da buga tagumi, haydar jin shurun ya yi yawa yasa yataso yashigo d’akin ganinta yayi a zaune,

Murmushi yayi tare da takawa inda take, Sapna bata ko d’ago kai takallesaba shima zama yayi kusa da ita yace baby fushin ya isa haka nasan na yi laifi please forgive me, banza sapna tayi masa tare da k’ara had’e fuska, ganin haka yasa haydar yarik’o hannunta yace please my princess talk mana banason shurun nan da kike min yana sauyamin zuciya.

Sapna janye hannunta tayi daga rik’on da yayi mata har lokacin batace masa komaiba, ganin haka yasa haydar yace taso muje kiyi breakfast kisha magani kinga har yanzu jikinki akwai zafi.

nan ma dai bata tankaba, mik’ewa haydar yayi tare da rik’o hannunta yace please kidaure kitaso muje ko so kike ind’aukeki inkaiki dakaina? banason zamanki da yunwa, nima yunwar nakeji bana iya ci batare da kin ci ba, sai a lokacin Sapna tad’ago kai takallesa a wulak’ance tace haydar kenan sai a yanzu kasan da haka? tunda ka samu abinda kake so shine kake lalla6ani kana min dad’in baki
Murmushi tayi Wanda iyakarsa bakinta tace gaskiya natayaka murna da kasameni batare da kasha wata wahala ba, banso kataimaka min ba naso ace ka bari ciwon ya kasheni, ammah inaso kasani ba zan cigaba da zama da kai ba dole kasakeni.

Tunda tafara maganar haydar yakafeta da manyan idanuwansa cike da mamaki yace Sapna saki kuma? ina tunanin laifine nayi miki kuma na baki hak’uri ya kamata kihak’ura muzo mugyara zaman aurenmu,

Sapna mik’ewa tayi tsaye itama fuskarta babu alamun tsoro tace kar ma kasaki kayi tunanin cigaba da zama da ni, lokacin rabuwarmu ya zo dole kasakeni fashewa tayi da kuka tace wlh haydar ka cuceni, da nasan kaine zaka rabani da mutuncina da nabayar da shi a waje ga wasu domin kamar yarda kace baka sona nima bana sonka, natabbata soyayyar da kace kana yi min ta yaudarace jikina kawai kakeso domin bana tunanin k’iyayya irin wacce kayi min zata iya komawa soyayya.

Haydar cike da tashin hankali yarik’o Sapna yace Sapna please believe me wlh ina sonki fiye da yarda kike tunani ban ta6a yi ma wata mace soyayyar da nayi mikiba.

Sapna fizgewa tayi daga rik’on da yayi mata tare da wurga masa harara tace taya kake tunanin zan yarda da kai? Toh bari kaji ni bana sonka, ba zani ta6a sonkaba kuma dad’in kalamanka ba zasu ta6a tasiri agareniba dan haka dole karabu da ni inkuma ba hakaba abinda banyiba a baya shi zanyi a yanzu,

Haydar a kid’ime yarik’ota yace haba sapna kifahimce ni mana wlh dagaske nake miki ina sonki dan Allah kibani dama domin in nuna miki irin son da nake miki wlh ba jikinki nakeso ba ke nakeso,

Sapna fizgewa tayi daga rik’on da yayi mata tace dallah malam kadaina ta6ani kaje can kayi dad’in bakin ka a inda zaiyi amfani ammah ba a wajen sapna ba, ka mance duk cin mutuncin da kadinga yi min ko kamance da d’aukata da kayi kakaini ayomin test d’in HIV? K’ara fashewa tayi da kuka tace idan ka mance toh ni ban manceba wlh haydar na tsaneka ina zaune da kai ne kawai saboda mahaifiyata, tana gama fad’in haka tafad’a saman gado tacigaba da kukanta.

Haydar tsaye yayi kamar gunki maganganun da sapna tayi masa suna yawo a cikin kwalwarsa kukan da takeyi yana jinsa har cikin ransa.

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button